Izzuddeenms
Mu....... (Us)

Mu....... (Us)

38 6 3

Mu Da Iyayenmu rayuwarmu tana tafiyane da albarkarsu, Mu Da Iyalanmu rayuwarmu tana tafiyane da kyautatawarmu ga junanmu, Mu Da Abokanmu rayuwarmu tana tafiyane da hakurinmu a tsakaninmu, Mu Da Makwabtanmu rayuwarmu tana tafiyane da kawaicinmu ga zamantakewarmu, Mu Da Sana'armu rayuwarmu tana tafiyane da gaskiyarmu a sana'ar, Labarinmu da kuma Hikayarmu tana tabbata ne da dadin faruwa gwargwadon yadda muka fahimci zahirin rayuwar da kuma yadda muka shiryawa fuskantar wannan kalubalen na rayuwa.Alhaji Hashim ya kyautata kwarai ga iyalansa, iyayensa, makwabtansa, ma'aikatansa da Abokansa. Amma kaddararsa ta sanyashi rasa ransa a kaddara bayyananniya. Sai dai rayuwarsa ba aba bace da zata salwanta haka kawai! Akwai kalubalen da yake biyowa baya wadda ya girgiza dukkan madafan ikon kasar ta Najeriya.โ€ฆ

Bin Son Zuciya

Bin Son Zuciya

17 1 1

Dukkan damuwa mai saukice, dukkan takaici mai saukine, dukkan kewa mai saukice, idan har an shirya musu ko an san da yiyuwar faruwarsu. Rana daya tak a wayi gari an nesantaka da iyalanka, sana'arka da al'umma, an kuma kebeka cikin kulawa ta musamman a wajen da kai ma kanka ba zaka iya cewa ga gabashinsa balle yammansa ba, watakila a wannan shekarar ta 2022 masu garkuwa da mutane ne suka sace ka, watakila kuma masu son yin tsafine da kai. Fatan jiran tsammanin ganin menene dalilin wannan killacewar da akai maka, ba ita ce babbar damuwa, takaici da kewar da ke addabar zuciyarka ba. Yaya iyalanka da 'yan'uwanka da makusantanka suke ciki? 'Dan hakuri kadan za ka kara a killace, har ka fahimci shin zaka rayu ne ko kuwa wannan shine karshenka; wato zaman jiran tsammanin rayuwa ko mutuwa, cike da dumbin damuwa, takaici da kewa.Izzuddeen Muhammad Sani,27th September, 2013.โ€ฆ