*AMFANIN SOYAYYA*
(aure )
*NA*
*BATUL ADAM JATTKO*
*29*
sunan Hamrah kam shima anyi shagani sai de mejego bata da kuzari saboda kukan da ruwaida tayi ta mata awaya kwata-kwata bata da walwala ga ba Ayya ba Ruwaida yarinya taci sunan mama Bulkisu maman Sahal an mata alkunya da Fhuttihatul khairi amma tsaban iya bata suna irin na walwala sun fara kiranta da Fhutee sai washe gari yan adamawa suka tafi
da sha tara na arziki
After 3months
a tare suke saukowa hannu su sak'ale da juna kallo daya zaka musu kagane kwanciyar hankali da nutsuwa ya gama samun muhalli bakar suit da wando ne ajikinsa sai farin T-shirt da bakin necktie bakin cover shoe dinsa sai iban ido yake itako cikin dogon shijabi me hannu har k'asa ko takallmin ta ba a hangowa sai de tozon cikin ta da yayi das dashi ga nikamf cikin nutsuwa suke takawa da ganin yanda yake sakar mata murmushi fira sukeyi Ismail mutum ne marar yarda musamman a wannan zamanin dan haka bai sanar da kowa time din da zasu sauk'a ba ko office dinsa basu san ma da zuwan nasa ba balle su zo tarya kai tsaye office din wani abokin sa da yake aiki anan airport din ya wuce knocking Yayi na cikin yaba da izinin shigowa Imran yana ganin Ismail ya mek'e tsaye "ah ah to yau kuma manya ne airport dinnamu amma bamu ji operation tarzoma suna mana Scanning ba."
"au tarzoma ne ma ba salama.
"haba Manjor ai ba a ganinku a inda ake salama. murmushi Mall yayi yace "i to dame ko do yafi gaya muda masu fiffike.
Imran yanunawa Mall dogon kujera alaman su zauna zaunar da Ruwaida yayi ahankali yana kallon kafarta da ya kumbura sosai ruwa Imran ya kawo musu sai da yakoma mazaunin sa sannan yace "Allah abokina dama ko baka zoba idan kazo zan nemeka seriously wllh nagaji da aikin tuk'innan a ce kullmu kana sama idan ma ak'asan ne baka da wani lokaci nagaji amma ba yanda zanyi kaga de tare muka karanci pailot amma lokaci guda kaida sahal kuka can za dalilin kuna da alfarma."
Mall yace
"ai tun farko haka na gano naki saka certificate dina na pailot da za a daukeni aiki kaga yanzu ba wanda yasan ma na iya tukin jirgi amma yanzu kai ma kasan lokaci ya kure maka saide alfarma daya nasan za a min zan sa ma maka gurbi a office dina idan kana so amma dole za aturaka course koda na shekara daya ne saboda koyan harbi da sauran ka idojin soja kuma da certificate dinka na tukin zaka shiga in sha Allah akwai hutu da sauyi da cigaba fiye da nan."
"kai amma ka min gata zai fi nan sauk'i sosai thanks my friend."
"never mind kuma dama muna bukatan matukan da doctor ci.
Ruwaida tace "ina wuni.
atakaice Imran yace "lafiya madam.
ta cikin likaf Ruwaida ta tabe baki ko meyasa duk abokan Mall da take gani masu girman kai ne idan kaji suna zuba zance to a tsakanin sune jibi ba kun sauk'a lafiya ba dan kulawa irin na abokin miji
Ismail yace "to ka samo mana motan da zai kai mu walwala."
ture laptop din gabansa yayi tare da daukan key yana mek'ewa yace "bari na sauke ku nima madam na jirana." Ismail da yake mammatsawa Ruwaida kafa yace "ko zaki huta sai anjima mutafi....
ai kafin ya k'arasa har ta mek'e dariya yayi yana cewa wai duk dokin ganin Khairee dinne."
suna cikin tafiya wayan Imarn da yake tuki yayi ringing rage gudu yayi dareda amsa wayan ahankali yake maganan dan suda suke baya basu masan me yake cewa ba suma nasu firan suke gani tayi ya mekowa mall wayan yana cewa "kabawa madam wayan zasu gaisa da JIDDARH" Mall ya karbi wayan yana mek'awa Ruwaida Ruwaida sallama tayi daga can aka amsa tareda cewa "Ruwaida ko ai najima ina son mu hadu mazajen mu ami nai amma mu bamu san juna ba amma lefin mune nawa me gidan yawanci baya gari ya kike zaki samin rana zanzo in sha Allah."
" lafiya lau Alhamdulillah OK sister gobe zan tafi meduguri daga nan zanwuce gida kaduna amma zuwa next week insha Allah koda wane lokaci ina gida."
sun dan taba fira kafin suyi sallama ta mekawa Mall wayan ya bawa meshi Ruwaida da k'er ta tsaya aka gyara packing ta balle ta fito Mall murmushi kawai yake mata masu aiki sai sannu suke mata hannu kawai take daga cikin sauri take wuce su har tawuce gidan Ummi da yake gidane kashi-kashi kowa da get dinsa arufe acikin gidan ba wanda ya ganta yaran gidan tanajin karatunsu a islamiya aiko yaro daya ne ya hangota Kafin ta karasa gidan Hamrah har su karaso da gudu suna ga Aunty Ruwa har yan matan sun fito "kai hammee karatun fa harda ku kuka fito ina ga ba mlm Usman a makarantan ko.?" Hamida tace "wllh yana nan ai lokacin tashi har ya wuce dama fa addua akeyi... Meena ko turo baki tayi wllh Aunty Ruwa baki kyauta mana ba anfa yi hutu da tomorrow fa ya Jallal yace zai kai mu Hutu wajenki nagaji da kurkukun nan wllh".
dariya Ruwaida tayi tana tafiyan tace ummm su Meena yan mata har yawon shak'atawa kuke son fita wato dama jira kuke su Nafi zubaku waje ko to gobe sai kumin rakiya meduguri... Ameer yace Aunty harda mu?
"eh mana babana dukkan mu Amal tabe baki tayi "wllh mude London zamu wajen Aunty Jamila."
duka yan matan biyar suka hada baki Eh wllh hakan ma yafi yaran kuma sukace zasubi Ruwaida medugurin Hamrah da take kokarin hawa sama dan taji kukan Fhuttee taji hayaniya tare da ban ko k'ofar ita tsorata ma tayi amma da tayi tozali da Ruwaida ai tuni ta manta da dauko Fhutee da gudu ta fada mata Ruwaida tace "sakeni malama ba ke nake son gani ba ina babyna"? Hamrah tabe baki tayi tace "masu baby manya to nemeta inda kika ajiyeta." da sauri Ruwaida tayi sama tana cewa "Allah sarki nama jita tana min oyoyo.
dan har wannan lokacin kuka take yarinyar sosai d'a gota tayi ta nata juyi da ita tace "Masha Allah
I love my daughter a zashiri kinfi kyau... juyi tayi - tayi da ita har su Meena suka shigo anan aka yada zangon fira yawanci firan da Aunty Ayya akeyi dan ajiye wayan akayi akasa
a hands free kamar tana nan knocking akayi Khalifa ne yashigo
"wai inji boss akai masa baby Fhut."
hararan sa Ruwaida tayi tace " kai Khal bata sunan har kan yaran mu to tun wuri ku canza idan bazaku kirata da Fhutiatul khairin ba kuce mata bulkusun ta ko Amira ."
dariya Khalifa yayi yace "ai abinda bai faru ba akeyiwa woning ba abinda yarigaya ya faruba rashin karasa suna tambayi tarishin gidan nan mijin ki ne yafara shi yafara kiran ya Sahal da Sall shima yace Mall a wajen su yafito har muma ya bimu dan haka ai dole yabi yaran su." kwafa Ruwaida tayi
Hamrah tace
"wai tsaya wane Boos kake nufi Abban Fhutti yazo ne."?
Khalifa yace "soja nake gaya miki."
"wai kana nufin Yamall da kansa yace a kaita" Ruwaida tace "lalle baki san yanda Habibi ya ke ji da Khairi ba ne."
"nasani sister ko a waya fa sai yace wai zasu gai sa inajin su Abban ta yayi ta mata cakul Kuli wai yaji dariyar ta a yan da Mall yake nuna k'iyayyata afili ban zaci zaiso abinda yafito daga gareni ba abin yana bani mamaki."
Khalifa yace "mamaki dan yamall yaso ya'r yasal lalle har yanzu baki san soyayyar yake tsakanin su ba ya kamata kusan tarishin gidan nan su suka fara kafa soyyaya tsakanin Wanda kake kusan sa anni har yazo kan mu nida Khalid da Lawan da k'annen mu maza da mata kowa yana da aboki sune silan hadin kan gidan nan wanda kuka ga de nawaje dawuya ya gane wannan dan gidan Umma ne wannan na Mama ko Mommy yaran Ummi ne de suke nuna kansu da yake yawanci ita suke biyowa akamanni Lal da Hamee ne kawai suka biyo walwala."
Ruwaida tace "gaskiya bata san kaunan da Habibi yake wa Khairi bane wai bakiga da duk wani kafar sa ta media ita ce ba sai ni na masa magana ya cire saboda duniya ya lalace da mutane da shedanu duk sunfi cutar da mutun da abinda yanuna soyayya afili musamman media be kamata wanda aka San sa aduniya kamar yamall ya nuna familyn saba mutane su suke jawowa kansu Kidnapping ."
Hamra tace "haka ne kuma zansa Abban ta ma yacire"
Ruwaida tace "tun yaushe ai ina gaya masa yasashi shima yacire khalifa yasa hannu ya dauki futtee Hamra tana bari na canza mata kayan ta ya fice
Ruwaida da tabi baby da kallo ta sauke ajiyan zuciya
tace "Masha Allah wllh kamar sahal ya zauna ya zana fuskan sane amma sai naga kamar tafi a hoto haske."
"Eh kwana biyun nan naga tana washewa sosai ina ga fa ba bak'a bace irin haifuwar inna na gado inna idan ta haifu jaririn baki amma yana girma yana k'ara haske
wai tsaya ina kika bar shi mijin naki."?
wllh ban sani ba muna sauk'a nayi nan."
ido Hamrah ta
warararo tace "kina nufin baki bi dokan gidan nan ba."?
Ruwaida tace "doka kuma wane irin doka."?
''k'a idane idan yaran gidan nan suka zo a bangaren Mama ake sauk'a daga nan ka nemi inda kake bayan ka huta ka zaga ka gaida mutanen gidan kin san Mama ita aka fara aurowa bata samu haifuwa har aka auro umma ita made bata samu haifuwa daruri ba sai bayan an auro Ummi tarigata haifuwar yamall kinga ana garrama mama ne saboda bata haifu ba kuma duk yaran maza fa ita take yayesu sai sunyi wayo kowa yakoma inda yafiso".
Ruwaida tace"wllh ban sani ba amma ai lokacin da mukazo daga india ai agidan Ummi muka sauk'a."
"Eh wannan ai tafiyan jinyane."
"to tashi kirakani wllh gidan su Umma ne jamaa da hayaniya Yayi yawa musamman part din Mama."
aiko a cike suka samu parlour nasu a babban parlour na Umma da samarin gidan dan dama duk agidan suke yan matan gidan agidan Maman farida duk da kowacce a part na su tana da 'daki amma zama de meyawa abangaren mama farida zaman yafi yawa walwala suna da wani irin hadin kai tare da soyayar juna ba nuna ban banci suna hakurin kawar da ido akan komai
kamar yanda suka zata kuwa gidan cike yake da yan samari mama tafita Umma na tsakiya sai cin dariya ake da murjejjen jikin ta mekyau kamar ba ita ta haifi Sahal ba dan Umma bata daukan girma ko ajikin Hamrah taga style na dinki idan yamata to zatace zanyi idan kin cire aiko min kunde san yanda idan gayu ya hadu da hutu yake
"lale lale da 'yata"... tameke tana taryo ta Ruwaida zata durkusa ta kamo kafadunta ta zaunar da ita a kujera "Umma mun sameku "lafiya.?
Lafiya lau y'ar albarka ya naki jikin ba wani abu da kikeji ko ai da bai kawo kiba 'karshen watan nan zamuje nida Mama mu dauko ki kin kusa kin higa wata na na tara amma munyi munyi ya kawoki yaki gashi da gake harshi masu son zak'i."
shiru Ruwaida tayi tana sa kanta a k'asa
abinci kala kala aka dinga gabatar mata taci kamar ba gobe dan tayi missing dinsu over haka tayi ta zagawa suka yada zango a gidan hajiya Ummi da bakin ta yak'i rofuwa sai nan nan take da ita Ruwaida har ta manta da zuwa gidan ta ma har bayan isshai Hamra ma sai da Sahal yayi kira ta tashi tamek'e tana cewa oga yana k'ira yamayi hakuri inde abul Fhutti ne".
Ruwaida tana gyara kwanciyar ta akan kujera tace "dan yasan munyi kewar juna ne yabari."
Hamrah ta harareta tace "kema malama tashi zakiyi ki wuce gidanki ai ya isa."
Ruwaida tace "ummm ai wlllh sai ya nemeni dan wllh nasan fushi yake dani idan ya huce zai kira da kansa."
"Fushi akan me?.
"inaga akan banje gidan ba ko ban kirasa ba baki ga yanda d'azu ya shareni ba kamar fa bai sanni ba kinsan baya rena lefi.
"to kunfi kusa nide yanzu ko ina zan samu y'ata."
Ruwaida tace "kamar de NÍ ima ce ta fita da ita ahannun ta".
Hamrah tace "ai yanzu ta zama nema kawai.
Hamrah tafita bajimawa Mall da Abba suka shigo sai wani cin kunu yake itama Ruwaida sharewa tayi sai da safe yayiwa Ummi yana mek'ewa UMMI tace "to ilu Allah ya huta gajiya Ruwaida ko tana nan sai ta sauk"a ko?.
juyowa yayi yana yiwa Ummi kallon tambaya amma sai yayi murmushi yace "ba damuwa idan hakan shine dai-dai Allah yara ba lafiya..
dariya Ummi tayi tace " ah ah dawasa nake gobe zata koma yau zamu dan taba fira ne".
"amma Umma hakan ma ai ba dai-dai bane goben ai sai tazo Allah Ummi duk ke kike daurewa yarinyar nan take abinda taga dama yanzu fa tunda mukazo ko gidan bata jeba ai acan ba haka take min ba tama isa yanzu daga zuwa taganki har ta canza ....
cikin dariya Ummi tace
"ah-ah dakata naji me rowar mata dauki kayan ka ai dama nasan tunda ta aureka to ta auri hakuri..
Ismail ficewar sa yayi dan ruwaida ta bashi haushi Ummi tace "tashi kibi mijin ki .'
cikin shagoba tace
"Ummi ya tafi fa."
''baki san hanyar gidan bane'.
baki a zunbure ta tashi taso Ummi tace anan zata kwana dan tasake kularda mall
ahankali take takawa dareni amma hasken wajen ba abin da ya rabashi da hasken rana gidan da take kyau tata zaton na sune gani tayi an canza fasalin komai na gidan ba dan ta masa kyakkyawan sani ba zata iya cewa ba shibane ahankali ta tura get din "masha Allah. tace afilli tana takawa har zuwa ga inda take zaton nanne mashigan falon batayi knocking
ba amma tamurd'a bakinta dauke da sallama cak ta tsaya tana kallon fasalin parlour sai juj-juya ido take itade ba dan kartayi k'arya ba zata iya cewa duk yawan ta kasashen turai da dolan larabawa zata iyacewa bata ga fasalin falon da ya burgeta haka ba gashi anyi amfani da colours din tane wato fari da ja red haka kujeru da duk wani abin decoration din parlour kana gani kasan na musamman ne tsayawa fadin tsaruwan sa b'ata lokacine komai de off whale tana juyi tare da hamdala idonta yasauka kan wani makeken hoton su tana sanye da abaya purple colours tayi nadin larabawa tayi d'as cikinta yafito sosai shiko sanye cikin jallabiya b'aki yarungumota tabaya hannnayin sa akan cikin murmushi tayi tatuna haduwar su da ANAS a saudia ne yamusu kwanaki amma batasan yayi kyau haka ba dan bata k'arba ta gani ba jitayi an rungumota ta baya a kunneta yarada mata
''YARABBI INA ROK'ON KA DAN GIRMAN ZATIN KA KA DAWWAMAR MIN DA MURMUSHI A FUSKAR KY'AKY'AWAR BAIWAR KA AISHA YAR MAHAMMADU MATAR ISMAIL.''
juyowa tayi ta hade fuskokin su cikin sanyin murya tafara magana ''AMEEN HABIBI KA IYA SIYE ZUCIYAR MASOYI YANDA KASANI FARIN CIKI BA ABU NE DA ZAN IYA MANTA SHIBA.....
''Matata ai nidama babban murina nasaki cikin farin ciki dan kema kina sani fiye da yanda nake saki bana gajiya da ganin murmushin ki abincin zuciyata''
''amma ya akayi kasan kalolina bayan ban gaya maba.''?
''Ya bazan sani ba bayan zucuyata da taki abokan juna ne.''
''Gaskiya na yarda da abinda su Aunty AYYA suke fada wai ni y'ar wa wace sai de abira a yina ako ina sai yanzu na yarda da hakan tunda na kwashe ra ayin me tsassauran ra a yi kamar ka.''
Ismali yace
" sosai ke y'ar wawace amma nede Wawan sonki ne ya kwashe komai na ra ayi na iya. ''
" YA ALLAH kai shedane ina son nayaru da mijina fiye da komai kasake haskaka kʼaddaran mu muzauna cikin aminci da yar dan ka....
''Ameen uwar daʼkina me masauki na.'
taji muryar macce an amsa mata sheda me muryar yasa ta juyo da sauri idon tane yasauka akan wanda take kyutata zaton dama ita zata gani cikin mamaki tace ''Caballiya.!!.....
''Naam uwar ʼdakina.' Juyowa tayi tana kallon ismail din cikin mamaki gira daya ya daga mata yana murmushi yace ''kinyi mamaki ko haka zanyi ta gaba da baki mamaki amma fa na farin ciki.... kafin yarufe bakin sa sai taji an rungumota ta baya juyowar nan da zata taci karo da BARRAT ABDALLAH
cikin sauri tace ''Barrat Abdallah''.
''AUNTY munyi missng naki sosai ''nima haka my bro haka aka zube Caballi ta kawo abinci kala - kala Ruwaida sai farin ciki take har yaran suka ce bacci zasuyi Abdallah ya yi ʼdaki Barrat kam da Caballi suka shige nata d'akin
kallo fa yakoma sama Ruwaida a bedroom dinsu
nan ma fari da ja komai na ʼdakin gaban mirrow ta kʼarasa ta taba wannan ta taba wancan bawani abu da zata bukʼata ashe shiyasa da tace zatayi siyayya fur yahana ashe da abinda yataka tana dago kanta ta miron taci karo da wani tafkeken show glass juyowa tayi nan ma ta kʼarasa kayan turaren wutane kala-kala aciki duk da arufe yake fitunannen kamshin da yake fitarwa kamar ana amfani dashi hannu tasa tana neman inda zata mude taji ankama hannun har yayi wankan sa ya canza singlet da boxer yace ''abar kallon haka sai gobe ki kʼarasa ko'.
''amma habibi haka zakamin'.?
.ido yaware da nayi me. ?
''Kayi wankan ka baka nemeni ba.'
''Oooh! sorry my dear naga kin shagala dayawa ne da yara nikuma kayan sun min nauyi ne amma muje na miki Indon mata.'
Dʼan wani kwana taga sunsha sai gasu a dressing room ummm sai kace wani babban shago anan kallon ma yake gefe daya wordroop ne me murfin gilas ana hango duk abinda yake ciki daya rigunan bacci ne a lan kʼaye nasa da nata sai daya kananun kaya na shan iska
daya kuma man yan kayane gefen lace daban gana atumfa da shadda materials da yaduna kowanne an jerasu a ninke ba alankʼaye kamar kʼananan kayan ba ban duk bata tsaya irgasu ba tasan kowane zanyi kala dari-dari geren ta kalma da sarkʼa da ban haka shima agogunan wajen ya hadu kamar wani babban super market ba abinda babu ga miro ta ko ina amma andan sa katanga ne tsakanin sa da gadon dan haka idan kana cikin bathroom baka hankowa sai kasha kwana amma duk cikin dʼaki dayane bathroom din yana gefen dressing room din har yagama cire mata kayan jikinta ya daura mata ta towel tana mamaki wai duk yawonta bata taba ganin ko kwatanta irin wannan dakin ba sun kuyawa yayi dai-dai kunne ta yace ''INDON MATA ya akayi? '' ajiyar zuciya ta saukʼe tace ''Abu Fayyat ina tunanin irin kudin da akar- anan ne yaya kaduba ban garen sarkʼan da agogo na gol ma bukʼata nawa za abawa jarin da zasu tsaya da kafafun su afumfofi kawai inaga yafi kala dʼari haka les wadan nan suturun kad'ai ya isa jarin wani kayan sunyi yawa shekara nawa zanyi ban taba wani ba wllh in ban taba kwatan ta irin wannan ni iman aduniya ba''.
Jan kujera yayi ya jauna tareda zaunar da ita akan cinyar sa yana shafa bayan ta
yace ''farin cikin ki da murmushin ki nake bukʼata koda baki godemin ba ni zan gode miki kin bawa zuciyata abincin sa murmushin ki su kuma mabukʼata da kike magana ina iya bakin kokarina dan kinsan Allah shine kʼadai zai iya yaye damuwar kʼasannan ni ame dan na dan farantawa iyalina ai gyaruwan kʼasannan sai da irinku-irinku yan kasuwa....
''ni kuma?.'
Eh mana ai kedin babbar hajiya ce wanda arana daya kina samun albashina na shekara ko fiye da haka ma dan Abban kaduna yabada duk kan takardun company da yazama na mallakin ki ya dankʼa komai a hannuna.''
Ruwaida tace
''company na kuma ban gane ba '?
''wanda yabaki tun kina yarinya mana cewa yayi yagaji da juyamiki nashi ma ya ishehi shima yana da iyali ya raba naki wai muji dashi''.
'' ummm Abba kenan ai da ya barshir abinda zai Iya jurewa wazai iya.''
Mall yace
''Hakan shine dai-dai Aisha Abba da yabani labarin sa nayi mugun tausaya masa Abba bashi da matemaki ma ana dan uwa tunda ya budi ido akasuwa yaga kansa ga dukiya kullum hau hawa yake dan ma yana da mutane na amana in sha Allah zan temaka masa dana kin ba dan aikina da bana fatan na barsa ba da saide ya kadʼe gado ya kwanta.''
'' gaskiya habibi bana fatan kamar aikin ka kana matakin major da muke sa ran samun General kwana kusa
Murmushi yayi yace ''da yar dan Allah''.
''amma Habibi kabani tsoro fada kace arana daya a na samun riba fin albashinka na shekara kana menjo.''
'' to ai haka ma na kamfani daya nayi aiki akansa wata ukku zuwa yanzu bansan sauran ba a company shinkafa da taliya na kaduna ana samun riba na 35millions akowacce rana wai a ansamu dʼan ma kenan kinga ko ai kune da alhakin gyara kʼasa bani almajirin gomnati ba yanzu de mushiga kiyi wankan gashi gobe kina da zuwa abuja.'
'Abuja kuma habibi.'?
''Eh akwai taro da ake na matan manyan kʼasa kamar wanda suka rike shugaban kʼasa manyan sojoji tsofi da kuma nayanzu ku dari hudu da sinttin ne a taron amma ke kina daga cikin matan da zasuyi jawabi mutum
ashirin da biyu.''
Ruwaida ta marai raice fuska tace "Kuma yallabai baka sanar dani na shirya ba sai a kureren lokaci''.
''Eh Wllh da ba kyacikin wanda zasuyi jawabin jiya da takardar tabiyo ta office dina ne na canza nacire wata shahasha wanda nasan ba abinda za
You are reading the story above: TeenFic.Net