KADDARA CE
KADDARA!Shin me cece ita?.KADDARA na ɗaya daga cikin hukuncin Allah da ya kan zartar a kan bayinsa tun yayin hallita.KADDARA tamkar zagayen zobe take, wanda ɗan adam ke rayuwa a tsakiyarsa.Duk wani abu da ya samu bawa tun daga ranar haihuwarsa zuwa ga ranar da zai koma ga mahallicinsa sunansa KADDARA.KADDARAr ko wani bawa na rubuce ne tun kafin ya iso zuwa duniya.Kowa da ka ga yana rayuwa a doron duniya yana yin ta ne a doron KADDARA.KADDARA na ɗaya daga cikin manya manyan siffoffin Allah subhanahu wata'ala.Domin duk abin da ya samu bawa a rayuwa muƙaddari ne daga wurinsa. Wa lau me kyau, ko akasinsa.…