Smiling_Bay
71,756 7,707 58
Murmushi tayi mishi wanda ya tafi da imanin sa yayin da ta juya kallonta ga duΙΙin mutanen wajen. Dogayen yatsunta biyu wanda suka sha jan lalle ta buga akan speakern dan ta ga ko yana aiki. Illai kuwa sai ta ji Ζaran bugun da tayi. Murmushi ta Ζara sakar wa mutanen da duk ita suke kallo, da mamaki a idanuwansu, kafin ta buΙe baki tafara magana kamar haka." Assalamu alaikum " sai ta Ιan dakata kaΙan don su amsa mata, ba laifi wasu sun amsa mata wasu kuma sunyi Ζum da bakin su. " dama na zo ne don na nuna farinciki na game da taya abokin mu, kaninmu da yayen mu Salim murna " tace yayin da take kallon angon wanda tun tahowarta stage yake warwara ido kamar baΖin munafuki, gashi yanda zufa yake ta keto masa, zaka zata ba ac a wajen.Kau da idanunshi yayi kafin su hadu da nata. " amma kuma abin da ya sosa min rai game da wannan abin shine ni nafi chanchanta da a kira in zo in bada tarihin wanan bawan Allah. " ta Ζara dan dakatawa yayin da ta runsunar da kanta kamar mai wani tunani, sai kuma ta k'ara daga kanta ta kalle mutanen da duk suke yi mata kallon mahaukaciya wadda batasan abin da take ba.Budar bakin ta ne sai tace. " duk da dai an kira abokin ango yayi nasa bayanin barin in Ιan baku tak'aitaccen nawa "." amarya Salima " tace tana kallon amaryar da tace kwalliya a cikin doguwar riga kalar ja itama, sai dai na amaryar bai kai na wannan budurwar kyau da tsaruwa ba, dan inbaka san wacce amaryar ba sai kazata itace.Salima wacce tun da yarinyar tafara magana ta ke ta faman bankamata harara, taja wani Ιan tsaki game da sake sakarmata wani hararan.Afra , yarinyar da ta ke kan stage in ta murmusa kafin tace ." ina taya ki murnar auran munafukin namiji, azzalume wanda bai san darajar mutane ba, ina kuma Ζara tayaki murnar samun daΖiΖin na namiji wanda ban da wata shakka Ζarshen sa bazai yi kyau ba, kuma ki kasa kunan ki kiji mijinko mayaudari ne, me bin mata ne kuma zan iya rantse miki fasiΖi ne "Read and find outβ¦