Tweenty tree

Background color
Font
Font size
Line height

#fatymasardauna

*Paidbook, Account details 0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz Bank, WhatsApp number 07069917168*

*23*

Nannauyar ajiyar zuciya Billionaire Dawoud ya sauk'e, gami da rumtse idanunsa saboda tambayar da yaji Soumaya'n ta jefo masa.
Tambayar dabai tab'a tunanin ji daga bakinta ba.
Haka kuma tambayar da tasanya wani miki nasa dawowa sabo, tare da sanya masa ciwo acikin zuciyarsa.

Yayinda lokaci d'aya kuma farkon abun ya soma dawowa cikin tunaninsa.
Wanda hakan yasa shi yin shiru, batare daya bata amsar abunda ta tambaya d'in ba.

Soumaya kuwa jin yayi shiru d'inne yasa ta sake sunkuyar da kanta k'asa, tare dajin wani iri saboda tambayar nasa da tayi, batasan hakan zai zamanto wani abu na daban ba da bata tambaya ba.
Wannan dalilin yasa ahankali ta d'ago ta d'an kalli Billionaire Dawoud d'in murya asanyaye tace.

"Abba bansan zakaji wani iri ba, kayi hak'uri bazan sake tambaya ba..."

"Meyasa bazaki sake tambaya ba? kina da hakk'in ki sani Soumaya, bawai Kuma nayi shiru ne dan banaso kisani ba, nayi shiru ne saboda neman k'warin guiwar da zata bani daman sanar dake, duk da bansan Tayaya zan misalta abunda nakeji ba, akoda yaushe ba komai ne yake zama kammalalle ba, sannan akoda yaushe sauda dama abunda mukeso bashi ne ke faruwa ba, wani lokaci hanyar da zaka bi daban, amma hanyar da zaka samu kanka aciki daban,
Yau Ina farinciki gobe kuma akasin hakan, zamu taso cikin samun nutsuwa da k'warin guiwa akullum, amma RANA D'AYA kawai, RANA D'AYA tak sai komai ya canja batare da katsarawa hakan ba, akan abu guda wacce bazaka tab'a iya sauya ta ba, domin rubutacciya ce acikin rayuwar kowa, rubutun da ba'a tab'a gogesa, Wannan abun ba komai bane fa ce K'ADDARA, k'addara ita  ke sauya rayuwar kowa Soumaya, ita ta sauya rayuwata da naki harma dana Majeed, da kuma na sauran mutanen duniya."

"K'addara."
Ta maimaita kalmar akan harshenta, tare da d'an d'agowa ta kalli Billionaire Dawoud d'in saboda rashin sanin inda kalaman nasa suka dosa.
"Meyasa koda yaushe kalmar Destiny ita kad'ai ake nanatawa acikin rayuwa? Meyasa kalmar ke gudana acikin jikin mutum kamar jini?."

Tayiwa kanta tambayar tana me neman amsar daga zuciyarta.
Saidai jin maganan Billionaire Dawoud d'in yasa ta yin shiru.

Inda araunace yace.
"Sunan MAJNOON ya shigo cikin rayuwarmu ne tun shekaru biyu da suka wuce, shine kuma sunan daya tsayar da farincikin mu, sannan shine wanda tabonsa ke manne ajikin gidannan yayi mana tambari,  bansan yaushe ne ba, bansan tayaya akayi ba, abu na farko da kunnuwana bazasu tab'a mantawa da jinsu ba shine k'ara da kururuwarsa, alokacin da yake kuka yana yaga duk wani sutura dake jikinsa, ban tab'a sanin tashin hankali ba sai awannan ranar, ranar da bazata tab'a gogewa acikin idanuna ba."

Ajiyar zuciya ya d'an sauk'e gami da fesar da numfashi kafun yaci gaba da cewa.

"MAJEED daban yake Soumaya, shi wani irin mutum ne da bai damuwa da kowa acikin rayuwarsa, koda yanajin damuwa shi kad'ai yake shanye kayan sa,  duk da kasancewa na amatsayin mahaifinshi amma babu shak'uwa sosai atsakanin mu,
Domin nakasance mutum wanda bashi da lokaci, bani da lokacin kaina balle nasa.

tun yana da shekaru 7aduniya Mahaifiyarsa ta rasu, Wanda hakan yasa shi komawa United State Of America da zama.
ASALINA
Soultan Bn Saoud shine sunan mahaifina wanda ya kasance balaren  k'asar Yemen, inda muka kasance mu biyu ne kacal y'ay'ansa, daga ni sai  kuma y'ar uwata Khaltoum, Aufana shine sunan mahaifiyar mu, Wacce takasance y'ar asalin k'asar Nigeria.
Wanda kuma aure ya had'ata da mahaifin mune sanadiyar had'uwar da sukayi a Madina, kasancewar iyayenta masu matsakaicin k'arfi anan Nigeria, hakan yasa ta tahowa aiki garin madina,  mahaifinmu Soultan kuwa kasantuwarsa d'an kasuwa, kuma ma'abocin zuwa garin madina hakan yasa shi had'uwar da ita, ya kumaji sha'awar aurenta, duk da cewar shiba k'aramin mutum bane yana da matuk'ar arzikin daya gada daga wajen mahaifinsa wato kakanmu Sa'oud, ya kuma sota ne saboda tsananin kyaun da take dashi, duk da cewar bata da hasken fata kamar na sauran y'an k'asashen duniya, amma tana da haske irin nasu nay'an Nigeria,  mahaifina da Mahaifiya ta sunyi aure bayan gwagwarmayar da suka sha, nak'in amincewar danginsu, inda acikin auren nasu ne kuma Allah ya azurtasu damu, cikin farinciki mukeyin rayuwa nida y'ar uwata Khaltoum, tun muna k'anana kuwa har izuwa girman mu, Saidai Ina da shekara 20 Khaltoum nada 17, Allah yayiwa mahaifiyarmu rasuwa, Wanda hakan yasa muka koma rayuwa da mahaifinmu wanda zuwa lokacin yatara arzikin dashi kansa baisan iyakarsa ba.
Saidai ba'a jima ba shima ya rasu, Wanda hakan yasa muka rage dagani sai Khaltoum, sai kuma y'an uwan mahaifin nawa.
ak'asar Yemen mu kayi  karatu dukanmu nida Khaltoum, Saidai Ina da shekara 25 nakoma England nakarasa duka karatuna acan.
Yayinda Khaltoum kuwa tana da shekara 24 tayi aure, ta auri wani balaraben Yemen, Wanda ya d'auketa zuwa Turkey acan suke rayuwa.
Alokacin dana taso na taso da burin kasuwanci kamar yanda mahaifina keyi, wanda hakan yasa tun ak'asar England d'in nafara kasuwanci, ta hanyar saka hannayen jari a company's daban daban, cikin sa'a kuwa komai nawa yana tafiya a daidai, akoda yaushe kuma ci gaba nake samu.
Saidai akullum burina bai wuce naga na kafa reshen kasuwanci na a Nigeria, wato k'asar mahaifiyata k'asar da nakejin sonta acikin ranta, domin kuwa koba komai Ina da alak'a da k'asar.

Ina da shekaru 27 aduniya na k'ara saka k'afata acikin Nigeria, bayan tsawon shekaru dana kwashe banzo ba, garin Kano shine inda na fara sauk'a, batare da b'ata lokaci ba na fara kasuwancin sayar da gold, kasancewar ina da jari mai k'arfi hakan yasa sana'ar tawa ta samu karb'uwa sosai,  duk da bancika zama anan dinba, amma inajin dad'in k'asar sosai.

Saboda akwai albarkan kasuwanci acikinsa.
Nasamu abokan kasuwanci na k'warai, Wanda suka d'aurani akan wasu business din maban banta,  hakan yasa na zama mutum marar lokaci koda yaushe ina hanyar zuwa k'asashe daban daban, musamman England wanda acanne tushen Company na *S* yake.
Haka kuma time to time nakan ziyarci K'asar  Turkey🇹🇷 inda y'ar uwata take aure, akuma wani zuwa da nayi ne na had'u da wata matashiyar budurwa a Instanbul me suna Azmah, wacce take y'ar asalin k'asar Kuwait 🇰🇼 tana kuma zaune ne a gidan marayu dake nan k'asar Turkey cikin garin Instanbul,  kasancewar ta taso marainiya bata da kowa sai k'anin mahaifinta, Wanda shine kuma ya kawota gidan marayu anan Instanbull d'in ya ajiyeta.

Azmah kyakkyawar macece sosai domin har yanzu zan iya cewa ban tab'a ganin wata mace me kyaunta ba, koda kuwa akwai To ni idanuna basa ganemin, wannan dalilin yasa  na matsawa son aurenta saboda tana da d'abi'u nagari, ga kuma jink'ai kasancewar bata da kowa sai iyayenta na gidan marayun ma'ana way'anda suka rene ta."

Numfashi ya d'anja kafun cikin sanyi yace.

"Inason Azmah Soumaya, Ina nufin so sosai, domin ita mace guda ce acikin dubu, duk da na fuskanci wasu k'alubale dangane da aurenta, amma hakan baisa na janye ba, cikin ikon Allah na samu aurenta, bayan nabi wasu matakai da kuma sharud'a da gidan marayun suka gindayamin,  na Aureta batare dason Khaltoum ba, saboda wani dalili nata daban da bansan shi ba, bayan munyi aure da ita munyi zama a Yemen na shekara biyu, kafun na d'auketa zuwa England, har zuwa lokacin kuwa bamu samu haihuwa da ita ba, Saidai sau d'aya ta tab'a samun miscarriage, shekaranmu 1 a England na d'auko ta zuwa Nigeria, saboda tace ta nason zuwa k'asar.
Saidai koda muka zo bata iya Hausa ba, haka nima bawai na iya bane, amma saboda sa kai dole haka muka koya, amma bawai sosai takeji ba nafita ji, ita dai takanji sama sama, yaren turkey kawai tafi iyawa sai kuma turanci daya zamarwa mutane jiki ayanzu,   Munajin dad'in zaman Nigeria sosai, domin koda nace da Azmah mu koma England k'i tayi, acewarta tafison nan saboda culture d'insu yayi mata yadda takeso, hakan yasa sau dayawa nakan zauna da ita, duk da bana samun isasshen lokaci amma ako yaya ita Ina bata lokaci, zan iya kashe appointment da kowa dan na zauna da ita, saboda ta taso acikin maraici banaso ta sakeyin wani maraicin, ahaka har Khaltoum ta haihu, inda ta haifi yaronta namiji me suna Soultan.
K'alubale d'aya da Azmah ta fara fuskanta shine rashin soyayyar da Khaltoum keyi mata, wacce ayanzu take amsa suna Lady Khaltoum, Saidai kasancewarta mai hakuri hakan yasa ta danne komai,  ana haka Khaltoum suka samu miss understanding da mijinta har yakaisu ga rabuwa, wannan dalilin yasa ta dawowa Nigeria muka zauna atare.
Acikin yanayin kuwa Allah ya kuma hawa Azmah ciki, ciki mafi soyuwa agareta, cikin da mukasa duk wani fatanmu akai.
Duk da yazo mata da yawan laulayi da kuma yanayi marar dad'i, haka kuwa mukaci gaba da renon cikin har saida yakai wata 8, kafun na d'auketa mukatafi Turkey, saboda tace acan takeso ta haihu, cikin ikon Allah kuwa tana cika 9 month, ta haifo yaro na Miji, yaron daya zama zakka haka kuma tsoka da jinin jikinmu, saboda tsananin kamannin da yaron keyi da ita ne yasa nakejin sonsa sosai, inamatuk'ar sonsa Saidai duk yanda nakai ga sonsa bankai Azmah ba, domin itace ta saka masa suna ABDOUL MAJEED."

Murmushi yayi tare da juyawa ahankali ya kalli daidai saitin d'akin Majeed d'in.

"Majeed! he's the reason for our happiness, he's the sous of our joy, Muna alfahari dashi akoda yaushe, domin zuwansa ya kawo mana sauyi arayuwa,  acikin shekaru 7 mun reneshi kamar sarki, mun bashi farinciki ingantacciya, mun inganta rayuwarshi ta hanyar sanyashi amakaranta mai kyau, Azmah tabashi kulawa fiye da yanda na bashi, domin akoda yaushe ita ke koyar dashi duk wani abu daya shafi addini, tun daga k'uruciyarsa yake da shiga rai, Saidai wani Hali nasa shine miskilanci, idan har yayi dariya to yana tare da Azmah ne, wacce yake kira da (Ammu) ko kuma ni mahaifinsa.
Wanda zuwa lokacin kasuwanci na yana ta hab'aka, inda muka bar Nigeria muka koma Russia da zama, saboda wani aikin kwangila da zanyi na tsawon shekara 2, muna acan d'inne kuma Azmah ta shirya dan zuwa turkey, saboda kai gudumawarta ga gidan marayun da ta tashi,  Hak'ik'a naso mu tafi tare Saidai hakan baisamu ba, saboda babu yanda zan iya tafiya nabar wannan aikin da nakeyi,  bayan haka ga kuma Majeed dake karatun primary a k'asar ta Russia, Wanda lokacin suna exam dole yasa ta tafi ta barshi, tafiyar da har yau na kasa mantata, tafiyar da tazama mafari na jefa Rauni acikin rayuwarmu...."

Rawar da taji muryarsa keyi ne yasa ta d'ago Idanunta ta kalleshi, dan hakan taji zuciyarta babu dad'i, musamman ko da taga hawaye acikin idanunsa, k'warai bata iya jure ganin hawayen babba, wannan dalilin yasa ta sunkuyar da kanta k'asa.

Billionaire Dawoud ko cikin rawar murya da sanyin jiki yaci gaba da cewa.

"Tafiyarnan itace ta nesanta mu da farinciki ta kusanta mu da bak'inciki, itace tafiyar data mai damu abun tausayi marassa galihu, Tafiyar da ta sauya rayuwar Majeed  daga dariya izuwa kuka, haka kuma tafiyar da har yau takesawa munajin kanmu amatsayin bamu da kowa,  domin ginshik'inmu bata dawo ba, Azmah bata dawo ba Soumaya, taje Instanbul da kwana 2 aka k'irani cewar hearattack ya bugeta ta fad'i ta rasu..... naji ciwo sosai munyi kuka kukan da har abada bazamu daina ba,  Saidai babu yanda zamuyi dole muka hak'ura, koda na gama Contract dina na shekara 2 kasa barin Russia nayi, saboda Majeed dake karatu ninake kulawa dashi, duk da bamajin dad'in zama da juna saboda acikinmu babu wani maifarinciki, ahaka har ya kammala Primary school d'insa, naso tafiya dashi England amma yak'I, haka yasa dole na nema masa makarantar gaba da primary anan Russia,  yayinda ni Kuma na tafi England nabarsa anan bayan na d'auki hayar me kulawa dashi, saboda Khaltoum tana can Nigeria, ta kuma ce bazata zo nan Russia'n ba.
A Russia Majeed ya kammala duk wani karatun secondary d'insa,  har zuwa lokacin kuma bansake waiwayan wata mace ba, duk da Khaltoum tace nayi aure amma har abada banajin akwai wata mace da zata kaimin Azmah, bayan haka kuma bani da lokacin kowacce mace, koda kaina ma banda lokacin sa, saboda kasuwancina da yake k'ara k'arfi, yayinda sunana ke yawo ak'asashen duniya, tun Majeed nasa shekara 18, na rantab'a sunansa amatsayin shugaban gamayyar company's d'ina na *S* wanda d'aya ke nan England, d'aya kuma yake Nigeria, Wanda dagacan England din ake k'era Kaya sai akawo su nan Nigeria, kasancewar kayan na'urori muke sarrafawa Fridge A/C dadai sauran duk wasu abubuwan na'urori,  A irin cigaban da kasuwanci na ke samu nafuskanci k'alubale da yawa, ina da hatters (Mak'iya.) daga k'asashe daban daban, haka ma Majeed Wanda yayi tasowar k'awa, saboda basiran da yake dashi wajen iya sarrafa computer, kasancewar sa ma'abocin karance karance shi yasa yake da k'wak'walwa sosai, succeeder ne shi mainasara akan komai, hakan yasa ya taso da son business kamar dai ni, Wanda zuwa lokacin ina cikin sahun masu kud'in duniya, saidai banason tara dukiya marar iyaka, wannan yasa akowanni shekara nake cire k'ud'ad'e masu yawa ina sadaka had'i da aikawa gidan marayu, musamman gidan marayun da Azmah ta rayu acikinsa,  shekarar Majeed 20 ya kammala karatun degree d'insa na farko ak'asar Portugal, inda daga nan kuma ya wuce London danyin Degree d'insa na biyu,  daga wannan lokacin kusancina dashi yaja baya, saboda bana samun wadataccen lokacin zuwa gareshi, haka shima koda naje yakanyi baya baya dani saboda wani dalili nasa da har yanzu bansani ba, ya kammala deegree d'insa na biyu, alokacin yana da shekaru 25, ya zama matashin saurayi mai rayuwa da samartakansa wajen aikinsa, yana taimakamin k'warai akan company na,  inda yana da shekara 27 ya bud'e nasa companyn *M&J dake k'asar Italy,  tun daga lokacin darajarsa take k'ara sama akoda yaushe, ni nakeyi masa wahalar gani amma sai yazamana shikemin wahalar gani, akowanni mujallu hotonsa ne yake yawo, kasancewarsa matashin saurayi da kud'i, yakan karb'i awards na matsayi daban daban,  yayinda nima nake nawa sana'ar, Saidai nakanzo Nigeria sab'anin shi da bai damu ba, domin ashekaru 4 baiwuce yazo sau 1 ba, nan ma idan yazo ko 1week ba yayi yake komawa, hakan ma kuma yakan zo ne kawai saboda yasan Ammu'nsa tarayu anan,   Hak'ik'a shekaru suntafi Soumaya, rayuwa kuma ta samu sauye sauye da dama, ci gaba ne ke faruwa akoda yaushe, sai kuma matsalolin da baza'a rasa ba, domin Majeed na girma na fahimci yana fama da wani irin matsanancin ciwon kai, duk da nakaishi asibitoti da dama amma abu d'aya suke fad'a, shine sun kasa gane kan ciwon,  Wanda hakan yasa dole muka hak'ura saboda pain reliever din da yake sha.
kamar kuma yanda nak'iyin aure haka ma y'ar uwata Khaltoum wacce take zaune anan Nigeria, Saidai time to time takan kai ziyara wasu k'asashe, yayinda d'anta Soultan ke aiki a k'asar Yemen, saidai shi yana zuwa nan akai akai saboda mahaifiyarsa,  Tabbas bazan iya fad'an wasu abubuwan banda Wannan ba, iyakansu shine abunda na sani, aduk sanda naso ganawa da Majeed To saina nemi appointment, kuskuren farko na rayuwata kuwa shine rashin sanin abunda ke zuciyarsa, bana gane damuwarsa Soumaya."

Hannu yasa ya share hawayen da suka zubo masa, cike dajin zafi rad'ad'i da kuma ciwon abunda zai fad'a d'in yace.

"shekaru biyu kenan yanzu da yake zaune awaje d'aya, ni kaina bansan meya dawo dashi Nigeria ba,  jin ya dawo Nigeria d'inne kuma yasa nima na biyoshi, Saidai abunda natarar ya zauta tunani na, saboda tunda nazo banyi ido hud'u dashi ba,  akullum kulle kansa yakeyi ad'aki me tsananin duhu, idan kayi masa magana kuwa baya amsawa, dafari nayi tunanin depression na kasuwanci ne ke damunshi, saboda amatsayina na d'an kasuwa nasan hakan na faruwa, Saidai abun ya soma girgizani alokacin dana fahimci cewa ko sallah bayayi ba kuma yacin abinci,  nasojin wani abu daga garesa amma Soumaya bansamu daman hakan ba, har yau bansan mene dalili ko musabbabin ciwon ba, rana d'aya kawai mukaji ihu da kururuwansa, daga wannan ranar kalmar MAJNOON ya hau kan sunansa, daga wannan Ranar Soumaya komai ya tsaya, bugun Zuciya had'i da fatan dake rayuwa acikin zuciyarsa duk suka mutu, Rana d'aya data kawar da kyakkyawan tunani, ta kuma sauya rayuwar Majeed, Wanda har izuwa yanzu yake zaune ahaka, aduniyar nan babu inda bamu shiga ba, amma babu maganin wannan matsalar abu d'aya doctors ke fad'a shine matsalarsa Mental problem ne, kuma daga cikin brain d'insa abun yake, k'wak'walwarsa ce ta tab'u acewarsu, ba'a kuma san ranar warkewarsa ba.... Inajin ciwo Soumaya akullum idan na kalli Majeed ahaka, tun muna b'oyewa duniya amma abun ya riga da ya bayyana, ko Ina jita jita ake cewar MDS shugaban companyn M&J ya haukace, ako Ina manema labarai neman gaskiyar lamarin suke amma munkasa basu daman sanin hakan,  ina cikin damuwa Soumaya, domin Majeed ahalin yanzu k'unci kawai ya sani, shi kad'ai yake rayuwa cikin kad'aici,  rashin Azmah yayi mana miki azuciya, domin da ace tana nan Majeed dole zai zamana cikin kulawa, amma duk da hakan ko kad'an ban tab'a kawo araina cewar na nema masa abokiyar zama ba,  saboda shid'in mai rauni ne, yana da tabo atattare dashi mai wuyar gogewa,  akuma sanin danayi masa, sau d'aya tak bai tab'a cewa yana son wata mace ba arayuwarsa, domin kowacce irin mu'amalace idan zata had'ashi da mata janye jikinsa yakeyi, Saidai koda Dr. Mouhammad Bulama ya kawo shawara akan anema masa abokiyar zama, bank'i ba kasancewar sa Family Doctor d'inmu, Wanda yake tamkar d'an uwa agaremu, domin shi yake kulawa da lafiyar Majeed d'in akoda yaushe, K'addara ce ta had'a ki damu Soumaya, K'addarar da bamusan me zata haifar ba anan gaba ba,  Saidai acikin d'an kwanakin  da kikayi acikin gidannan, nafahimci cewar MAJEED yana matuk'ar buk'atarki arayuwarsa, kece wacce zata zame masa bango kuma majingina Soumaya  Tabbas Kece..."

Billionaire Dawoud d'in ya fad'a yana me kai dubansa ga
Soumayan, bayan yasa abu ya share hawayen dake idanunsa.

Gami da d'an sakin murmushin dake bayyana ciwon dake zuciyarsa.
Batare kuma dayaji cewar zai iya jurewa zama acikin falon ba ya mik'e asanyaye ya fice.

Zafafan Hawayen dake gangarowa daga cikin idanunta ta sanya hannu ta share, had'i da d'ago kanta ahankali ta kai dubanta ga k'ofar d'akin nasa.
Wani irin rauni takeji acikin zuciyarta fiye da da, yayinda sassan jikinta kuwa ke amsar wani muhimmin sak'o dake gudana acikin jininta.

Wanda hakan yasa ta mik'ewa ahankali, cikin sanyin da jikin nata yayi ta nufi d'akin nasa.
Ahankali ta murd'a handle d'in k'ofar ta shiga bakinta d'auke da sallama, sallamar da tasan cewar babu mai amsa mata. 

Da mamaki d'auke afuskarta take k'arewa ko Ina dake cikin d'akin kallo, saboda rashin ganinsa da tayi wanda hakan yasa ta sakin k'ofar tare da k'arasa shigowa ciki,   Wanda sai alokacinne kuma idanunta suka sauk'a akan k'afafunsa da suka bayyana ta gefen kujera.

Hakan yasa ahankali da kuma yanayin sand'a ta soma takowa har zuwa jikin kujeran, zuciyarta nayi mata wani iri, yayinda takejin jikinta duk asanyaye, tamkar wacce takeson fashewa da kuka kuwa haka yanayinta yake.
Koda ta iso wajen kuwa kasancewar yana kwance abayan kujeranne yasa ta d'an lek'awa ahankali ta sauk'e idanunta akansa.

Sabbin hawaye ne suka silalo daga cikin  idanun nata, saboda ganinsa da tayi ahaka, inda yake kwance ya duk'unk'u ne jikinsa waje d'aya, tare da rumtse idanunsa.

Tabbas aduniya zata ce bata tab'ajin tausayin wani ba kamarsa, Rauninta akansa na daban ne,  haka ma abunda takeji akansa na musamman ne, bawai kawai acikin tunani da zuciyarta yake yi mata yawo ba, har cikin jini da b'argonta.

Juyawa tayi anutse ta k'arasa ta d'auko masa lallausan blanket din dake kan gadon, tare da pillow saboda tasan cewar dole ayanda ya kwanta ak'asan zaiji sanyi.

A tunaninta bacci yake wanda hakan yasa ta k'araso, tare da sunkuyowa asanyaye ta rufa masa blanket d'in, tare da durk'usawa akan guiwowinta.
Cikin nutsuwa ta sanya tafukan

You are reading the story above: TeenFic.Net