Tweenty six

Background color
Font
Font size
Line height

#fatymasardauna

*Paidbook, Amount 300, Account Number 0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz Bank*

*26*

K'aran fashewar wani abu da taji daga cikin d'akin Majeed din.
Abunda yasa zuciyarta mugun bugawa, Wanda hakan yasa ta fasa bin wanda taga ya fita din, da sauri ta nufi d'akin wanda yake awangale.

Wanda sako kanta cikin d'akin  kuwa yayi daidai da fashewar bedside lamp din dake cikin d'akin, Wanda hakan yasa ko Ina na d'akin yayi duhu dulum.
Abunda ya tilasta mata tsayawa, tare da jan jikinta baya, saboda sautin da kunnuwanta suka jiye mata, sautin da ya sanya ta jin wani irin shuuuuu acikin kunnenta, haka kuma sautin da ayanzu jinsa ya zame mata sabo.
Bawai kuma dan bata tab'a ji ba, kawai salon growling dinnasa ne ya canja.
Tamkar dai ganin da tayi masa na farko.
Kamar kuma an daki kanta haka taji wasu abubuwa na yawo acikinsu, Wanda hakan yasa ta soma jan jikinta baya, tare dasa hannu ta toshe kunnenta.

"Innallah!"
Shine abunda take fad'a alokacin da still take jiyo wani  k'ara like mutum yana buga kansa da bango,  Saidai bata tabbatar da hakan ba, saboda  idanunta da basa iya gane mata komai saboda duhun dake cikin d'akin.

"Meyake shirin faruwa ne? Waye wanda ya fita? Meyasa gurnanin da yakeyi ke k'ok'arin tar watsa k'wak'walwar kanta?."

Tayiwa kanta duka tambayar a lokaci guda, gami da yanayin rud'ewa batare kuma da ta tsaya jinkiri ba ta juya da sauri ta nufi k'ofar fita daga falon.

Sauri takeyi sosai had'i da tafiya mai kama da gudu gudu, yayinda take tsallake steps din da zai sauk'o da ita main parlorn da bibbiyu.
Wanda hakan yasa batare da ta kula ba tayi missing step, take k'afanta ya karkace ta fad'i akan last step din.
Wanda hakan yasa ta rumtse Idanunta tare da sakin siririyar k'ara.

K'aran da amon sautin sa yasa Billionaire Dawoud dake kokarin shigowa cikin falon k'arasowa da sauri.

Daidai lokacin ita Kuma ta yunk'ura ta mik'e tsaye, duk da cewar ta bugu sosai amma sam bata wani ji zafi sosai ba, saboda tunani da hankalin ta duk yana garesa.

"Soumaya."
Billionaire Dawoud ya k'ira sunanta da yanayin mamakin ganinta da yayi a daburce.

D'ago kanta tayi saboda jin muryarsa, tare da k'arasowa inda yake.
"Abba Maaa..."
Bakinta dake motsi yayi kokarin fad'in hakan amma Saidai harshenta yak'i bata daman sarrafuwa ta yanda zata ambaci sunansa.

"Maaa? Soumaya? Calm down meya faru  fad'amin me kikeson cewa?."
Billionaire Dawoud ya fad'a yana me k'ok'arin ajiye suit din dake hannunsa.
Tare da maida attention dinsa duka ga Soumayan.

Wacce ta rumtse Idanunta cikin fusgo muryarta daya sark'e tace.
"Abba Majeed ne."

"Majeed! Innalillah."
Billionaire Dawoud ya fad'a yana me haurawa saman da sauri, Wanda hakan yasa Soumayan bin bayansa.

Kusan atare suka shigo cikin falon, yayinda Billionaire Dawoud na gaba ita kuma tana biye dashi abaya.

"Majeed! Majeed!!"

Muryar Billionaire Dawoud ta karad'e d'akin wanda ya shigo amatuk'ar rud'e bayan yasa hannunsa yana lalub'ar makunnin wutan d'akin.
Inda cikin sa'a kuwa yana sauk'e hannunsa akan makunnin d'akin ya gauraye da haske.
Wanda hakan yasa idanunsu sauk'a akanshi.

Atare suka zaro idanu shida Soumaya'n, saboda ganinsa da da sukayi atsaye cikin yanayin fitar hayyaci yake gwara kansa da jikin bango, yayinda duk wani gaba dake jikinsa ke rawa karkar tamkar anjona masa shocking,  kallo d'aya zakayi mishi kuma kafahimci cewa baya cikin hayyacinsa. 

"Majeed!!"
Billionaire Dawoud ya k'ira sunansa cikin rud'ewa, tare da k'ok'arin k'arasawa inda Majeed d'in yake ya soma k'ok'arin rik'esa.
Saidai sam ya kasa yin hakan saboda k'arfinsa da na Majeed din ya sha banban.
Musamman ayanzun da yake yin komai cikin k'arfi.

Duk wani jijiyoyin dake jikinnasa sun mimmik'e, musamman jijiyoyin kansa da yake bugawa da k'arfi, ad'imauce yana sakin gurnani tamkar mayunwacin zaki.

Tare kuma da fusgo numfashinsa wanda ke k'ok'arin k'wace masa.

Hak'ik'a bunda yakeyi mai hankali bazai tab'a yinsa ba, tayaya mutum zai dinga cutar da kansa? Wannan wacce irin jarabtace ta hauka me nakasar da farinciki da kuma garkuwar zuciya?

Idanu Soumaya da jikinta ke rawa ta rumtse, Wanda hakan yasa hawayen dake tsiyaya daga cikin idanunta soma kwaranyowa tamkar an kunna famfo, ahankali kuma ta zame tare da zubewa akan guiwowinta, ad'imauce ta saki wani irin kuka mai sauti, kukan dake bayyana rauni da kuma tsananin tausayinta akansa.
Domin saboda hakan ji takeyi tamkar ana tsikarar naman jikinta tako ta Ina.
Bata tab'a ganin irin wannan abun ba tunda take, wani irin abune yake cutar da zuciya da gangar jikinsa? Bawai iya shi kawai ba acikin jininta takejin duk wani pain d'insa,  bata saba da Wannan ba, sai yaushe ne kuma zata koya? Ita yarinyace da har yanzu bata gama sani ko fuskantar menene k'alubalen rayuwa ba, a iya duniyarta abu biyu kawai ta sani, zama acikin farinciki da mahaifinta, sai kuma karatun ta wanda shi kawai tasa agaba, batare da ta damu da tsangwamar da Madou keyi mata ba, Saidai kamar yanda tayi imani kowanni bawa da irin Jarabtarsa, sannan da irin salon K'addararsa, ita sauyin rayuwa itace k'addarar ta, daga rayuwa da Abbou izuwa dashi.
Mutum mai damuwa da tarin rauni kamarsa, ta inane zata soma warware Wannan matsalan?

Kai ta soma girgizawa cikin yanayin kukan dake k'ok'arin cin k'arfinta kuma ta manna jikinta da bango.

Yayinda Billionaire Dawoud dake tsaye kuwa, duk ya fice acikin nutsuwarsa.
Musamman saboda yanda ya kasa iya control na Majeed din.

"Kabari Majeed.... Dan Allah..... , kabar cutar da kanka ya isa haka Majeed!!!......"
Muryar Billionaire Dawoud da tayi mugun rauni ta furta hakan, alokacin da yake sake k'ok'arinsa wajen ganin ya rik'e Majeed d'in, amma kuma abun yaci tura saboda yanda Majeed din ya tsaya da k'afafunsa babu wani abu dake nuna alamar akwai me iya matsar dashi daga wajen, domin duk wani surarsa na k'arfi ya bayyana.
Abunda Billionaire Dawoud bai sani ba kuma shine, Tayaya mutumin da baya cikin hayyacinsa zai saurari abunda kake fad'a har yayi aiki dashi?
Tabbas Majeed bazai iya jure abunda yakeji ba, kansa ne ke barazanar tarwatsewa, yayinda yakejin tamkar yata kururuwa ta yanda duka duniya zasu jiyosa, so yake yayi kuka yayi ihu ko zai fitar da abunda ke rikita masa k'wak'walwa da zuciya amma ya kasa, bashi da bakin fad'an abunda ke damunsa, kamar yanda bashi da k'warin guiwan yin kuka akan komai nasa.
Waye zai ji irin yanda yakeji acikin jikinsa? Waye zaiji ko kad'an daga cikin abunda yakeji ak'ahon zuciyarsa? Waye zai fahimci koda kad'an d'in abunda ya keji? Acikin kunnuwansa yakejin wani irin k'ara da kururuwa, kamar yanda acikin fatar jikinsa yakejin tamkar ana caccaka masa allura akan kowanni ma b'ulin gashin dake jikinsa,  wani irin matsanancin zafi yakeji daga tafin k'afarsa har zuwa tsakiyar kansa tamkar ana kwad'a masa gudu ma, dake sawa yakejin duniyar gaba d'aya na juya masa, komai ya k'wace masa, inda zai saka kansa yaji sauk'i kawai yake nema.
Domin babban abunda ya rasa ayanzun shine nutsuwar zuciya, Wanda hakan yasa zuciyar nasa ke bugawa da sauri kamar zata faso kirjinsa ta fito.

Har dai yanzu agigice ake matuk'a irin gigitar da tasa yake ci gaba da cutar da kansa, yana mejin kamar ya cire kannasa dake masa azabar ciwo ya wurgar.

"Innalillahi wa Inna ilahirraju'un Allahumma ajirni fi musibati wa'aklifni kayran minha!!!"

Shine abunda Billionaire Dawoud ke maimaitawa cike da tashin hankali, saboda ganin abun na kokarin wuce tunaninsa ne, yasa shi juyawa batare da sanin inda yake takawa ba kaitsaye ya fice daga cikin d'akin da sauri, yana me lalub'ar wayarsa dake cikin aljihunsa dan k'iran Dr. Mouhammad.

Soumaya dake durk'ushe kuwa Ganin hakanne yasa ta tasowa da sauri, ta k'arasa inda yake batare da ta damu da yanda jikinsa ke jijjiga da kuma gurnanin numfashin sa dake rikita lissafinta ba.

Isowa tayi dab dashi tare da rumtse idanunta cikin wani irin yanayi, ta d'aura hannunta akan tsakiyar bayansa kasancewar dama ya bata baya.

"Amor!!!"
Ta k'ira sunansa da muryarta wacce rabinta ta fito da sautin kuka.

Gami da durk'usawa ahankali ta zame akan guiwowinta, tare da rik'o k'afarsa na dama.
Cikin muryar kukan dake neman danne duk wani juriyarta jiki na rawa tace.

"Please stop Mi Amor! don't get your self injured please,  Its our destiny, I also feel the pain, I believe it will become history one day!!....  kabari dan Allah!!"

Cikin matsanancin kuka ta k'are maganan, had'i da sake rik'eshi k'am saboda babu d'aya daga cikin abunda yakeyi wanda ya daina.
Hasalima sakeci gaba da buga kan nasa yayi, Wanda zuwa yanzu har saman forehead d'insa ya fara fitar
da jini.
Sam ayanayin nasa nayau babu wata alama dake nuna cewar zaiji rarrashi.

Domin sauk'ar muryarta kawai acikin kunnuwansa, haka yasa shi jin tamkar ana juya Brain d'insa.
Musamman ayanzu da sautin kukanta ke dukan dodon kunnuwansa yana me k'ara birkita masa lissafi, yayinda acikin zuciyarsa kuwa yakejin tamkar ana watsa masa narkakken ruwan dalma dake k'ona cikin k'irjinsa.
Tabbas acikin ciwon nasa Wannan sautin kukan nata da yakeji, shine abu mafi ciwo da rad'ad'i agaresa.

Duk da akwai kalma d'aya acikin kalamanta wanda suka tsaya acikin brain d'insa, kalmar  da baya iya nanata ta abaki, amma zuciya da k'wak'walwarsa sun rik'e ta k'am.

"I believe it will become history oneday!"

Wannan kalmar itace kalma ta farko data fara zama acikin tunaninsa.
Kalmar da tasa shi jin wani abu, like hope, hope din da yayi losing tsawon shekaru.

d'ik d'ik. sautin k'aran wani abu daya soma d'iga a kan hannunta, yasa ta saurin bud'e idanu, tare da sauk'e ganinta akan fatar hannun nata wanda jinin forehead d'insa ya soma d'iga akai.

Arazane ta zazzaro idanunta waje, gami da janye hannunta cikin sauri kuma ta mik'e tsaye saboda tayi imani cewar, har abada bazata tab'a iya jurewa ganinsa acikin irin wannan yanayin ba.

Saurin shigewa gabansa tayi, Wanda hakan yayi daidai da saka kansa da yayi ajikin bango zai buga, da sauri ta rik'osa tana me fashewa da sabon kuka.
Akaro na biyu kuwa da raunatacciyar murya tace.

"Dan Allah kabari...... dan Allah!!!"

Idanunsa da sukayi jajur ya kuma rumtsewa, batare da ya bud'e su ba kuma, ya sanya duka hannayensa biyu ya rik'o  y'an siraran damatsanta,  wani irin rik'o da saida k'ashinta yayi k'ara.
Still Batare da yasan abunda yake shirin yi ba, ya soma buga forehead din nasa akan shoulder d'inta da iya k'arfinsa.

A azabce ta lumshe nata idanun, alokacin da taji k'ashin kafad'unta sun amsa, Wanda asanadiyar hakan har saida taji legs dinta sun sauki rawa.
Already hannayenta kam dama jinsu tayi tamkar basa jikinta, saboda yanda yayi mata wani irin rik'o tamkar zai b'allata biyu.
Saidai ba damuwarta ita kanta ba, damuwarta shi ne, bata damu da taji rauni ko akasin haka ba, abu d'aya kawai takeso shine ya samu relief.
Duk da cewar tanajin zafin yanda yake buga kansa a shoulder d'inta amma ta fahimce shi.
Bayi da wani zab'in daya wuce haka.

Daidai lokacin kuwa Billionaire Dawoud da kuma wani Dr. Uthman dake biye dashi abaya suka  turo k'ofar d'akin suka shigo da hanzari, inda Lady Khaltoum dake biye dasu batare da sun sani ba, ta sake matsowa jikin d'akin, tare da zuro idanunta ta tsakankanin k'ofa tana kallonsu.

Cak Billionaire Dawoud ya tsaya saboda abunda ya gani, Wanda hakan yasa cike da tashin hankali yace.

"Kayi wani abu Dr. Uthman inajin tsoro kada ya cutar da ita, duk da bai tab'a cutar da wani ba, amma zai iya cutar da ita sannan Kuma ya cutar da kansa."

Kai Dr. Uthman ya jinjina, tare da fiddo da jakar kafad'arsa, ya soma b'are wasu sabbin allurori manya, irin dai alluran nan da akeyiwa dokuna masu manyan syringe.

Ruwan alluran mai tsananin maik'o dake cikin wani kwalba ya zuk'a acikin syringe din, bayan ya saka kan alluran.
Kamar kuma yanda k'a idar alluran take cikin shammata akeyinta.
Hakan yasa shi takowa ahankali adaidai gefen wuyan Majeed d'in na dama, ya caka alluran da k'arfi kan d'aya daga cikin tarin jijiyoyinsa da suka bayyana.

Tare da zuk'e ruwan alokaci d'aya cikin hanzari.

K'aran azaba Majeed d'in ya saki alokacin da yaji zafin ruwan alluran na ratsa kowacce jijiyar jikinsa, Wanda hakan yasa shi sake rik'eta k'am, had'i da mannata da bango a d'imauce ya manna jikinsa da nata.

Siraran hawayen dake kwance acikin Idanunta ne suka silalo kan fuskarta, alokacin da taji yana janye jikinsa daga nata, har zuwa sanda ya kifa duka guiwowinsa ak'asa,  cikin yanayin bazata kuwa taji wani abu mai tsananin d'umi da taushi ya kamo hannunta ya rik'e k'am.
Abunda ya sata bud'e idanunta kenan ta sauk'esu akan hannunsa daya  rik'o nata.

Fuskarsa ta kalla had'i da zaro idanunta waje, saboda ganin yanda fuskar tasa tayi jajur yayinda idanunsa kuwa sukayi luhu luhu, then ga kuma jini dake bin gefen fuskar nasa.

"Amor! Amor!!"
Ta k'ira sunansa ad'an razane tare dasa hannunta ta soma goge masa jinin da sauri, gami da durk'usawa agabansa.

"Amor!!!"
Ta fad'a da k'arfi tana me jijjigasa saboda wani irin zazzafan zazzab'i da taji ya sauk'a ajikinsa.

"Don't worry Insha Allah he'll be fine, karku damu da zazzab'in k'arfin alluranne ya sa masa, amma Insha Allah zuwa nanda 3am komai zaiyi normal, alluran side effect dinta ne sanya zazzab'i mai zafin gaske, amma tana samar da relief ga mutane masu irin ciwonsa."

Ajiyar zuciya Billionaire Dawoud ya sauk'e, gami da k'arasowa wajen cikin sanyin jiki.
Hannayensa duka biyu yasa had'i da soma kokarin d'ago Majeed d'in.
Wanda ganin haka yasa Dr. Uthman taimaka masa suka shumfud'e Majeed d'in akan gado.
Duk da bawai ya fita ahayyacinsa bane, Saidai babu wani abu na jikinsa dake motsi in banda idanunsa da suka juye zuwa kalan maye.

"Ina fatan watarana Majeed ya samu lafiya Dr. Uthman, sai yaushe ne zai fita daga wannan wahalan? Yaushe ne zaiyi rayuwa da hankali da kuma nutsuwa, yaushe zaiyi tunani da k'wak'walwarsa kamar yanda kowa keyi? Wanni irin ciwo ne haka da bayajin magani, every week allurai akeyi masa, Wanda ak'alla kud'in kowanni allura d'aya yakai 150k, alluran ma da daga k'asar waje ake shigo dasu,  amma babu canji har yau, munsa ana yi masa sauk'an karatu aduk sati, munyi magunguna da yawa amma Wannan ciwon bashi da alamar sauk'i...."

"Karkace haka Billionaire Dawoud Saraki Insha Allah Majeed zai samu lafiya watarana, mu dukanmu musulmai ne kuma munyi believing cewa kowanni tsanani yana tare da sauk'i, amma ni kaina Ina mamakin ciwon Majeed, duk da cewa muna tare da irinsu a Hospital, amma nashi yayi worst saboda bayajin kowanni irin magani, saidai komai zai wuce watarana, dama cuta tana shiga ne lokaci d'aya amma sauk'i sai ahankali kar hakan ya dame ku."

Dr. Uthman ya fad'i hakan cikin tausasawa, gami da sunkuyawa kan Majeed ya soma treating forehead din nasa daya fashe.
Anutse ya kammala komai tare da sa masa bandage ya rufe wajen, bayan yasa magungunan da zasu rage masa rad'ad'in ciwon.

D'ago da kansa yayi ya kalli Billionaire Dawoud dake tsaye, cikin kulawa yace.

"Yana buk'atar hutu sosai, saboda kwakwalwarsa ta samu ta d'an huta, domin da alama duk da gangar jikinsa basa aikin k'arfi, amma kwakwalwarsa nayi, Wanda hakan ke k'ara haifar masa da damuwa da kuma yawan ciwon kai, kuma bayan haka akwai chronic ulcer ajikinsa, itama kuma tana taimakawa wajen sakawa mutum damuwa, haka kawai sai mutum yanajin kansa acikin tashin hankali, ko mutum taji yana yawaita tsoron wani abu dashi kansa baisan menene ba, saboda ita chronic ulcer tana amfani ne da abunda yafi tasiri ajikin ka, for example idan kana da yawan ciwon kai, To ta kanbi jikin Wannan ciwon kan sometime sai pain din yayi yawa, ta hanaka samun sukuni kwata kwata, ko ta hanaka bacci domin tana zuk'e ruwan jiki, haka kuma tana janyo problems da yawa,  saboda haka ya kamata akiyaye ci da shansa, matsalarsa babbace amma kowacce matsala tana sake worst ne idan chronic ulcer ya shigo ciki, duk da dayawan mutane basu d'auki Ulcer as serious ciwo ba, amma ciwo ce da illanta ya wuce tunanin d'an Adam saboda haka akiyaye."

"Insha Allah Dr. Uthman, mungode sosai."

Billionaire Dawoud ya fad'a yana me mik'a masa hannu sukayi musabaha, yayinda shi kuwa Dr. Uthman din jakarsa ta likitoti ya d'auka tare da rataya ta akan shoulder dinsa.

Cikin nuna tausayawa yace.
"Babu wani damuwa, yanzu saboda arage masa zafin zazzab'in ya kamata ak'ure gudun A/C, sannan idan da hali arage masa kayan jikinsa, akuma samo ruwa ana shafa masa ajikin nasa domin temperature dinsa yayi high."

"Insha Allah."
Billionaire Dawoud ya fad'I hakan, cikin yanayin damuwa gami da juyawa ya bi bayan Dr. Uthman d'in dake k'ok'arin fita.
Ganin hakanne kuma yasa Lady Khaltoum dake tsaye saurin shigewa cikin labule, har suka wuce batare da sun ganta ba.

Ita kuwa ganin sun wuce d'inne yasa ta binsu da kallo, yayinda fuskarta ke d'auke da wani irin yanayi na kokonto.
K'aramin madaidaicin kwalban dake hannunta ta d'aga tare da dubawa.

"Waye wannan? Duk way'annan abubuwan na meye? Meyasa yake rigani akan komai? Nasan dudduniyar nan babu Wanda yasan shiri na saini kad'ai, amma meyasa duk wani abu da nakeson aiwatarwa yake rigani cimmasa,  na turo asawa Majeed maganin nan a drink yasha, but d'an aiken ya koma ya sanar dani cewa ya samu Majeed d'in acikin mawuyacin hali, ya rigani shirya komai, kafun na aiwatar yake ida nasa, wayeshi! Wayeshi?."

Tayi maganan cikin tashin hankali had'i da soma yin safa da marwa acikin falon, saboda tunaninta dake neman tsayawa cak.

A iya tunaninta ita kad'aice bak'uwar da ta shigo cikin  gidan ayau, bayan ita kuma babu wani Wanda ya sake zuwa, to waye kenan? Waye wanda yazo da wani abu na daban ya sake warzaga nutsuwar Majeed?

"Wani daga cikin gidannan ne, wani mafi kusanci dako ina."

Wani sashi na zuciyarta ya amsa mata da hakan.

Wanda yasa atake ta zaburo ta re da soma jinjina kai don ta aminta da hakan.
"Hak'ik'a koma waye acikin gidan nan yake, dashi muke rayuwa, haka kuma mutum ne mafi kusanci,  To amma daga Ina yake? masu bawa flowers ruwa? Kuku's? Drivers or gates men?, Daga ina ne lallai inaso na sani!!"

Ta k'are maganan cikin damuwa, batare da ta tsaya ba kuma cikin sauri ta nufi k'asa.

Yayinda ab'angaren Soumaya kuwa fitan su Billionaire Dawoud ne yasa ta, tashi daga durk'ushen da take, tare da takowa ahankali ta k'araso jikin gadon.

Idanu ta zuba masa saboda yanda yake kwance flat, yayinda dogon gashin kansa ke watse akan pillow'n da su Billionaire Dawoud sukayi masa matashin kai dashi.
Tabbas kallo d'aya zakayi mishi kafahimci cewar babu wani abu na kuzari atattare dashi.
Sai idanunsa wanda suke kallon gefe, duk da suma sunyi luhu luhu amma basu rufe rub ba, yayinda jijiyoyin jikin nasa kuwa har yanzu ke bayyane rud'u rud'u more especially jijiyoyin hannayensa da kuma na saman goshinsa.

Ajiyar zuciya ta sauk'e tare da sunkuyowa kansa ahankali, tasa hannunta na dama ta shafa saman goshinsa.

Sakalallun Idanunta ta lumshe saboda yanda taji jikin nasa zafi Zaauuu kamar wuta.

"I'm sorry Mi Amor!!!."
Ta fad'a cikin sanyi da kuma tattausar muryarta wacce ta k'arayin sanyi saboda kukan da tayi.

Wanda amon sautin yasa shi juyo da sexy eyes din nasa zuwa kanta.
Ya kafeta dasu yana meyi mata wani irin kallo, da yasa tsikar jikinta soma motsawa.

Inda jin hakan yasa itama d'ago da idanunta masu d'auke da shek'in hawaye ta kallesa.
Ido acikin ido sukayiwa junansu, Wanda hakan yasa heart dinsu normal beating atare.

Kamar kuma yanda yake abayyane ita ta fara janye idanunta daga kan nasa, yayinda shi kuwa ya maida duka kallonsa ga jajayen soft lips d'inta, Wanda suke d'auke da danshin hawayen ta da suka zuba

You are reading the story above: TeenFic.Net