Tweenty seven

Background color
Font
Font size
Line height

#Fatymasardauna

*Paidbook, Amount 300, Account Number 0002224625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz Bank, WhatsApp number 07069917168*

*27*

Ya k'are maganan yana me sanya hannunsa akan screen din laptop din yana shafawa.

Cike da shauk'i had'i da fatan isa ga tsohuwar ajiyarsa, ajiyar da ya adanata tsawon shekaru, haka kuma yake da fatan  cimma buri da manufarsa akanta.
Tabbas ak'age yake dason zuwa gareta, duk da zuciyarsa na tafarfasa da kuma k'una akan tsananin kishinta da yakeyi.

*8: 00 pm*
K'aran knocking door din da akeyi ne ya soma ratsa cikin kunnuwanta, gami da kutsawa cikin mafarkin da takeyi, Wanda yasa ta had'a gumi lokaci d'aya, duk da masifaffen sanyin A/C'n dake tashi acikin d'akin.
Wannan dalilin yasa ta sake gyara kwanciyar nata ahankali, gami  da matse jikinta waje d'aya, da yanayi irin wanda ke bayyana pain din dake damunta.

Tabbas bawai acikin baccin ta ba kawai har azahiri k'aran bugun k'ofar ya dame ta, Wanda hakan yasa ta soma bud'e idanunta wanda sukayi nauyi.
Inda ta sauk'esu akan wani pink rose dake gefen gadon.
Numfashi taja da d'an k'arfi saboda rashin sanin inda take, Wanda ganin ta acikin bak'on waje yasa ta k'arasa bud'e idanunta da sauri tare da tashi zaune.

"Wayyo Allah!"
Ta fad'a da raunanniyar murya, saboda wani irin ciwo da taji na sukan k'asar mararta, ciwon da ya nhanata sakat acikin baccin nata.
Yayinda lokaci d'aya kuma duk abubuwan da suka faru a daren jiyan suka soma dawowa cikin brain dinta filla filla.

Sassanyan numfashi taja saboda sai alokacin taji wani irin abu nabin duk kan sassan jikinta.
Wanda hakan yasa ta juyawa ahankali ta kalli b'angaren damanta.
D'ar idanunta suka sauk'a akan kyakkyawar fuskarsa, Wacce take jajur yayinda fatar saman madaidaitan idanunsa sukayi luhu luhu, like Wanda ya sha kuka ya k'oshi.
Ga kuma zara zaran eye lashes d'insa da suka kwanta lub ak'asan idanun nasa dake arufe.
Numfashi yake fitarwa ahankali, Wanda hakan ke nuna alamar cewa bacci yakeyi musamman idan akayi la'akari da yanda beautiful lips d'insa suka d'an bud'e kad'an, domin  da taimakon hakanne yake shak'an numfashi gami da fitarwa yanda ya kamata.

Bak'i banci da idanu ta bud'e tana kallonsa, dan haka takejin tamkar yau ne ganinta
dashi na farko.

Kwantaccen black beard din da yayiwa fuskarsa k'awanya ta tsurawa ido, tana me kallon yanda gashin wajen ke kwance lub, yayinda lips d'insa me 3 colors ya  k'awata kyakkyawar fuskar tasa.
Lips din da bata tab'a ganin wani mai irin su ba, saboda kai tsaye baza'a ce musu Red ba, Saidai ak'irasu da  pink color, me mix da d'an black saboda basuyi kala da light pink ba.

"Kyakkyawa ne shi, kyakkyawar da k'addara ta musanya rayuwarsa, ba ni kawai ba, kowa ma ahaka idan ya kallesa bazai tab'a kawo cewar akwai nak'asu acikin rayuwarsa ba,  K'addara tayiwa rayuwarsa tsinke , ta hanyar sauya masa gabansa izuwa baya."

Wani sashi na zuciyarta ya fad'i hakan,  tare da soma sun dawowa da brain d'inta kalmar da ake jifansa dashi.

*MAJNOON* sam bata yarda da Wannan kalmar ba, domin kuwa bataji ajikinta cewar shi Majnoon ne, ba kuma ta fatan ranar da kalmar zata d'auru agaban sunansa.

Domin ita awajenta shi ha MAJNOON bane kamar yanda kowa ke d'auka.
Idanunta basayi masa kallon Mad, saboda haka har abada shi wani na dabanne agareta.

Idanunta da akullum suke da saurin kawo ruwan hawaye ta lumshe, tare da kawar da kai daga kallonsa bayan taja dogon numfashi akaro na barkatai, saboda tayi imani cewa kallonsa kan iya zautar da tunaninta, musamman ayanzu da takejin wani irin abu na yawo acikin jini da tsokarta dangane dashi.

Wannan dalilin yasa ta d'an muskutawa ahankali tare da zuro k'afafunta k'asa daga kan gadon.
Asanyaye ta mik'e tare da juyawa ta soma tafiya cikin sand'a gudun kada ta tashesa daga baccin da yakeyi. 

Saidai taku biyu kacal tayi taji mararta tayi wani irin rik'ewa, tare dajin wani abu mai kama da hajijiya na neman kada ita. hakan yasa da sauri ta dafe bango.
Had'i da cije lips d'inta saboda tasan cewa yau d'in ranar wahalarta ce ta tsaya.
Saidai babu yanda zatayi kasancewar har yanzu ba adaidai knocking k'ofar falon ba yasa ahankali ta murd'a handle d'in k'ofar d'akin ta fice.

Fitowa falon tayi cikin dauriya da kuma b'oye ciwon dake damun nata ta k'arasa ta bud'e k'ofar.

"Good morning."

D'aya daga cikin masu kawo musu abinci, Wanda shi yake ta knocking d'in almost 10mn ya  fad'a yana me sunkuyar da kai, had'i da mik'o mata babban tray din dake hannunsa.

"Morning."
Soumayan ta amsa masa akasalance, gami dasa hannu ta karb'i tray d'in, batare da ta bashi daman shigowa ba kuma ta maida k'ofar ta rufe.

Kamar koda yaushe akan table din dake tsakiyar falon ta ajiye tray d'in.
Ba tare da tsaya duba abincin ba kuma kaitsaye ta nufi d'akin da yake masauk'inta.

Tana shiga ko ta turo k'ofar tare da soma yunk'urin rage kayan jikinta, inda idanunta ke kallon agogo, Wanda yake nuna mata k'arfe takwas da mintuna sha biyu.

Tabbas tasan yau dolenta tayi missing paper guda d'aya, saboda bayan makaran da tayi batajin zata iya zuwa makaranta ayanayin da take ciki, ga kuma shi da yake kwance, bazata iya yin nisa dashi ba ayau d'in, bazata tab'a tafiya batare da taga farkawan sa ba, saboda tana matuk'ar tsoron ya farka da pain irin wanda ya kwana dashi daren jiya.

Doguwar rigar dake jikin nata ta zame gami da d'aura towel kaitsaye ta wuce bathroom.
Inda koda ta shiga ruwan d'umi ta sakarwa kanta.
Bayan tayi wankanne kuma ta fito jikinta sanye da bathrobe.

Tana me tafiya ahankali yayinda duk fuskarta yayi kalan tausayi saboda zuwan period d'inta.
Wajen kayanta ta nufa saboda sanin akwai sauran pad dinta da Inna Hauwa ta had'o ta dashi.
Wanda gashi hakan ya taimaketa domin da ace babu pad din batasan ya zatayi ba.

Pad din ta sanya ajikinta, bayan ta shafa body lotion ne kuma ta zaro wani riga da skirt tare da sanyawa.
Saidai kasancewar skirt din nada fad'i yasa surar jikinta rufuwa, yayinda top shirt din da tasa mai guntun hannu kuwa ya bayyana lafaffen stomach shape dinta, da kuma madaidaitan breast nipple dinsa, kasancewar batasa bra ba, saboda ciwon da sukeyi mata, Wanda already ta saba dama duk lokacin da take period sukanyi mata ciwo.
Kamar koda yaushe dake gyara parking hair dinta tayi, tare da rufe kan nata da wani siririn vail din daya sauko har kirjinta.
Sassanyan tutaren Calvin Klein Women ta fesawa jikinta, Wanda hakan yasa duka d'akin ya d'auki k'amshinta.

Kamar yanda yake ko bata wani saba da kwalliya ba, shiyasa bata gwada yi kwata kwata, sometimes haka take barin natural face dinta,  Wannan yasa yanzun ma bata matsawa kanta ba,  tana gama shiryawa ta juya ta fice daga cikin d'akin.
Saboda tasan zamanta waje d'aya zai iya sawa menstrual pain din ya matsa mata.

Falon ta fito da yanayinta na kasala, tare da zama akan kujera ta soma bubbud'e plates d'in dake kan tray din.
Yau madai abincin daban suke dana sauran rana ku.

plate din farko Grilled Tallapia fish ne aciki, sai kuma next plate dake d'auke da Chicken Caesar salad, then Parsley  patatoes and scrambled eggs, last plate kuwa shike d'auke da moonies  banana pancake.

(Parsley potatoes and scrambled eggs. Ingredients: patatoes, 2 tsp salt for boiling patatoes + more or to taste for seasoning the patatoes, 1 bay leaf, optional 3/4 cups unsalted butter melted 1 bunch parsley, finely chopped (1 cup) Methood:  1) cook your patatoes in water with salt and 1 bay leaf till soft and tender (2) drain your patatoes (3) drizzle your melted butter over the patatoes and toss to coat (4) sprinkle with 1/2 tsp salt or taste. Add 1 cup chopped parsley and toss to combine. Toss again just before serving!  For the egg sauce. ingredients.    4 large eggs _ chopped tomatoes_ chopped onions_ seasonings_ salt to taste_ melted butter_ evaroped milk_ chopped green bell peppers and some sweet corn. Method: 1 crack your eggs in a bowl add in your evaporated milk and whisk. 2 in your pan add in your melted butter. 3 add your chopped onions and tomatoes stir fry. 4  add in your chopped green bell pepper. 5 then seasonings of your choice and salt to taste. 6 pour gently your egg mixture and scramble! scramble!! 7 add in your sweet corn. 8 saved with your   boiled parsley patatoes.).

Komawa tayi ahankali ta jingina bayanta da jikin kujera bayan ta gama duba duka abincin, Wanda sam batajin cin kowanne daga cikinsu.

Idanunta ta kuma lumshewa, kamar meyin tunani wani abu, Saidai azahirin gaskiya ba hakan bane, koda ma akwai abunda take tunawa d'in to baiwuce mafarkin da tayi daren jiya.
Mafarkin da ta kasa sanin ma'anar yinsa, da kuma rashin fahimtan abunda yake nufi.

Gudun kada wani tunani ya shigo cikin brain dinta ne kuma yasa ta tashi, kaitsaye ta nufi d'akin nasa, bayan ta murd'a handle d'in k'ofar ta shiga da sand'a.

Har yanzu bacci yake domin kuwa bai motsa daga inda ta barshi ba.
Ganin hakan yasa ta sauk'e sassanyar ajiyar zuciya, tare da k'arasowa cikin d'akin ta soma kimtsa duk wani abu dayake ba daidai ba.

Hak'ik'a ko acikin bacci bayajin zai iya missing najin motsinta, wannan dalilin yasa tun shigowarta kunnuwansa suka jiye masa alama, Wanda hakan yasa shi katse baccin da yakeyi d'in, batare kuma daya bud'e idanunsa ba.
Saima lafewa da yayi yana me sauraran bugun zuciyarsa.

Soumaya kuwa gama tattare d'akin da tayi ne yasa ta k'arasowa wajen gadon nasa, tare da sunkuyowa ahankali ta d'an rank'wafo kansa.

Tafin hannunta na dama ta d'aura akan forehead d'insa, cike da fatan Allah yasa fever din nasa ya sauk'a.
Saidai akasin fatan nata da ya kasance ne yasa ta janye hannunta da sauri, saboda har yanzu jikin nasa akwai zazzab'i sosai.

"Har yanzu fever din bai sauk'a ba."
Ta fad'a araunace tare da d'an zama abakin gadon.
cikin sanyi ta jawo blanket ta rufa masa.
had'i da kifa kanta atsakankanin cinyoyinta, domin zuwa yanzu ita kad'ai tasan wani irin ciwo saman marar nata keyi mata.

Majeed kuwa hakan da tayi d'inne yasa shi bud'e idanunsa ahankali ya sauk'esu akanta.
Duk da cewar shi kansa baisan me yake kallo atattare da ita ba, amma hakanan yaji idanunsa sun tsaya akanta.
Saidai bashi da ikon fahimtar yanayin nata.
Wanda hakan yasa dole ya maida idanunsa ya rufe.

Daidai lokacin ne kuma aka turo k'ofar d'akin wanda hakan yasa Soumayan, d'ago kai ahankali inda ta sauk'e ganinta akan Billionaire Dawoud, Wanda shi d'inma ita yake kallo da mamaki akan fuskarsa yace.

"Soumaya mekikeyi haka? Ko dai Yau babu makaranta ne?"

Kai ta sunkuyar saboda batason ya hango rauni da kuma ciwon dake cikin idanunta, hakan yasa cikin dauriya tace.
"A'a Abba akwai kawai dai na makara ne shiyasa banje ba."

"Makara kuma Soumaya? are you okay?"
Billionaire Dawoud ya tambaya, da yanayin damuwa saboda sanyin da yaga duk jikinta yayi.

"I'm okay Abba."
Ta fad'a tana me cije lips d'inta had'i da sanya hannayenta duka biyu ta dafe k'asan mararta.
Saboda wani irin murd'awa da taji yayi, ga wani sabon ciwo dake k'ok'arin b'allo mata without control.

"You're not okay Soumaya, me yake damunki haka? kodai baki da lafiya ne?."
Billionaire Dawoud d'in ya sake tambaya adaidai lokacin da ya k'araso tsakiyar d'akin.

Kasa amsawa Soumayan tayi saima sunkuyar da kanta da ta sakeyi, had'i da soma fusgar numfashi, saboda ciwon nata ako yaushe da haka yake zuwa mata, da yayi worst to numfashinta zai fara seizing.

"Soumaya tell me what happen, karkiji komai kema y'ata ce kamar yanda Majeed yake Biological son d'ina, saboda haka ki fad'amin duk wata damuwar da ta dame ki."

Abban ya fad'a atausashe saboda ayanzu ya gama yarda cewa bata da lafiya.

Bakin ta ta bud'e daniyar yin magana amma sai taji harshenta yayi mata nauyi wanda hakan yasa, cikin shaking voice tace.
"Ciki na ne yake ciwo."

"Subahanallah sannu bari nak'ira ko Dr. Uthman ya duba ki, domin ayanzu yafi kusa damu akan Dr. Muhammad."

Billionaire Dawoud d'in ya fad'a yana me zaro waya daga cikin aljihunsa, bayan ya danna k'iran Dr. Uthamn d'inne kuma ya juya ya fice daga cikin d'akin.

Soumaya kuwa zamewa daga kan gadon tayi ta zauna dab'as ak'asa, had'i da rumtse idanunta, bayan ta sanya hannayenta duka biyu ta kama mararta.
Breath take fitarwa da sauri sauri.
Wanda sautinsa yasa shi bud'e idanunsa, da akaron farko yaji ya kasa iya sarrafasu.
Duk da yanason juyasu kuwa amma ya kasa, wannan dalilin yasa shi jin tamkar ana sukan kowanni gab'an jikinsa da allura.

Ab'an garen Billionaire Dawoud kuwa Mintuna 10 kacal ya d'auka, sai gashi ya dawo cikin d'akin, yayinda Dr. Uthman ke biye dashi.
Wanda ganinsa yasa zuciyar Soumaya tsinkewa, dan tasan dole sai yayi mata allura, abunda tafi tsana arayuwarta.
Hakan yasa ta soma jan jikinta baya tare da yayyarfa y'an yatsun hannunta, tun kafun Dr. Uthman din yakai ga tambayarta abunda ke damunta.

Daidai lokacin ne kuma mota k'irar 2020 Lexus GX 460,  ta danno kai cikin gidan, bayan maigadi ya wangale babban gate d'in gidan.
Wanda hakan yasa shi sako kai cikin compound d'in gidan.
Da k'warewa yake murza siterin motar, har ya k'araso tsakiyar gidan, Wanda hakan yasa shi parking motar.

Idanunsa da sukayi ja ya lumshe, alokacin daya zuk'i cigarette, had'i da busa hayak'in.
Hayak'in da yakejin tamkar daga azuciyarsa wacce keci da wuta yake fitowa.

Bud'e murfin motar yayi ya fito, akan fuskarsa babu ko d'igon murmushi kaitsaye ya nufi cikin gidan, bayan yasaka k'afarsa ya take sauran cigarette din da yasha.

Yayinda acan b'angaren Soumaya kuwa, tsoro ne ya cika ta saboda ganin Dr. Uthman din na had'a wani ruwan allura dake hannunsa, batare kuma daya tambayeta me yake damunta ba.

Wanda hakan yasa cikin sanyi tace.
"Dan Allah Dr. karkamin da zafi."

Murmushi Dr. Uthman da Billionaire Dawoud sukayi, saboda tsoro da suka hango k'arara acikin idanunta.

"Bazanyi miki da zafi ba, ai kinsan alluran ciwon ciki bata da wani zafi sosai."
Dr. Uthman din ya fad'a yana me nufo ta da alluran wanda hakan yasa ta sanya hannunta batare da sanin abunda takeyi ba, kuwa ta daura hannunta akan kirjinsa daidai saitin zuciyarsa.

Had'i da rumtse Idanunta da k'arfi.
Wanda hakan yayi daidai da turo k'ofar d'akin da akayi.

"Auchhhh!!"
Ta saki wani irin k'ara alokacin da taji zafin alluran na ratsa ta, da kuma bak'on k'amshin turaren daya hade da numfashinta.
Wanda hakan yasa ta bud'e idanunta inda ta  sauk'esu akanshi.

*Not editing*

10:55 pm

(Im sorry wannan book din Ba free bane but nake baku, Saidai kusani idan babu yawan vote daga wannan page din wallahi bazan sake update anan ba.)


You are reading the story above: TeenFic.Net