Tweenty

Background color
Font
Font size
Line height

*MAJNOON*

*20*

Kansa yake jujjuyawa da iyaka k'arfin sa, cikin kuma matsanancin ciwo gami da azababben rad'ad'in da yakeji acikin jikinsa, Wanda har saida hakan ya sanya fuskarsa yin ja, yayinda jijiyoyin jikinsa suka bayyana rud'u rud'u.

Gurnani had'i da k'ara yake sakewa saboda tsananin azabar da yakeji, na ratsa kowanni mahudar gashi na jikinsa, Wanda suka mimmik'e saboda suka da yakejin fatar jikin nasa keyi.

Kamar yanda yake ganin d'akin na juya masa, haka ma kwakwalwarsa ke juyawa, Wanda hakan yasa jikinsa ke jijjiga tamkar mayunwacin zakin dake tsaka da farauta.

Wanda ganin hakan yasa Soumaya amatuk'ar tsorace ta soma girgiza kanta, had'e da jan jikinta baya tana mejin kirji da zuciyarta na wani irin duka.

Saboda yanda sautin gurnaninsa ke tashi yana me amsa amo acikin kunnuwanta.

har yanzu ta kasa d'auke idanunta daga kansa, duk da yanda gurnanin numfashinsa ke shirin toshe dodon kunnenta.
Idanunta da suka cika da kwalla ta rumtse da k'arfi, hade da sake kankame jikinta waje d'aya.
Domin Bazata tab'a iya jure kallonsa ahaka ba, bazata iya sauraran k'aran da yakeyi, Wanda ke kokarin haukata nutsuwar taba.

Saurin taro numfashinta dake shirin k'wacewa tayi, alokacin da k'aran fashewar wani abu ya ratsa kunnenta, Wanda hakan yasa azabure ta Ware idanunta, inda ta sauk'esu ak'asan d'akin, Wanda gilasan Bedside lamp ke tarwatse pieces, saboda wani irin wurgi da Majeed din yayi dashi.

Atsorace ta kuma d'agowa ta kalli Majeed d'in, Wanda yake kokarin sauk'a daga kan gadon yana me rik'e da kansa.
Akid'ime kuma ya soma buga hannayensa da jikin bango, tare da k'arasawa gaban drawern dake d'akin ya shiga dukansa da duka k'arfinsa.
Yana sakin numfashin da duk maiji yasan da k'yar yake iya fusgosa, musamman idan akayi duba da irin ihun da yakeyi.
Wanda yake nuna tsananin fitar hayyaci da kuma zaucewarsa.

K'ok'arin janye jikinsa yasoma yi ta hanyar rik'e kansa dake juyawa,
Saidai kasancewar duk jikin nasa rawa yake tamkar wanda aka jonawa shocking, hakan yasa kafafunsa kasa d'aukarsa, atake kuwa yatafi luuu ya fad'i a k'asa.

Kuka Soumaya ta sanya mai tab'a zuciya, ganin yanda ya bugu ak'asane kuma yasa ta
, tasowa da sauri cikin matsanancin tausayinsa da takeji ta nufo Kansa, batare da ta damu dacewar ko zai iya cutar da ita ba.

"Ammmooorr!!"
Ta kira sunansa cikin muryar kuka, had'i da tsananin tashin hankalin da take ciki.

Daidai ta k'araso wajen nasa ne kuma, yasanya duka hannayensa biyu ya tureta.

Wanda hakan yasa ta tafi da baya baya ta bugu ajikin gado.
"Auchhhhhhhhh."
Ta saki wani irin k'aran azaba, tare da sanya hannu ta rik'e bayanta wanda ya bugu da k'arfi, kana cikin rashin sanin abunyi ta saki sabon kuka mai sauti.
Kukan dake narkar da zuciyar maiyinsa, domin duk da tanajin rad'ad'in buguwan da tayi, amma nasa rad'ad'in da takeji acikin zuciyarta yafi mata komai ciwo.

Majeed dake neman zaucewa kuwa, sautin kukan nata dake ratsa cikin kunnuwansa ne, yasa shi sake rik'e kansa dake juyawa.
Domin atsakar kansa yakejin kukan nata, yayinda muryarta kuwa ke neman fasa dodon kunnensa.

Wanda har takaisa ga kasa iya jurewa, domin Akaron farko na rayuwarsa, kenan da ya fara jin tamkar ana d'iga masa ruwan dalma akan zuciyarsa, dake bugawa da k'arfi.
Hakan yasa shi mik'ewa tare da soma yawo atsakiyar d'akin, yana me kama kansa da yakejin kamar zai bar ganganjikinsa.

Tabbas duk da bawannan ne akaro na farko arayuwarsa ba, daya farajin rad'ad'i da ciwo amma abun da yakeji acikin jikinsa yau, ya wuce misaltawa.
Shi baisan wanene shiba, kamar yanda ayanzu baisan gabas da yamma ba, ba kuma zai iya tantance duniyar da yake cikinta ba.
Wannan dalilin yasa shi d'imaucewa da neman mab'oya daga abunda yakejin yana sukan naman jiki da kuma zuciyarsa.
Abunda yasa shi yake sakin k'ara tare da soma yawo atsakiyar d'akin cike da neman mab'oya, inda zai b'oye kai da jikinsa, ko hakan zaisa ya samu sauk'in lamarinsa.
Rasa inda zai saka kannasa ne kuma, yasa shi zubewa ak'asa tare da takure jikinsa waje d'aya.

Saidai sam ya kasa samun sukuni saboda karkarwan dako wanne naman jikinsa keyi.
Ga kuma gurnanin da yakeyi maiban tsoro.

Ganin hakan kuwa shiyasan yata tsayar da kukan nata, ta hanyar rage sauti saboda kirjinta da taji yana wani irin duka.
Domin aduk gaba d'aya rayuwarta bata tab'a ganin irin hakan ba.
Kallonsa take da idanunta wanda suka bayyana tsananin rauni, had'i da wani abu na daban dake yawo acikinsu, kallon dake cike da tsananin tausayawa.

Dan tayi imani idan har abunda takeji acikin jikinta, shine kwatan kwacin ciwon da yakeji, To Tabbas dole k'wak'walwarsa zata sake zautuwa.

Wanni irin K'addarace Wannan?
Shine tambayar da takeyiwa kanta akullum, akuma lokacin da bata da amsarta.

Yaushe Wannan zuciyar zata huta? Yaushe kirjin dake bugawa tamkar zai rabe gida biyu, zai samu salama da sanyi acikinsa?
Yaushe ne k'wak'walwar zata daina d'imaucewa?

Hak'ik'a Shine mutum na farko arayuwarta, da takejin duk wata damuwarsa acikin jini da tsokanta.

Kukan dake neman k'wace mata me k'arfin gaske ta soma k'ok'arin dannewa, ahankali kuma cikin rawar da jikinta keyi ta soma rarrafawa zuwa inda yake.

Kasancewar ya takure jikinsa waje d'aya, agigice ya soma bubbuga kansa da k'asa, ahaukace yake fusgar jikinsa da yatsunsa wanda suke d'auke da yalwatattun faratu.
Wanda hakan yasa atake jini ya soma d'iga daga hannun nasa.

Agigice Soumaya ta k'araso garesa, had'I da zube guiwowinta ak'asa.

"Ammmoorrr!!!!"
Takira sunansa da muryarta wacce ke rawa sbd kuka, had'i da tsoro na ganin halin da yake ciki.

Still jikinta na rawa, akuma karon farko na rayuwarta da ta d'ago, tafukan hannayenta ta d'aurasu akan nasa hannayen.
Tare da matse hannun nasa da yake fusgar fatar jikinsa dashi.

"A'a dan Allah! Dan Allah kabari.......!!"

Da matsanancin kuka ta fad'i hakan, bayan ta rik'e hannayen nasa k'am acikin nata.

Hannayen da tab'asu ya sanya tsikar jikinta motsawa, tare dajin wani irin yaaarr acikin jikinta.

Majeed d'in kuwa dake kwance yana me sake duk'unk'unewa waje d'aya, jin an tab'a hannayen nasa ne yasa shi tasowa agigice.
Tamkar wanda aka zaburar.
inda ya sauk'e idanunsa akan hannun da yayiwa nasan rumfa.

Kyawawan yatsun hannunta wanda baya iya tantance ko menene ya zubawa idanunsa, Wanda suke gane masa dishi dashi.
Saboda hawayen dake fita daga cikinsu.

Batare daya tsaya tunanin komai ba kuma, jin d'umin numfashin mutum akusa dashi.
Cikin rauni da kuma yanayin gigitan da yake ciki, ya matso kusa da ita ta hanyar rike hannun nata gam.
Ad'imauce kuma ya fad'a cikin jikinta, yana sakin wani irin kuka.
Mafaka yake nema, mafakar da zata sanya shi samun nutsuwa.
Duk da tun asali baisan meyakeyi ba, amma ayau akuma yanzu yana buk'atar dawowa cikin hayyacinsa.

Wannan dalilin yasa shi mannewa acikin jikinta, ta hanyar cusa kansa akan cikinta, yana wani irin kuka mai tab'a zuciya.

"Heeeeeeeeeeee."
Soumaya da numfashinta yayi d'aukewar wucin gadi, ta jawosa da k'yar, saboda wani irin shocking da taji acikin jikinta na had'uwar jikinta da nasa.

Lokaci d'aya ta saki kukan da takejin aduniya bata tab'ayin wani irinsa ba.
Koda ranar da Abboun ta ya fad'i kuwa.

Hannayenta dake cikin nasa ta rik'e da k'arfi, kamar yanda ta rumtse Idanunta, dalilin jinsa da tayi ajikinta, yana me murza kansa ako Ina nata, da niyan neman mafaka.

Tausayin sane ke neman fasa zuciyarta, Wanda hakan yasa ta soma rera kuka mai tab'a zuciya, kukan dake bayyana gazawarta afili.
Yayinda acikin jikinta kuwa takejin cewar ta gaza kulawa dashi.
Saboda sautin kukansa dake shirin wargaza duk wata nutsuwarta, aduniya bata tab'a ganin wani kamarsa yana kuka haka ba.
Saidai abunda ta kasa tantancewa kanta shine, kuka yake ko kuwa jinin jikinta yake zuk'ewa.

Domin ad'imauce take jin sauk'an sautin kukannasa acikin kunnuwanta.
Wanda hakan yasa duk wani nutsuwa da ya saurawa zuciyarta ya kau.

Wannan dalilin yasa ta zare hannunta daga cikin nasa, ta hanyar rungumesa acikin jikinta, batare da ta damu da zubawar da tsikar jikinta keyi ba.
Batare kuma da ta tsayar da kukan da takeyi dinba.

Majeed kuwa dake sake duk'unk'unewa acikin jikinta, matse ta k'am yayi had'i da soma sakin wani irin nishi yana me jinjigata da hannayensa.

Akaron farko na rayuwarsa sau d'aya tak da yaji cewar ya samu mafaka, mafakar da zata rage masa rad'ad'in duk wani abu da yakeji.
Wannan dalilin yasa shi sake matseta k'am tamkar zai b'allata, yayinda kansa da fuskarsa kuwa ya cusa su adaidai saman lafaffen cikinta.

Gaba d'aya jikinsa rawa yake kamar mazari, kamar kuwa yanda bai daina sakin gurnani ba, haka bai daina kuka ba, duk da cewar kasantuwarsa ajikin nata, yasa bugawar zuciyarsa lafawa.
Yayinda wani irin abu da bai tab'a jiba, ke tasowa tun daga k'asan k'afarsa zuwa kwanyarsa.
Hakan yasa shi sake shigewa jikinta, Tare dasa hannunsa ya rik'e waist dinta da k'arfi, k'asa k'asa kuma yake kartan skin d'inta da zara zaran faratansa.

Idanu ta rumtse alokacin da taji yana caka tsinin fartun nasa akan fatar ta, Wanda hakan yasa ahankali ta tsagaita kukan nata, tare da bud'e lumsassun idanunta, inda ta sauk'esu abayansa, kasancewar gabansa na cikin jikinta ya takure kamar k'aramin yaro.

Yanda jikin nasa ke b'ari shine abun dake bata tsoro, shine kuma abunda yasa ta karyar da wuyanta gefe.

Tare da d'aukan hannunta ta kife akan dogon gashin kansa.

Hakika wannan shine karo na farko arayuwarta da ta fara samun kusan ci da wani d'a namiji.
Saidai shi jinsa takeyi daban, bawai don bata saba ba, kawai shi dabanne.

Rayuwa na juyawa ne alokaci d'aya, sama izuwa k'asa, k'asa izuwa sama.
Wani abun ba k'irk'irarre bane tabbatacce ne.
Yanzu zakayi farinciki anjima ka fuskanci k'alubalen da zai gusar da farincikin ka.
Yanzu zakayi kuka amma anjima ka samu abunda zai saka dariya.
K'addara bawai samunka takeyi asama ba, haifarka akeyi dashi.
Haka kuma abu me sauk'ine abunda baka tab'a tunani ya faru dakai.
Ayau tayi imani da Wannan.
MAJEED jini ne dake gudana ajikinta.
Sam ba k'addarar ciwon Abbou bane ya had'ata dashi.
Dama shi d'in ajinin jikinta yake yawo.
Shine tambarinta wanda har abada bazai gogu daga gareta ba.

Hawayen dake cike a idanunta ne suka silalo, Wanda hakan yasa ta jingina jikinta da bango, ahankali kuma ta tura hannunta Acikin tarin sumar kansa.

Cikin yanayin da ita kanta bata gama tantance wanne bane, ahankali ta shiga yawo da hannunta acikin sumar kan nasa.
Tare da soma motsa bakinta ahankali take karanto masa addu'a, duk da cewar muryarta tayi sanyi sosai.

Addu'ar takeyi da Duka confidence d'inta, domin ta mik'awa Allah dukkanin lamuranta.

Shi kuwa Majeed da jikinsa ke tsananta rawa saboda addu'an da takeyi dinne, ya sashi sake matse kansa ajikin nata, tare da rumtse idanunsa da k'arfi, yana me sakin numfarfashi, kasancewar lokaci d'aya ya nemi kukan da yakeyi din ya rasa, wannan ne kuma yasa shi soma sassauta rikon da yayiwa Soumayan.

*After 1 hour.*

Idanunta da suka kwashe tsawon mintunoni a rumtse, ta ware ahankali hade dajan wani dogon numfashi.
Kana cikin wahala ta fusgo numfashin daya tsaya kirjinta, saboda tsananin rik'on da yayi mata, Wanda yasa ta kasa motsa komai nata.

Idanun nata ta sauk'e akanshi, tana me kallonsa da yanayin mamaki, kasancewar jikin nasa ya daina b'ari haka ma ya daina wannan gurnanin dake kara hautsuna mata lissafi.
gargasan jikinsa da har yanzu suke a tsaitsaye ta kalla, kana kuma da dawo da kallonta ga kansa, Wanda tun d'azun daya kifa kan nasa akan cikinta baisake d'agowa ba, Saidai d'umin numfashinsa da yake sakar mata akan cikin, Wanda ke tayar mata da tsikar jiki.

Agogon dake can saman d'akin ta kalla, ga mamakinta kuwa k'arfe 11:30 pm ta gani, sam batayi tunanin dare yayi har haka ba.
Idanun nata ta kuma lumshewa, dan duk da yanda takai gajin matsar da yayi mata, hakan baisa taji cewa ta gaji ba, bawai kuma dan bashi da nauyi ba.
Saidan batason duk wani abu dazaisa ya motsa ko yaji rad'ad'i da zafi acikin zuciyarsa.
Ta amincewa kasancewa dashi ahaka koda kuwa zasu kwana da wuni.

Wannan yasa ta d'an muskutawa tare da kwantar da kanta ajikin bedside drawer.
Batare da ta fasa abunda takeyi ba kuwa, ta ci gaba da yawo da hannunta acikin tarin sumar kansa, Wanda take mamakin yawa da laushinsa, Sak irin gashin larabawa yake dashi me santsi da laushi.!

Daga wani b'angare na zuciyarta kuwa tunani ne fal.
Yayinda acikin ranta take raya wasu abubuwa daban.
Kasancewar yau ne rana ta farko da zata fara kwana da wani namiji arayuwarta, kamar yanda yaune rana ta farko da ta fara samun kusan ci.
Kusancin daya kawo sauyawan tunani agareta, kana ya narkar da jinin jikinta.

Hakika bazatace yaushe ne ko tsawon wani lokaci suka d'auka ahakan ba, duk da tasan sun kwashe sama da 2hours a haka, ammma lokacin da bacci b'arawo ya d'auke ta bazata iya tunawa ba.

4:00 am.

Ahankali Billionaire Dawoud ya turo k'ofar d'akin, wanda ya kasa bacci duk tsawon daren, kasan cewar zuciyarsa ta kasa samun salama, na sanin halin da Majeed din zai fuskanta a daren yau.

Gaba d'aya fargaba ne acikin zuciyarsa, na rashin sanin abunda zai tarar, wannan dalilin yasa koda ya turo k'ofar, ad'ad'are ya sako kansa cikin d'akin, cike da tunanin yanda zai iske Majeed din.

Saidai yana sako kannasa kuwa idanunsa suka sauk'a akansu.
Wanda hakan yasa shi d'an zaro idanunsa, cike da mamakin abunda suka gane masa.

"MAJEED da SOUMAYA!"

Ya fad'a da mamaki yana me sake zuba musu idanunsa.
Zuciyarsa cike da karaya, had'i da raunin da yasa yaji hawaye na cika idanun nasa.
Tsawon mintuna haka ya d'auka yana kallonsu cike da tausayawa.
Musamman Soumaya wacce take azaune ta tankwashe k'afafunta, yayinda Majeed din ke manne da jikinta, ya d'aura kansa akan cinyarta.

K'warai wannan shine karo na farko acikin rayuwar Majeed, da ya samu bacci bayan anyi masa Wannan alluran da akeyi masa duk sati.

Alluran da shikansa yake tsoron ranar zagayowarta, amma kuma ga mamaki sai gashi yau ya samu bacci.

Tabbas Billionaire Dawoud din yaji dadin hakan.
Saboda alamace dake nuna haske ya bayyana acikin rayuwar Maleek din.

Ajiyar zuciya ya Kuma sauk'ewa, tare da juyawa cikin sand'a gudun kada ya tashesu ya fice daga cikin d'akin.

Washegari.
*7:00 am*
Asanyaye take motsa Idanunta da takejin sunyi mata nauyi, had'i kuma da d'an motsa jikinta, bayan ta ware idanunta gami da sauk'esu akansa.

K'akk'arfan numfashi taja, kana cikin sanyi ta zare hannunta dake cikin gashinsa.
Alokacin da takai dubanta ga window'n d'akin wanda hasken sararin samaniya ya haska sa.
Idanu ta d'an zaro cike da mamakin bacci mai nauyin da tayi, a irin wannan yanayin da har yakai ga bata farka ba sai yanzu.
Sauk'akk'iyar ajiyar zuciya tayi, tare da sake lafe cikinta, saboda numfashinsa dake ratsa cikin fatar ta.
Bayan ta zuba masa idanu tana kallonsa, duk da cewar tun kwanciyar da yayi ajikin nata jiya bai motsa ba har yanzu.

Hannu tasa ahankali ta tallafo kansa, had'i da zare jikinta ahankali gudun kada ta tashe sa.
Wani d'an pillow da lallausan blanket dake kan gadon nasa ta jawo, tare da d'aura kansa akan pillow din, blanket din kuwa yafa masa tayi akan jikinsa.
Tare da mik'ewa tsaye cikin sand'a ta fice daga cikin d'akin, tana me sauke ajiyar zuciya.

Kaitsaye d'akinta ta nufa inda tana shiga, ta soma k'ok'arin rage kayan jikinta.
Bayan ta cire kayan nata ne kuma direct ta wuce toilet, inda ta had'awa kanta ruwan wanka acikin bathtub.

Agurguje tayi wankan saboda sanin da tayi cewa, idan ta b'ata lokaci zata iya makara wajen zuwa makaranta.

Tana fitowa awankan kuwa wata doguwar riga ta zura, tare da sanya hijab ta tada sallah.
Bayan ta idar azkhar kawai tayi ta mik'e tare da k'arasawa gaban mirror ta shafawa jikinta mai.

Ledan da Billionaire Dawoud ya bata jiyan ta d'auko, tare da bud'ewa ta zaro d'aya daga cikin uniform din.
Wanda yake riga da wando sai kuma madaidaicin hijab da iyakansa guiwan hannunta.

Zura kayan tayi wanda yayi mata cib cib ajikinta, kana ya kuma bayyana shape din lafaffen cikinta.
Dogon gashinta ta d'aure bayan ta zura hijab din makarantar, ta d'auki sabuwar school bag din, da Billionaire Dawoud din ya kawo mata na company'n Lovis Vuitton, jaka ce me matuk'ar kyau wanda hakan yasa ta rataya jakan akafad'anta na dama, had'I da sanya takalmanta sau ciki wanda suma suka kasance kalan jakan.

Agogon bangon dake sak'ale acikin d'akin ta kalla, 7:15 am Shine abunda idanunta suka gane mata, Wanda hakan yasa da sauri ta murd'a handle d'in k'ofar ta fice.

Fitowarta cikin falon kuwa yayi daidai da soma knocking k'ofar falon da akayi.

Ahanzarce ta k'arasa ta bud'e k'ofar kamar yanda zuciyarta ta bata kuwa masu kawo abinci ne.
Saidai wanda ya kawo abincin yau, ba shine ya kawo jiya ba.
Hakan yasa ta karb'an trayn tare da juyawa ta koma cikin falon.

Akan center table ta ajiye abincin, saboda bata tunanin zata iyacin wani abu daga ciki.

Anutse ta juya da niyan fita daga falon, saidai bai wuce taku uku tayi ba, ta tsaya cak gami da juyowa ta kalli k'ofar d'akin nasa.

"Tayaya za'ayi yaci abincin shi kad'ai? Nasan bazaici ba, nasani."

Ta fad'a murya araunane, lokaci daya kuma taji hawaye na kokarin taruwa acikin idanunta.
Wanda hakan yasa ta juyawa cikin sauri ta fice daga falon.

Da nutsuwa take sauk'owa daga kan steps din har ta k'araso zuwa cikin babban falon k'asan dake d'auke da y'an tsirarun ma'aikatan da suke ta gyare gyare.

Sam bata damu da tsayawa ta k'arewa cikin falon kallo ba kaitsaye ta nufi waje.
Wanda tun zuwanta gidan yau shine karo na farko da ta fara taka k'afanta zuwa wajen.

Wannan dalilin yasa koda ta fito, idanu ta bud'e tane k'arewa compound d'in gidan kallo, Wanda yake da matuk'ar kyau, musamman da aka k'awatasa da pink d'in flowers masu kyau, had'i da korayen shuke shuke.

Tabbas zata iya cewa bata tab'a ganin gida mai kyau da girman Wannan ba, kasancewar atsakiyar gidan ma wani tamfatsetsen swimming pool ne mai d'aukar hankali.

"Good morning."

Wata murya ta fito daga bayanta wanda hakan yasa ta juyawa da sauri.
Inda ta sauke idanunta akan wani matashin saurayi, dake tsaye jikinsa sanye da uniform masu kalan blue.

Batare da saurayin ya jira ta amsa ba kuwa, cikin yanayin yanda suka saba girmama mutanen gidan murya kasa kasa yace.
"Sunana Nura kuma nine Wanda zaina kaiki makaranta, dama duk inda kikeso kije."

"Nura."
Ta maimaita sunan akan harshenta, alokacin da take d'auke idanunta akansa, cikin yanayin dake nuna rashin sabonta da hakan, murya atausashe tace.
"Nagode muje kada na makara."

Hakan kuwa akayi Nuran ya wuce gaba, yayinda ita kuwa ta bisa abaya.

Kaitsaye wajen wata mota mai azabar kyau taga sun nufa, wato zafaffiyar mota k'iran Benz G63.

Da tsananin mamaki take kallon kyaun motar, Wanda wai yau acikinta ne za'a kaita makaranta, abunda bai tab'a faruwa da ita ba a iya tsawon rayuwarta, kasan cewar kullum taxi take hawa zuwa da dawowa.

"Bismillah."
Nura'n ya fad'a bayan ya bud'e mata gidan baya, yayinda shi kuma cikin sauri ya k'arasa ya zauna ab'angaren driver.

Tabbas itakam ta mutu da mamaki, Wanda hakan yasa asanyaye ta shiga cikin motar, Saidai kasancewar motar kiranta na Jeep ne yasa tana shiga taji tayi sama. hakan yasa ad'ad'are ta zauna tare da rufo k'ofar.

Nura kuwa Ganin hakanne yasa shi yiwa motar key had'i dayin reverse, kasancewar already maigadi ya wangale babban gate d'inne, yasa kaitsaye suka fice daga cikin gidan.

Tafiya

You are reading the story above: TeenFic.Net