Seventeen

Background color
Font
Font size
Line height

*Fatymasardauna*

                   *MAJNOON!!*
            *(The innocentmad)*

*PAIDBOOK*
*(Amount 300, Account Number 0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz Bank, Whatsapp Number 07069917168)*

              *Chapter 17*

Wani irin abu taji na yawo acikin sassan jikinta, saboda rikitattun idanunsa daya watsa mata, Wanda hakan yasa ta saurin jan jikinta baya.
Saidai abu na farko da ya rusketa shine kasa janye idanunta da tayi akan nasa, duk da yanda takejin zuciyarta na bugawa da tsananin k'arfi kuwa.

Yayinda daga k'ark'ashin tafin k'afarta kuwa, wani irin fitinannen sanyi takeji, Wanda ke ratsa kowani mahudan gashi na jikinta. 

Tabbas wani irin abu na musamman take hangowa daga cikin idanun nasa,  wani abunda kwakwalwa da tunaninta suka kasa farrashi.
Kasancewar sa abu wanda yayiwa idanunta girma.

"Wannan wanni irin mutum neshi?"

Tayiwa kanta tambayar dake neman rud'a tunaninta, ta hanyar tsurawa hannayensa idanu, Wanda duk kowanne gashi dake jikinsu ya mimmik'e, yayinda korayen jijiyoyin jikinsa kuwa  suka bayyana rad'au.

Abu yakeyi tamkar mai tsoron mutane, yanayinsa Tabbas irin na way'anda suka zauce ne, amma meyasa yake jan jikinsa baya da yanayin tsoro?
Tsoron mutane yakeyi?

Abubuwan da k'wakwalwa da zuciyarta ke tambayanta kenan, Wanda kuma bata da amsarsu.

Shi kuwa Majeed jin ya iso jikin bango ne ya sashi rumtse idanunsa k'am, tare da matse jikinsa dake karkarwa waje d'aya.
Kansa dake yi masa barazanar tarwatsewa yake jujjuyawa, agigice saboda yanda yakejin wasu abubuwa nayi masa yawo acikin kan, suna sukan kowanni tsagi na brain d'insa.
Daga gefe guda kuwa, amon sautin dake tab'o dodon kunnuwan nasa ne ke tashi.

Duk ilahirin jikinsa rawa yake, Kamar yanda harshe da labb'an bakinsa suke rawa, saboda wani irin suka da yakeji acikin jikinsa.
Sukar da idan za'a kwatanta da rabin wacce yakeji acikin zuciyarsa, to abun bazai tab'a had'uwa ba.

Wannan dalilin yasa shi birkito da yalwataccen gashin kansa,  tare dasa hak'waransa ya soma cizon lips d'in nasa.
Atake kuma ya soma sakin wani irin gurnanin numfashi.

Wanda hakan yasa Soumaya
zuba masa idanunta da suka ci ko da hawaye,  yayinda akaron farko da ta fara son nazarto abunda yakeji.

Duk da gurnanin numfashin nasa, ya sanya tsikar jikinta zubawa, amma acikin zuciyarta ji takeyi akwai abunda yake nema, haka kuma akwai abunda yake so.

Wannan dalilin yasa ta soma d'an tahowa izuwa gareshi, duk da kusantarsa na k'ara mata yawan fad'uwar gaba.
Amma abunda takeji acikin jikinta ya zarcewa k'arfin fad'uwar gaban.

Taku d'aya tak kawai ya rage atsakaninsu, ta sulale ahankali tare da zubewa akan guiwowinta.

Kana ahankali kuma ta lumshe idanunta, saboda sautin numfashinsa dake tafiya da bugun zuciyarta.

"Ammmoooor!!"
Ta sake k'iran sunansa akaro na biyu,  da Kuma muryarta wacce take cracking.
Saboda raunin da tayi.
Batare kuma da ta jira amsar saba, saboda sanin cewar bazai amsa ba, yasa ta bud'e idanunta ahankali, tare dasa hannunta ta d'auki d'aya daga cikin plate din abincin da aka kawo.

Juyo da kallonta garesa tayi, da narkakkun idanunta wanda suka cika da k'walla, tace.

"Please kaci abinci."
Asanyaye tayi maganan wanda hakan yasa, hawayen dake cikin idanun nata gangarowa kan fuskarta.

Amma sam bata damu da hakan ba, saima sake tura masa plate din abincin da tayi.
Tare da tank'washe k'afafunta, da yanayi na d'an tsoro ta lek'a kyakkyawar fuskarsa wacce ya kawar da ita gefe.

Jajayen lips dinsa wanda suke jajur kamar zasu d'igo da jini ta zubawa ido, saboda yanda taga yake taunesu tamkar ba ajikinsa suke ba. 

Saurin kawar da kanta gefe tayi, saboda yanda taji tsikar jikinta na mimmikewa, Dan yanda yake taune lips din nasa babu alaman cewar akwai sauki alamarinsa, kamar yanda tasan cewar yanajin matukar zafi, amma kasancewar baya cikin hayyacinsa yasa sam bai damu da hakan ba.

Idanunta ta d'an rumtse da k'arfi, domin sab'anin shi ita ce ke jiye masa zafin taunan lips d'in nasa da yakeyi.

Wanda hakan yasa ahankali, kuma cikin yanayi mai kama da d'ari d'ari ta d'aura hannunta, akan nasa.

Akaro na farko na rayuwarta da hannunta ya fara, had'uwa da na wani namijin.
Wanda hakan yasa ta jin wani irin shock, mai k'arfi daya sanya ta zabura ta janye jikin ta baya.

Tare kuma  da saurin waigawa saboda, k'aran takun takalmin    Da taji yana dunfarowa cikin library din.

Idanu ta zubawa k'ofar shigowan, tamkar wata wacce bata da gaskiya kuma haka jikinta ke rawa.

D'aya daga cikin matasan masu aikin gidanne ya shigo, hannunsa d'auke da cup na freshmilk.
Ganin ta da yayi d'inne kuma yasa shi, d'an sunkuyar dakai cikin k'ank'an da murya yace.

"Goodmorning Maaa, ance na fad'a miki cewar kina  da bak'o afalon k'asa."

Ya k'are maganan yana me ajiye cup d'in dake hannunsa, akusa da Majeed wanda akullum babu wani abu da yake sha sai fresh milk d'in, nanma bawai wani sosai ba.

Soumaya kuwa idanu ta zubawa saurayin, Wanda yafi mata kama da Christian saboda yanayin askin dake kansa, da kuma tsarin fuskarsa wacce babu alaman hasken sallah akan goshinsa.

"Bak'o."
Ta maimaita kalmar acikin ranta, yayinda zuciyarta ke cike da fargaba had'i da tantamar wanda yazo wajen nata?

"Waye zaizo?"
Shine abunda ta tambayi kanta, tambayar da dole sai ta je taga waye sannan zata bawa kanta amsa.

Hakan yasa ahankali ta tashi daga durk'uson da takeyi.
Tare da d'an juyawa ta kalli Majeed d'in.

Daya kasa motsawa daga inda yake sai faman vibrating da jikinsa keyi.

Houseboy d'in dake tsaye mai Number 8 ajikin rigarsa ta kuma kallo, kana cikin sanyi ta juya ta fita daga library'n.

Ajiyar zuciya house boy din me suna, john ya sauk'e tare da d'an binta da kallo, acikin zuciyarsa yana mejin dad'in tafiyar nata, saboda yasan idan ba haka ba, aikin da aka basa bazai tab'a kammaluwa ba.

Sa'arsa d'aya kuma shine babu CCTV acikin libraryn, hakan yasa zaiyi abunda yakeso cikin nutsuwa.

Soumaya kuwa ahankali take tafiya, tamkar wacce k'wai ya fashewa haka take taka lallausan carpet din dake cikin falon.
Wanda sai ayanzune ma zatace ta samu daman kallonsa, har ta san wasu color'n furnitures ne aciki.

Ahankali ta soma sauk'a daga kan steps din, wanda yake kamar glass saidai saboda quality dinsa, yasa mutum komai girmansa idan ya taka bazai fashe ba.

Saidai rashin sanin hakan yasa take ta kasa ahankali, saboda tunda take arayuwarta bata tab'a ganin irin steps d'inba.
Dama kuma gidan wanda ayanzu take k'are masa kallo gaba d'aya.

Wani irin duniyace guda mai zaman kanta, saboda kud'in da aka narka akan gidan kuwa, wallpaper'n dake mamaye da duka bangon falukan gidanma  kadai abun kallone.

Wanda hakan yasa Malam Musbahu dake tsaye ya juya bayansa wa steps din fitowa falon, yake bin komai da idanunsa dalla dalla, zuciyarsa cike da mamakin irin kud'in da Billionaire Dawoud ya kashewa gidan.

A iya furnitures din gidanma kad'ai millions of naira ne, balle kuma sauran abubuwan k'awa da akasawa gidan.

More especially wannan falon da suke ciki yanzu, Wanda yake wadace da girma, yayinda asaman sa aka lik'a cctv cameras guda biyu.

Lallai yau ya yarda da yawan arzikin Billionaire Dawoud din da ake fad'a, da kuma wanda ake bugawa ajarida, domin ada yana ganin kamar babu mai irin wannan tarin dukiyan.

Jiyo k'aran takun mutum abayansa da yayine Kuma yasa shi, juyowa cikin hanzari wanda hakan yasa shi sauk'e idanu akan Soumayan.

"Baffa!!"
Soumaya ta k'ira sunansa fuska d'auke da mamaki, farinciki, had'i kuma da rauni wanda ke tafiya da yanayinta nako da yaushe.

Murmushin dake kan fuskarsa ce ta d'an fad'ad'a, Wanda hakan yasa farincikin ganinta bayyana akan fuskarsa, cikin kulawa yace.

"Na'am Soumaya."

Ajiyar zuciya ta d'an sauk'e, tare da K'arasa sauk'owa Daga kan step din, zuciyarta d'auke da k'warin guiwan da ta gani akan fuskar Baffan.

"Baffa am dama zaka zo?."

Ta fad'a tana me k'arasowa inda yake, tsaye wanda ganinta yanzu ya sashi zama akan, d'aya daga cikin original  royal cushions d'in da suke kewaye da falon.

"Zanzo mana Soumaya dole zanzo kinsani, saidai da fari nayi tunanin ko b'atan kai nayi dana ganni awannan gidan."

Yayi maganan yana me sake k'arewa ko Ina kallo, danshi sai yake ganin kamar ba a Nigeria yake ba.
Kasancewar karonsa na farko daya fara shiga gida mai tsananin kyau irin haka kenan.

Idanunta ta d'an lumshe had'i da sunkuyar da kanta k'asa, saboda yanda taga Baffan nata k'arewa falon kallo.

"Baffa Ina kwana." Ta fad'a cikin sanyin murya, tare da zamewa cikin nutsuwa ta durk'usa akan guiwowinta, Wanda suka lume cikin lallausan carpet din dake falon.

"Lafiya k'alau Soumaya, fatan kin tashi lafiya."

"Lafiya"
Ta fad'a tana me murza yatsun hannunta, hade da d'an d'agowa ta kalli Baffan.

Wanda hakan yasa Baffan shima kallonta, sanin abunda ke zuciyarta ne kuma yasa shi sauk'e ajiyar zuciya, tare da gyara zamansa, cikin kulawa yace.

"Ya jikin mijin naki?."

Dummmmm
Haka taji ak'irjinta saboda yanda taji kalmar MIJI'n yayi mata nauyi, tare dasa mata fad'uwar gaba.

Busashshen yawun daya tsaya mata amak'oshi ta had'iya.
Cikin kuma muryarta da ta sark'afe lokaci guda tace.

"Da.... da  sauk'i... Abbouna  fa?, Baffa dashi na kwana acikin zuciyata, saboda arayuwana jiya ce rana d'aya tak da na tab'a wayan gari har na kwana batare da nasashi a idanu na ba, hakan yasa nake ganin komai bak'o."

Numfashi Baffan ya d'an fesar  tare kuma da sunkuyar da kansa, cikin son tausasa mata zuciya yace.

"Jikin Abbounki Alhmdlh, domin  dama maganan jikin yana d'aya daga cikin abunda ya kawoni, saboda angama komai anjima k'arfe 11 jirginmu zai tashi zuwa k'asar ta masu jajayen kunnuwa wato (Germany)."

Saurin d'ago da kai tayi ta kalli Baffan, saboda yanda taji kirjinta ya buga daya ambaci tafiyar Abboun nata.

Saboda hakanan taji tamkar Abboun idan ya tafi bazai dawo ba, wannan dalilin yasa hawaye taruwa acikin idanunta. 

Cikin kuma kasa b'oye tsananin damuwar dake ranta, murya na rawa tace.

"Tsoro nakeji har yanzu Baffa, tsoron kada wani abu ya samu Abbou na, duk da inajin ajikina cewar zai samu lafiya, amma banason yayi nesa dani, zanyi kewarsa sosai, zanyi kewar Abbouna.
Dan Allah Baffa ka k'ara bani tabbacin cewar zai warke zai tashi yayi rayuwa kamar da."

"Insha Allah Soumaya cuta da lapia duk ta Allah Ne, ina kuma da yak'inin cewa zai yaye masa, ni kaina Ina fatan samun lafiyarsa, amma Allah kad'aine yasan abunda zai faru anan gaba, yak'inin mu kawai muke akullum, tabbataccen abu kuwa sai Allah."

Baffan ya fad'a cikin sanyin da jikinsa yayi, domin shi kansa yana tsoron kada aje Germany din kuma wani sabon abu yazo ya b'ullo.     

Ahanki hawayen dake cikin idanunta suka gangaro,  Wanda hakan yasa ta d'an langwab'ar dakai.
Araunace tace
"Inason naganshi Baffa, Dan Allah muje na gansa kafun ku tafi."

"A'a Soumaya ke yanzu matar Aure ce, dole idan zaki fita saida izinin mijinki, idan kuma zaki tambayosa ya barki ki fita shikenan, saidai kisani shima yana da buk'atar kulawarki ayanzu, Soumaya Majeed bawai zamanki akusa dashi kawai yakeso ba, yana bukatar kulawarki tabbas, domin duk da kasancewarsa MAJNOON, dole akwai abunda yakeso."

Baffan ya fad'i haka cikin sanyin da jikinsa yayi. 

Wanda hakan yasa Zuciyar Soumaya'n sake karyewa, atake kuma hawaye suka soma gudu akan fuskarta.

Tayaya ne zata iya neman izinin mutumin da ba magana yake ba? Tayaya zata nemi izini daga mutumin da baya sanin inda yake, baya hayyacinsa, baisan komai ba sai gigita da kuma gushewar tunani.

Wannan abune da bazai yiwuba ta sani, hakan yasa ta sanya hannu ta share kwallan dake idanunta.

Baffa kuwa still cikin son kwantar mata da hankali yace.

"Karki damu Soumaya Insha Allah zanyi k'ok'arina wajen ganin na kula dashi, da yardar Allah kuma zai samu lafiya,
kamar yanda Dr. Mouhammad ya fad'a shi yayi mana komai, ya bada gudummawa sosai akan hakan, saidai bansan iya tsawon lokutan da zamu d'auka acan ba, duk da Dr. Mouhammad din yace bazamu wuce wata 3 ba."

D'an tsagaitawa yayi ta hanyar sanya hannunsa acikin aljihun rigarsa,  sabuwar waya k'iran Samsung ya ciro.

"Ki rik'e wannan idan mun isa can ta ciki zanna k'iranki, saidai karki manta muna da buk'atar addu'arki Soumaya."

Bafffan ya fad'a yana me mik'o mata sabuwar wayar, tare da wani atm card.

Asanyaye ta karb'i wayan, had'i da ATM card d'in Wanda ta soma juyasa, saboda ATM card din Abbounta ne.

"Duka sauran kud'inki suna ciki, kinsan password da komai, idan kina da buk'atar wani abu zaki iya amfani dashi, Dan Allah Soumaya ki kula, Insha Allah zanna k'iranki Ina sanar dake abunda ke wakana, ni zan tafi kada na makara saboda yanzu ma 10 tayi."

Ya fad'a yana me mik'ewa tsaye, saboda duk da bai tab'a shiga jirgiba, amma yasan cewa jirgi baya jira. 

Ganin ya mik'e d'inne kuma yasa Soumaya itama mik'ewa, saidai gaba d'aya ta kasa cewa komai, Dan wani irin fitinannen kuka takeji na taso mata.

Fahimtar hakanne kuma yasa Baffan yi mata sallama, tare da juyawa ya soma tafiya.

"Baffa."
Muryar Soumayan dake rawan kuka ta tsayar dashi daga tafiyan da yakeyi, kasancewar har yaje bakin k'ofar fita daga falon.

"Ka kulamin da Abbou please Baffa, idan ya tashi ka fad'a masa maganan aurena ta yanda zai fahimta, zanyi kewarku dukanku....."

Kukan da take dannewa ne yaci k'arfinta, Wanda hakan yasa ta juyawa asanyaye ta nufi saman.

Baffa ko jikinsa duk amace haka ya juya ya fice daga cikin falon, zuciyarsa d'auke da damuwa kala kala.

Yana fitowa compound din gidan kuwa, drivern da Billionaire Dawoud Saraki, ya bawa izinin zuwa ya kaisu airport ne, ya tari Baffan tare da nuna masa motan da zai shiga,  take suka wuce Hospital, inda daga nanne zasu wuce Airport din.

Soumaya kuwa jikinta duk asanyaye haka ta k'arasa hawa saman, saboda kukan dake cin zuciyarta kuwa har wani juwa takeji.

Ahankali ta maida k'ofar falon ta rufe, kana cikin sanyi ta jingina bayanta da jikin k'ofar had'i da lumshe idanunta.

Wanda cikinsu ke hasko mata fuskar mahaifin nata.

"I'll miss you Abbou."
Ta fad'a adaidai lokacin da takejin soyayyar mahaifin nata na ratsa kowani sashi na jikinta.

Sanin cewar kuka ba mafita bane yasa ta bud'e idanunta, tare da kallon hanyar Libraryn saboda, maganganun Baffa dake yawo acikin k'wak'walwarta.  

Tabbas abunda yake so shi takeji acikin bugun zuciyarta, Wanda bashi da iyaka.

Wannan dalilin yasa ta nufan libraryn kaitsaye Dan ganin ko yaci abincin.

Hannu tasa ahankali da niyan yaye cutting din libraryn, saidai kuma abunda ta gani shiya tilasta mata tsayawa cak.
Tare da sake waro idanunta Dan tabbatar da abunda take gani.

"Jini."
Ta fad'a ta hanyar motsa labb'an  bakinta, tare da d'an rank'wafowa ta zubawa d'igo d'igon jinin dake kan tiles din idanu, zuciyarta cike da fargaban abunda ya kawo jini wajen.

Wanda hakan yasa ta kutsa kanta cikin library'n.
D'aras kuwa  idanunta suka  sauk'a, akan tray da kuma plates d'in abincin da kukun ya kawo, anwargaza komai yayinda duk abincin dake cikin plates din akayi watsi dasu ak'asan d'akin.

Idanu ta kuma zarowa ganin yanda  duk jini ya b'ata wajen, ga kuma glass cup na fresh milk din dake tarwatse awajen, duk fresh milk din ya malale ak'asan d'akin.

Da sauri ta d'ago da kanta tare da kallon inda ta tafi tabarsa, saidai wayam ta gani babushi babu alamarsa.

Wanda hakan yasa ta jin fad'uwar gaba, tare da k'arasa shigowa cikin libraryn, saidai ko alamarsa bata gani ba, sai d'igo d'igon jininsa da duk ya b'ata wajen.

"Innalillah!"
Shine abunda ta fad'a alokacin da take cigaba da lek'a, ko ina dake cikin libraryn har bayan drawers amma bata gansa ba.

Daidai taje gaban wani drawer ne kuma, hannunta ya buge wani d'an flower dake wajen, Wanda hakan yasa littatafan dake saman drawer'n, watsowa suka zubo kanta.

"Auchhh."
Ta fad'a tana me kallon wani littafi like diary daya fad'o k'asa bayan ya daki kanta.

Wanda hakan taji tsikar jikinta ya zuba saboda tozali da littafin da tayi.
Ahankali kuma ta soma bin y'an k'ananun papers d'in da suke watse ak'asa.

Wanda kowannensu ke d'auke da wani tambari.
Idanu ta zubawa wani paper da akansa aka rubuta.

*My SOUL*

Da golden paint, Wanda ya k'arawa rubutun kyau.
Idanu ta zubawa takardar saboda ganin wani rubutu da tayi agefensa.

Rubutun daya sanya idanunta ganin dishi dishi, saboda wani sabon abu da taji ya sauk'a agangar jikinta.

Adaidai lokacin ne kuma daga b'angaren su Baffa, suka shigo cikin babban  airport d'in, yayinda Dr. Mouhammad ke tare dasu, kasancewar akan gadon marassa lafiya aka turo Abboun, dake kwance har yanzu oxygen ne kawai ke aiki.

Koda suka shigowa airport din Dr. Mouhammad ne yayi musu duk wani abunda ya dace.
Kasancewar Baffa ba wasu abubuwa ya sani ba.

Kamar kuma yanda yake 10:00 am daidai jirginsu ya tashi izuwa k'asar GERMANY.

*10:56 pm*


You are reading the story above: TeenFic.Net