Nineteen

Background color
Font
Font size
Line height

*19*

*Note editing*

3:00 pm

Ahankali take motsa kyawawan idanunta, Wanda suka b'ata tsawon lokaci a lumshe.
Yayinda kuma asanyaye take k'ok'arin fusgo numfashinta, daya sark'e, saboda nauyin da taji kirjinta yayi.
Batasan meyasa ba kwata kwata baccin bayayi mata dad'i.
Musamman ayanzu da takejin zuciyarta na tsananta bugawa, saboda abunda idanunta ke gane mata, kasancewar tana cikin wani irin yanayi mai kama da mafarki. 

Komai ganinsa takeyi ba adaidai ba, duk da irin kukan da taga tanayi acikin mafarkin, dake k'ok'arin zautar da tunaninta, saidai idanuwan nata basu daina gane mata kyakkyawar fuskarsa ba.

Numfashi taja mai k'arfi tare da bud'e idanun nata, wanda ta sauk'esu akan zanen pop'n daya k'awa ta saman d'akin.

Sassanyar ajiyar zuciya ta sauke, alokacin da ta fahimci cewar kukan da taga tanayi amafarki ne, bawai azahiri ba. 

Wannan dalilin yasa ta yunk'urawa ta tashi zaune, tana  me k'arewa falon kallo, had'i da sauk'e idanunta akan babban agogon bangon dake falon.

"Innalillahi K'arfe uku?"
Ta fad'a da muryarta wacce tayi low sosai, kana cikin mamakin yawan awannin da ta b'ata tana baccin.
Baccin dako kad'an bataji dad'insa ba.
K'afafunta ta zuro k'asa daga kan kujeran, tare da tashi tsaye, tana me kallon saitin k'ofar d'akin da Majeed din ke ciki.
Wanda haka nan taji duk hankalinta ya tafi izuwa gareshi.

"Wata k'ila ya tashi daga baccin."
Ta fad'a tana me gyara siririn
mayafin dake kanta, tare da nufan dakinta kaitsaye kasancewar batayi sallan azahar ba, ga kuma la'asar da ta kawo kai.

Koda ta shiga  d'akin kuwa Direct toilet ta wuce ta d'auro alwala,  tare da zuwa ta tada sallah.
Bayan ta idar da sallanne kuma ta d'an jingina kanta da jikin gado had'i da lumshe idanunta.
Tana me sauraran bugun zuciyar da ta zama k'awa kuma abokiya agareta, bugun dake sanya ta jin wani iri akoda yaushe.

Ahaka tana zaune akan prayer mat din har aka kira sallan La'asar, Wanda Anutse ta tashi tayi.
Kamar yanda ta saba kuwa acikin y'an kwanakin nan akowanni sujjadarta  sai ta saka Abbounta aciki haka yau dinma.
Asujjadar ta na k'arshe saida ta sako Abboun nata, bayan ta kammala azkhar ne kuma ta mik'e tsaye.

Ahankali take tafiya tare da nufar hanyar dakin nasa, koda ta k'arasa jikin kofar hannu tasa ahankali ta murd'a handle din k'ofar tare da kutsa kanta ciki.
Da yanayin sand'a gudun kada idan bacci yake ta tashe sa.

Sanin ta barsa akan gado ne kuma yasa ta kallon gadon, saidai ga mamakinta wayam taga gadon babu shi babu alamarsa.
Wannan dalilin yasa ta k'arasowa cikin d'akin da sauri, tana me raba Idanunta da niyan ko zata ganshi.
D'aram ko idanunta suka sauk'a a kanshi, inda yake zaune akan sallaya ya tankwashe k'afafusna had'i da sunkuyar da kansa k'asa.

Cike da mamaki take kallonsa, domin ganinsa da tayi akan sallaya ya nuna mata cewa sallah yayi.
Wannan yasa Brain dinta watso mata wasu irin tunani, had'i da tambayoyi.

Saboda wannan shine karonta na farko da taga, mutum irinsa wanda ake fad'in MAJNOON yayi sallah, a iya saninta duk wanda aka kira da sunan MAJNOON to bashi da hankali ne.
Tayayane mahaukaci zaiyi sallah? Bayan baya cikin hayyacin dazai iya tantance fari da bak'i.

Wannan amsar takeson samu, duk da cewar ajikin zuciyarta sam ta kasa aminta da Kalmar MAJNOON, ba tayi imani da Wannan kalmar dake yawo akan sunansa ba, abu d'aya tayi believing cewa shi wani mutum ne na daban, mutumin da komai na rayuwarsa ya kasance daban dana kowa.

Wannan dalilin yasa ayanzun ta zuba masa idanunta, tare da soma yawo da idanun nata akansa.

Kyakkyawar fuskarsa dake aduk'e take kallo, kasancewar  ya tattare duk yawan gashin kan nasa ya maidashi bayansa,  wanda hakan yasa cikakkiyar fuskarsa bayyana, duk da bai d'ago kansa ba, amma tana iya kallon yalwataccen eyebrow dinsa, da kuma zara zaran eyelashes dinsa, Wanda suka kwanta lub ak'asan idanunsa, sai kuma dogon hancinsa daya taho har kusan bakinsa, dake d'auke da jajayen labb'a,    Tabbas shiba fari bane sosai, dan tayi imani cewa bai kaita hasken fata ba,  saidai kuma baya daga  cikin layin bak'i ko chocolate color,  saboda farinsa barin na turawa ko larabawa bane, ba kuma irin colorn y'an Ethiopia ne dashi ba,  shi colorn sa dabanne ma'ana special color mai d'aukar hankali, Wanda kaitsaye za'ace masa fari, amma idan akan nutsu farin nasa yayi mis da milk color, Wanda hakan yasa yake cika idanun duk wani mai kallonsa.

Yayinda agefen kyakkyawar fuskarsa kuwa saje ne kwance lub, Wanda ya d'an kewaye cut lips dinsa.

Numfashi ta d'anja tare dayin k'asa da idanunta, domin duk da ba face to face sukayi ba, amma kwarjininsa takeji.

Wannan dalilin yasa ta sauk'e idanunta akan jikinsa.

Inda yake sanye da full kaya riga da wanda, sab'anin tun jiya da yake ta zaune ahaka babu riga.
koda ta kula kuwa ba wandon d'azu bane ajikinsa, yanzun wani black trouser ya sanya, sai white t-shirt wacce take sol babu alaman wani datti ko kuma yagu ajikinta, sab'anin sauran kayansa da ta d'aga d'azu wanda suke duk a yayyage.

K'asa tayi da idanun nata daga kallonsa, saboda yanda taji zuciya da kirjinta sunyi mara wani irin nauyi.
Take kuma taji wasu hawaye na son cika idanunta.
Wannan wacce irin jarrabawa ce?
Wacce irin k'addara ce dake sauya rayuwar mutum.
K'addarar da ta sauya masa rayuwa.
Wacce tasa kowa yakeyi masa kallon Mahaukaci.

Kanta ta d'an soma girgizawa saboda sam ita bata yarda da hakan ba.
Akallon da tayi masa yanzu abubuwa da yawa ta gani.
Wanda tasan cewar koba ita ba, kowani daban idan yazo ayanda yake ayanzu bazaiyi masa kallon mahaukaci ba.

Wannan dalilin yasa cikin d'an confidence din data samu, kaitsaye ta soma ta kowa ahankali harta k'araso inda yake zaunen.

Saidai ga mamaki ko motsi bataga yayi ba balle ya d'ago kansa.
Yana zaune shiru ne kawai, yayinda ta gaza gane idanunsa abud'e suke ko kuwa alumshe.

"Ammorr."
Tak'ira sunansa tana me d'an rank'wafo da kanta, zuwa kusa dashi,  tare da tsugunnawa cikin sanyi dason kore tsoro da kuma d'ar d'ar d'in dake ranta tace.

"Zakaci abinci? D'azu bakaci ba duk zubarwa kayi."

Ta k'are maganan tana me d'an son lek'a fuskarsa, tamkar wacce ta samu k'aramin yaro.

batare kuma da ta jira amsar saba, murya atausashe tace.

"Idan zakaci ka d'agamin kai idan kuma ba zakaci ba ka girgizamin kai kaji, bari naje na kawoma abincin."

Ta fad'a tana me mik'ewa tsaye tare da ficewa daga cikin d'akin kaitsaye ta wuce falo.
Ragowar abincin da bataci su ba ta d'auko tare da dawowa d'akin.

Agabansa ta dire try din abincin, tare da bud'e wani plate Wanda cikinsa ke d'auke da wani abincin, da ita kanta batasan sunansa ba, saboda tsabar ganyayyakin dake cike acikin abincin.

Mik'o masa plate din tayi da hannayenta, batare kuma da ta sake saka idanunta akan fuskarsa ba.

"Kaci sai ka koma kayi bacci, babu kyau zama da yunwa."
Tayi maganan tana me kokarin shanye ruwan hawayen dake idanunta, Wanda sam batasan dalilin taruwarsu ba.

Yayinda shi kuwa Majeed tun d'azu yake nan a inda yake, bai motsa komai nasa ba, duk da yanajin muryar nata nayi masa amsakuwa acikin kunnuwansa, amma ya kasa tantance abunda take fad'a, sautin muryar kawai Brain dinsa ke sarrafa masa.
Yayinda zuciyarsa ke motsawa akowanni second, saboda muryar wacce tasa tsikar jikinsa mimmik'ewa.
Daga cikin jikinsa kuwa wani abu yakeji na gudana tamkar jini, saboda matsowar ta kusa dashi.
Saidai bashi da ikon sarrafa idanunsa wajen kallonta,  domin sautin amon muryarta dake ratsa Brain dinsa, shi kesa yakejin yana kallonta, amma daga wani sashi na zuciyarsa, wacce yakejin tamkar ansa gungumen dutse acikinta.

Soumaya kuwa ganin baiyi wani k'wak'walwaran motsi bane, yasa ta sanya hannunta acikin plate din, ta d'ebo abincin acikin tafin hannunta, tare da kai hannun nata kusa da bakinsa.
"Kaci."
Ta fad'a tana me lumshe idanunta.
Kasancewar haka takeyiwa kuliyarta aduk ranan da tak'i cin abinci.

"Bazaici ba Soumaya, Majeed bazai ci ba, koda zaki kwana ahaka dashi bazai ciba, kamar yanda ba zaiyi miki magana ba."

Muryar Billionaire Dawoud ta karad'e d'akin wanda hakan yasa Soumaya dake durk'ushe agaban Majeed din, d'agowa da sauri ta kalleshi.

Ga mamakinta kuwa murmushi ta gani kwance akan fuskar Billionaire Dawoud din, Wanda yake tsaye abakin kofar d'akin, da alama shigowarsa kenan.

Ganin nasa ne kuma yasata maida abincin tare da sunkuyar da kanta k'asa.

Cikin girmamasa da takeyi tace.
"Sannu da dawowa."

"Yauwa Soumaya sannu, naje ina ta nemanki ashe kina nan."

Ya fad'a fuska asake tare da k'arasa shigowa cikin d'akin, saboda wani irin sanyi da yaji azuciyarsa.
Naganin Soumayan zaune agaban Majeed din tana k'ok'arin basa abinci.
Majeed din dake zaune ya kalla, yana mejin zuciyarsa daban.
Duk da cewar ba yau ya fara ganin  Majeed din na salla ba, shiyasa baiyi mamaki ba, dan yasan koda yaushe yana sallan, kasancewar akwai wasu d'abi'u nasa da basu canja ba.
Kamar yanda yake idan mutum ya samu matsalan mental problem daga sama, bawai dashi aka haifesa ba, To Tabbas akwai wasu halayyarsa da ko acikin haukan bazasu canja ba, haka kuma sometimes idan mutum ya sabayin abu, To koda yana cikin situation na mental problem din, bai zama lallai dole ya iya mantawa da abun ba.
Kamar dai Majeed d'in wanda yakasance tun asalinsa baya barin sallah ta wuce shi, haka kuma idan akwai abunda yak'i jini shine k'azanta.

Wannan dalilin yasa ko ayanzu, baya zama acikin k'azanta, saboda yana wanka kamar yanda kowa keyi, haka kuma yana sallah, saidai watarana idan ciwon nasa ya motsa, akan rasa gane gabansa da bayansa.

Domin sai yayi kwana 3 baiyi wanka ko sallan ba, wannan abun shine abunda ke sake sanya dafi acikin zuciyar Billionaire Dawoud.

Atake kuma lokaci d'aya yaji duk wani farincikinsa ya kau, saboda tunowa da yayi cewar, yau ne sati ya zagayo.

Ranar da take zama mafi fargaba da tsoro agareshi, ranar da yake kwana batare da ya samu isasshen bacci ba.
Saboda wata allura da akeyiwa Majeed d'in aduk k'arshen sati, allurar dake sanya sa gigicewa had'i da fita hayyacinsa.

Tabbas yana jin fargaba aduk sanda k'arshen sati zai zagayo, saidai yasani bashi da yanda zaiyi, dole haka zasu ci gaba da jurewa, saboda jarabawar rayuwa ce da Allah ya d'aura musu. 

"Inason ganinki a falo Soumaya."
Billionaire Dawoud din ya fad'a, yana me janye idanunsa daga kan Majeed din, zuciyarsa cike da radadin sanin nanda y'an wasu mintuna Majeed din zai rasa duk Wannan nutsuwar  daya samu.
Wannan yasa jiki asanyaye ya juya ya fice daga cikin d'akin.

Wanda ganin hakan yasa Soumaya'n  jin wani iri,  asanyaye kuma ta tashi tsaye tare dabin bayan Billionaire Dawoud d'in.

Ganinsa tsaye a falonne kuma yasa ta durk'usawa cike da ladabi tace.
"Abba gani."

"ABBA."
Ya maimaita sunan da ta kirasa dashi, Wanda yanzu almost 2years kenan ba ak'irasa da  sunan ba.
Hakan yasa shi jin wani sabon rauni azuciyarsa, tare dajin k'aunar yarinyar, murya asanyaye yace.

"Tashi ki zauna Soumaya, kema kamar y'a kike awajena, kada kiji nauyi na ki d'aukeni kamar Abboun ki."

Kai Soumayan ta sake sunkuyarwa k'asa, tare da tashi ta hau kan kujera kamar yanda Billionaire Dawoud d'in ya buk'ata.

"Gobe zaku fara exam na makaranta ko?."

Billionaire Dawoud din ya tambaya cike da kulawa, batare daya jira amsarta ba kuma ya mik'o mata wata babbar leda dake gefensa.

"Ga Wannan uniform d'inki ne da kuma sauran abubuwan da nasan zaki buk'ata, baya ga haka kuma akwai driver Wanda zaina kaiki da kuma d'auko ki, saboda haka gobe kishirya ki tafi school, banason wannan issues din ya tab'a school dinki, maganan kud'in exam d'inki kuwa dama already nasa anbiya, karki damu kanki da Wannan, sannan akwai phone  da laptop wanda zakina amfani dashi, nasan zai taimaka miki k'warai."

Wani irin sanyi Soumaya taji acikin zuciyarta, Wanda har saida farincikin hakan ya bayyana akan fuskarta.
Cikin jin dad'i ta karb'i ledan, tare da d'an tsugunnawa da yanayin ladabi tace.

"Nagode ABBA."

Kai kawai Billionaire Dawoud d'in ya jinjina, hade da juyawa ya fice daga cikin falon, saboda yana da appointment da wasu, bak'insa da suka zo daga France.

Soumaya kuwa cikin yanayin jin dad'i ta bud'e ledan, tare da soma zaro uniform din da tagani aciki har guda uku, yayinda ak'asan kayan kuwa kud'ine masu yawa, sai kwalin waya k'iran iphone 13 pro max.

Da mamaki akan fuskarta ta zaro wayan, tare da soma jujjuyata, saboda sanin kudin wayar da tayi, dan sometimes tana ganin the same wayan ahannun y'an schools d'insu. 

Ledan dake jikin kwalin ta b'are tare da bud'e kwalin ta ciro wayar, wacce take da colorn blue.
Saidai kasancewar wayar ba akunne take ba, yasa ta maida ita ta ajiye.
Dan zata iya cewa batayi farinciki da wayar kamar yanda tayi na komawanta school gobe ba.

Wannan dalilin yasa cikin jin dad'i ta d'auki kayan ta wuce d'akinta dashi.
Tana shiga ta soma warwarewa, tanajin zuciyarta wasai saboda, ji da tayi ajikinta cewar Tabbas Burinta ya kusa cika.
Fatan ta kuwa bazai tab'a zama matacce ba.

Jakan kayanta da tazo dashi ta jawo, tare da bud'ewa ta ciro littatafan makarantar nata.
Kasancewar already tasan da wani course zasu fara shiyasa ta fara dudduba littatafan nata.

Wanda azahirin gaskiya anata b'angaren hankalinta ya tafi ne izuwa ga karatun da takeyi.

Yayinda daga wani b'angaren kuwa wata zuciyar ke fafutukan neman abunda batasan menene shi ba.
Abunda nemansa ke rikirkita k'wak'walwa da nutsuwar mamallakin zuciyar.

MAJEED.
Akaro na barkatai kenan yanzun daya sake toshe kunnuwansa, had'i da bubbuga kansa dake yi masa wani irin ciwo.

Tamkar zai shid'e haka yakeji, wannan dalilin  yasa shi mik'ewa tsaye, duk da idanuwansa da yakejin suna rufewa, batare kuma daya san inda ya dosa ba, sai ji yayi ya fad'a saman makeken gadon dake d'akin.

Jin hakanne kuma yasa shi k'ank'ame jikinsa waje d'aya, had'e da cusa kansa cikin pillow.
Azafafe ya soma sakin numfarfashi'n da  yakanyi hakanne idan zuciyarsa na fafutukan neman abunda take so.

Abunda harshe da labb'an bakinsa sukayi nauyi wajen furtawa.
Duk da akowacce rana yana rayuwa da abun acikin zuciya da kuma gangar jikinsa.
Tabbas Jin hakan ya zame masa sabo.
Wannan dalilin yasa zuciyarsa ke yawaita bugawa acikin kowanne dak'ik'a.

8:00 pm .
Littafin Physics d'in dake hannun nata tsawon mintuna  ta rufe,  tare da yunk'ura cikin nutsuwa ta tashi daga zaunen da take, had'i da zare hijabin dake jikinta.
Kasancewar idar da sallan isha d'inta kenan taci gaba da karatun da take.

Wanda kuma ayanzun ma ta tashi ne saboda knocking d'in k'ofar falon da taji anayi.
Kasancewar tasan bazai wuce masu kawo abinci ba, hakan yasa ta yafa siririn mayafin ta, tare da fitowa kaitsaye zuwa falon.

Koda ta k'araso jikin k'ofar bud'ewa tayi, kamar yanda tayi tsammani kuwa kuku's ne  guda biyu a tsaye, kowanne kuwa  hannunsa rik'e da tray d'in abinci.

Tray din abincin ta karb'a tare da juyawa ta koma ciki.
Aranta take mamakin irin yanda ake b'arnatar da abinci agidan.
Domin ko breakfast din safe da aka kawo, ko plate d'aya bata iya cinyewa ba, haka ma Wanda aka kawo abincin dominsa.
Yanzu kuma gashi ansake kawo wani trays d'in da samansu ke d'auke da abinci kala kala.

Akan table din dake tsakiyan falon ta ajiye tray d'in.
Saboda babu wani alaman yunwa atattare da ita.

Wannan yasa ahankali ta juya ta nufi hanyar d'akinta, har takai bakin k'ofar shiga d'akin kuma sai ta tsaya cak, tare da juyowa ta zubawa k'ofar Majeed din idanu.

Hakanan taji zuciyarta ta raya mata shiga d'akin,  duk da takanji wani iri aduk sanda yake kusa da ita.
Amma tasan kulawa da komai nasa yanzu akanta yake.
Wannan dalilin yasa ta juyowa asanyaye ta nufi d'akin nasa.

D'aura hannunta akan handle d'in k'ofar da niyan bud'ewa kuwa yayi daidai da shigowar Billionaire Dawoud da kuma Dr. Mouhammad.
Wanda hakan yasa ta dakatawa, tare da d'an sunkuyar da kai cikin ladabi ta gaishe da Dr. Mouhammad d'in.

Fuska asake kuwa ya amsa mata, tare da tambayanta hannunta, Wanda har yanzu yake d'aure da bandage, duk da cewar bawai wani ciwone sosai taji ba.

"Da sauk'i."
Ta amsa had'e da soma k'ok'arin juyawa, daniyar komawa d'akinta, saboda ganin da tayi dukansu d'akin Majeed d'in zasu shiga.

"A'a Soumaya Ina kuma zaki? zo mushiga tare tunda naga dama ai shiga zakiyi."

Billionaire Dawoud ya fad'a yana me nemo aron murmushi ya saka akan fuskarsa.

Soumaya kuwa kanta kawai ta sunkuyar k'asa, bawai dan kuma taso ba haka tabisu abaya zuwa cikin d'akin.

Saidai koda ta shiga daga bakin k'ofa ta tsaya, tare da sauk'e idanunta akan tafukan k'afansa wanda sukayi jajur, saboda wahalan take take da suke sha, duk sunyi ja kana kuma sun d'an kumburo, da alama kuma sunayi masa zafi.

Yanayin kwanciyar da yayi ta kalla, kana asanyaye ta janye idanunta, tare da maidasu ya Dr. Mouhammad wanda ke k'ok'arin zuk'an wani ruwan allura'n daya taho da ita acikin wani madaidaicin akwati.

Yaarrr haka taji tsikar jikinta na tashi, saboda yanda yake zuk'an ruwan alluran da syringe,  kasancewar ita ba mace bace meson allura, shiyasa ko kallonta bata son yi, musamman irin wacce take hannun Dr. Mouhammad d'in ayanzu, wacce sbd girmanta har bata da kyaun gani.

Idanunta ta d'an rumtse alokacin da Dr. Mouhammad ya gama jan ruwan alluran.
Tare da kawar da kanta gefe.
dan tamkar ajikinta za'a soka alluran haka takeji.

Dr. Mouhammad kuwa k'arasawa wajen gadon yayi, tare da d'an sunkuyawa, cikin k'warewa da kuma yanayi irin na shammata, ya caka alluran akan dantsen hannun Majeed d'in, tare da soma fesa ruwan lokaci d'aya.
Wanda hakan yasa MAJEED d'in sakin razanannen k'aran, daya sanya Soumaya sulalewa awajen ta zauna dab'as.
Had'i da k'ank'ame jikinta dake karkarwa.

Yayinda Majeed kuwa cike da tsananin azabar da ruwan alluran ke shayar dashi idan ya ratsa cikin jikinsa, azauce ya soma yunk'urin fusge alluran daga hannunsa, saidai tuni Dr. Mouhammad ya riga daya gama matse masa ruwan alluran acikin jikinsa.

Wanda hakan yasa lokaci d'aya jikinsa ya shiga b'ari tamkar wanda aka jonawa shocking,  atake kuma duk wani gashi dake jikinsa suka mimmik'e, haka ma jijiyoyin kansa lokaci d'aya suka bayyana rud'u rud'u.

Idanu Billionaire Dawoud ya rumtse cike da tsananin tausayin Majeed d'in, ya juya kaitsaye ya nufi hanyar fita daga cikin d'akin, saboda bazai iya jure ganin abunda Majeed din zaiyi anan gaba ba.

Dr. Mouhammad kuwa da yake atsorace sobada sanin k'arfin alluran da yayi wa Majeed din, shima bin bayan Billionaire Dawoud yayi.

Saidai har yakai bakin k'ofar fita d'akin ya dakata tare da juyowa ya kalli Soumaya, wacce ta k'ank'ame jikinta dake b'ari waje d'aya.

"Yauce ranarki Soumaya, hakk'in kulawa dashi na kanki, ki tsaya atare dashi awannan daren, domin ayau ne kulawarki keda matuk'ar mahimmanci agaresa, saboda haka kada ki barshi shi kad'ai, ki kasance atare dashi har zuwa safiyan gobe."

Idanunta ta d'an zazzaro cike da yanayin tsoro, Wanda ya bayyana acikinsu k'arara.

Dr. Mouhammad din dake k'ok'arin ficewa ta kalla, kana cikin tsananin tashin hankali ta kuma dawo da kallonta ga Majeed d'in.

Wanda idanunsa ke kakkafewa, yayinda jikinsa kuwa ke wani irin rawa,  ad'imauce yake sakin ihun azaban dake neman tarwatsa k'wak'walwarsa.
Da Kuma tsayar da bugun zuciyar Soumaya, wacce take gab da fashewa.

*10:44 pm*


You are reading the story above: TeenFic.Net