Chapter Two

Background color
Font
Font size
Line height

                      *MAJNOON!!*
                  (The innocentmad)

*Writting by*
fatymasardauna
           *Wattpad @fatymasardauna*

https://chat.whatsapp.com/HpvXJSFFoZs9S2nIXPa5xh

*(This book is mainly for those that pay, If you know you didn't pay please don't read it. Here is the Account Number for people that are willing to pay- 0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz Bank. WhatsApp number 07069917168)*

             *CHAPTER 2*
*Freepage*

Ta fad'i akan guiwowinta wanda suka riga sukayi sanyi, kana kuma suke b'ari da kakkarwan tsoro da firgicin da ta samu kanta aciki.

"ABBOU!"
"ABBOU!!"

Ta k'ira sunan mahaifin nata cikin muryarta wacce ke rawa, saboda tsananin tashin hankalin daya rusketa.
Tare kuma da rarrafawa zuwa garesa.
Koda ta karisa
Sunkuyowa kansa tayi tana me kallon fuskarsa, da kuma idanunsa wanda suke a rufe ruf basa ko motsi.

"ABBOU! Abbouna!!"
Ta sake kiran sunansa cikin tarin fargaban dake dukan kirjinta, kana tana me girgizasa da hannayenta, zuciyarta cike  da fatan ganin ya bude idanunsa.

Rashin ganin hakanne kuma yasa ta, tallafo kansa ta d'aura akan cinyarta, cike da tsananin tashin hankali ta daura hannunta, adaidai saitin hancinsa.

Daidai lokacin kuwa Moudou dake cikin d'aki tana kallo ta fito, da niyar surfa fad'a saboda ihun Soumaya'n da taji, Wanda bisa dole ya taso ta.

Da yake kwata kwata ita din ba mace bace mai damuwa da sha'aninsu, shiyasa cikin fad'a tace. 
"Ke Soumaya lafiyanki k'alau kuwa, kodai kin fara haukane?, ko kuwa aljanune suka shiga kanki?."

Ta fadi hakan tana me kokarin karasowa inda Soumaya'n ke durkushe.

Soumaya ko jin muryar Moudoun abayanta ne, yasa ta juyowa da sauri, cikin tashin hankali da kuma  firgicin da ta samu kanta aciki, murya na rawa tamkar wacce aka jonawa shocking tace.

" Abbou na Moudou, ABBOU ne....."

Sauran maganan nata ya mak'ale saboda wani irin,  matsanancin kukan daya k'wace mata, still kuma tana me jijjiga Abboun da kansa ke kwance bisa cinyarta baya ko motsi.

K'irji da zuciyar Moudou ne suka buga atare, lokaci daya cikin yanayin tashin hankali,  ta tsurawa fuskar Abboun dake kwance idanu, zuciyarta cike da fargaban kada hasashe da kuma abun da tajima tana rayawa acikin zuciyarta ya zama gaskiya.

D'an jim tayi, zuciyarta cike da sak'e sak'e kala kala, wani sabon tunani da yazo ranta ne, Kuma yasa ta had'e fuska.
Cikin halinta nako inkula da tasaba yi musu, murya adak'ile tace.

"Shine kiketa kururuwa tamkar wacce ake zarewa rai? Kukan nakine zaisa shi dawowa cikin hayyacinsa?."

Da sauri ta soma girgiza kanta, still da muryar kuka tace.

"Moudou baya numfashi, mukaishi asibiti banason wani abu ya sameshi.."

"To idanu zaki zubamin ko kuma zaki tashi ne kije ki nemo mai taxi ko adaidaita sahu mu kaishi asibiti."

Moudou ta tambaya tana me watsawa Soumaya'n harara, dan daga ita har baban nata duk haushinsu takeji.

Soumaya ko jin abunda Moudou'n ta fad'a ne yasa ta, d'ago da kanta had'i da  idanunta wanda suke tsiyayar da ruwan hawaye tamkar a kunna famfo, ta kalli Moudo'un zuciyarta cike da tausayin kansu, dama kuma halin da suke kokarin fad'awa cikinsa ayanzu.

Tabbas bata da wani zabi wanda ya wuce, aikata abun da Moudou'n ta fad'a, hakan yasa cikin hanzari ta tashi daga durk'uson da take.

Arude ta nufi dakinta dan d'aukan mayafin da zata rufawa jikinta.
d'aya daga cikin lufayunta da take ajiyewa akan y'ar katifarta ta d'auka, batare da ta jira ta gama saka hijabin ba kuwa, haka ta nufi hanyar fita daga cikin gidan.
Hawaye na ambaliya akan fuskarta.

Da sassarfa mai kama da gudu gudu, ta k'araso kan babban tititin daya malale cikin unguwar tasu.
Wanda tsirran motoci ke wucewa jifa jifa.
Koda ta iso bakin titin kuwa babu kowa awajen, musamman ababen hawa na haya babu ko d'aya dake gilmawa akan titin, sai dai manyan motocin masu kudin anguwar dake wuce wa.

Su kuwa ko ka tsaidasu dama ba tsayawa zasuyi ba.

Hagu da damanta ta kalla, rashin ganin abun hawan da zai taimaka mata, yasa ta rumtse idanunta, araunace kuma cikin tsananin damuwa da fargaban ganin mahaifin nata da tayi awannan halin, yasa murya na rawa, cikin sigar neman  taimako tace.

"Allahumma La sahala illama ja'altuhu sahala, wa'anta taj alul hazna iza shiyta hasla, Yah Allah Kataimakeni, Yah Allah...."

Ta kare maganan tana kuka, hade Kuma da Ware idanunta, cikin matuk'ar sa'a kuwa ta saukesu akan wani taxi dake fitowa daga can cikin unguwar.

Da sauri tasa hamannayenta duka biyu ta soma kokarin taresa, batare kuma da ta jira ya karaso gareta ba, ita ta soma kokarin karasawa.
Wanda hakan yasa saura k'iris mai taxi din ya kad'eta.

Kiiiiiii..
Haka mai axi din yaja burki saboda ganin da yayi tayo kanshi, harma ya kusa take ta.

Ai ko gama parking din motar baiyi ba, da sauri ya bud'e murfin motar ya fito, fuskarsa dauke da yanayin damuwa, saboda yasan irinsu y'ay'an masu kud'i, idan ya kad'eta to ya kad'owa kansa masifa, Dan bashi da wani abu dazai iya kare kansa dashi, iyayenta sai su d'aureshi har sai igiya ta saura.

"Haba Yarinya bakya gani ne, kike kokarin kawo kanki tsakiyar titi, yanzu da na taka.......""

Shiru yayi tare da kasa k'arasa maganan nasa daya soma, saboda yanda yaga hawaye na ambaliya akan fuskarta, wannan dalilin yasa shi tsayawa yana kallonta, zuciyarsa cike da fargaba da kuma tsoron cewa kada daima ace harya takata baisani ba.

Soumaya'n dake cikin tashin hankali kuwa, Sam ma bata lura da cewar mai taxi din ya kusa kad'eta ba.

Saidai ganin yanda mai taxi din ya tsaya yana kallonta ne, yasa ta karasowa inda yake.

Cikin muryar kukan dake bayyana damuwarta tace.
"Dan Allah Mallam Ka taimakeni, Abbouna bana son wani abu ya sameshi,  Dan Allah ka taimaka mukaishi asibiti."

Tayi maganan tana me had'e duka hannayenta biyu awaje daya,  yayinda idanunta dake zubar da hawaye ke  kallon k'ofar gidansu.

D'an jim mai taxi din yayi, yana me k'arewa  kyakkyawar budurwar yarinyar kallo,  saboda saida ya matso kusa da ita, sai yake ganin kamar ba mutum bace.

Wannan dalilin yasa cikin son samawa kansa lafiya yace.
"Kiyi hakuri natashi a aiki, yanzu ma sauri nake na koma gida, saidai ko zaki tari wani, gashi duk asibitotin gari ma yanzu suna yajin aiki."

Yayi maganan yana me kokarin komawa cikin motarsa, kasancewar lokacin anata shirye shiryen kiran sallan magriba.

Ganin da tayi yana kokarin tafiya ne kuma, yasa da sauri  ta rik'o murfin motar nasa, hankalinta amatukar tashe, then still cikin kuka tace.

"Dan Allah karka tafi, Abbouna baya numfashi ka taimakemu Dan Allah...."

Idanu mai taxi din ya zuba mata, bawai saboda yana mamakin yanda take kukan ba, aa kawai dai yana mamakine game da yanda kyawunta yake.

Saidai kuma daga gefe guda kukan yarinyar da yasan bazata wuce, 18 to 19 years ba ya matuk'ar tab'a masa zuciya.

Saboda kuka ne da yaga tanayi nagasken gaske.
Ajikinsa kuma yaji cewa lallai tana bukatar taimako,
Hakan yasa  shi bude murfin motar ya fito waje..

"Muje."
Ya fad'a yana me rufe murfin motar.

Soumaya kuwa da sauri ta juya harta na cin tuntub'e haka ta nufi cikin gidan nasu, yayinda mai taxi din ya rufa mata baya.

Da gudu ta shigo cikin gidan, tare da durk'usawa ta tallafo Abboun nata jikinta.

"Abbouna."
Ta kiran sunansa asanyaye, tare da tab'a gefen wuyansa, saboda yanda taji jikin nasa ya d'au zafi sosai. 

"Barin tayaki mu d'aga shi ko."
Mai taxi din ya fad'a yana me kokarin sunkuyowa dan d'ago Abboun daga kwance.

Kasancewar kuma Abboun ba mutum ne mai garin jiki ba, shiyasa bayi da wani nauyi, asauk'ak'e mai taxi din ya d'agosa, inda Soumayan ta taimaka duk da bata da wani k'arfi, amma duk rabin jikin Abboun yana nata jikin.

Ahaka suka fito dashi daga cikin gidan, Kaitsaye suka wuce wajen taxi din.

Suna zuwa kuwa mai taxi din ya bud'e gidan baya, suka kwantar da Abboun aciki.

Daidai lokacin Moudou ta fito sanye da mayafinta , bayan tasa dan makulli ta kulle gidan, fuska duk babu fari'a, haka ta k'araso wajen motan.

Gidan baya inda aka kwantar da Abboun ta shiga, Wanda tuni Soumaya ma tana ciki.

Mai taxi din kuwa ganin da yayi  duk sun shiga ne, yasa shi jan motar ya nausa izuwa kan titi.

Sanin cewar kuma Ana yajin aiki a k'ananun hospitals dake cikin garin ne , yasa kaitsaye NIZAMIYYE Hospital ya nufa dasu.

Idanunta da har yanzu suke tsiyayar da hawaye ta zubawa, fuskar Abboun nata wanda kansa ke kwance bisa cinyarta.

Bata fatan wani abu ya samu mahaifinta, domin kuwa shine komai nata.
Shine mutumin daya kasance Bango kuma majingina agareta.
Shine madubin rayuwarta,  haka kuma shi kad'ai ne wanda yake bata farinciki acikin rayuwarta.
Shin Tayaya zata iya rayuwa babu shi?
Tayaya farinciki zai samu idan babu shi?
Waye zai kawar da duk wani damuwanta?

Tunanin da takeyi acikin zuciyarta kenan, Wanda suka sanya hawayen dake cikin idanunta kara tsananta.

Daidai lokacin suka iso kofar babban asibitin Nizamiyye.

parking motar mai taxi din yayi, tare da juyowa ya kallesu, cike da son taimaka musu yace.

"Bari na zagayo mushiga dashi ciki ko."

Kai Soumaya ta jinjina masa da sauri.

Take kuwa ya zagayo suka fito da Abboun, da taimakonsa suka nufi can cikin asibitin.

Cikin sa'a kuwa suna shiga suka had'u da wasu Norse's.
Kamar kuma yanda yake duk emergency patient ana bashi kulawa, before komai hakan yasa suna ganin jikin Abboun, take nurses din suka d'auko irin gadonnan na marassa lafiya, aka d'aura Abboun akai.

Direct emergency room aka wuce dashi,  domin duba lafiyarsa.

After 15mn.

Tsaye suke dukansu a k'ofar emergency room din.
Yayinda kowannensu da irin abunda yake sak'awa acikin rai da zuciyarsa.

Saidai banda ita da tunani da kuma nutsuwar zuciyarta suka kau.
Wani irin tarin fargaba takeji acikin ranta.
Sanadiyar hakanne kuma yasa hawayen dake cikin idanunta kasa tsayuwa.

"To nizan wuce Allah Ya k'ara sauki, ya kuma sa zakkan jiki ne."

Mai taxi din nan daya biyosu har bakin emergency room din ya fad'a, cike da tausayawa.

"To Bawan Allah mungode sosai Allah ya biyaka da alkahiri."

Moudou ta amsa masa ahanzarce dan dama batayi niyan biyansa ko sisi ba.

Souamaya kuwa idanunta da sukayi jajur ta zuba masa, kana cikin raunatacciyar muryarta mai dauke da tarin damuwa tace.

"Mungode sosai Malam, duk da nasan bazamu tab'a iya biyanka ba, amma nawa ne kudinka?"

Murmushi Mai taxi din yayi, hade da d'an girgiza kansa, cike da tausayawa yace.

"A'a ni Dan Allah Nayi, saboda haka bana bukatar wani abu, Allah Ya bashi lafiya."

"Amin."
Soumaya ta amsa, tana me binsa da idanu, kasancewar har ya juya ya fara tafiya.

Moudou dake tsaye kuwa, Soumaya'n take ta watsawa harara, zuciyarta cike da haushin d'agota da sukayi zuwa asibiti da magriban Allah, babban abunda ke sanya bugawar zuciyarta kuwa shine, abunda zaije ya dawo agame da rashin lafiyan Abboun.

6:30 pm.

Izuwa yanzu mintuna 20 kenan da suka d'auka suna tsaye abakin emergency room din.

Haka kuma mintuna 20 kenan da doctors din dake cikin emergency room din, suka kwashe suna mai kokarin daidai ta numfashin ABBOU, amma duk yanda suka so abun yaci tura.

Ganin abun na kok'arin fin k'arfinsu ne kuma, yasa su yanke hukuncin wucewa dashi ICU kaitsaye saboda, acanne zai samu ganin babban Doctor'n su, wato DR Mouhammad Boulama.
K'wararren likita kuma babba wanda yasan aikinsa sosai.

Acan wajen emergency room din kuwa Soumaya ce ke zaune, tayi jigum
yayinda ta manna kanta da jikin bango. Daga cikin raunanniyar zuciyarta kuwa.
Sunayen Allah take ta ambatowa, cike dasa duk wani fatanta akansa..
izuwa yanzu kuwa ta zubar da hawaye masu yawan gaske, har saida cikin idanunta sukayi jajur. 

Daga can gefenta kuwa Moudou ce zaune, rike da yar wayarta kirar techno mai keypad, sai faman latsawa take, da alama kuma wani Number take nema.

Motsin bude kofar emergency room din da akayi ne, kuma yasa duk suka d'ago idanunsu.
Musamman Soumaya wacce hakanan taji zuciyarta na bugawa, wannan dalilin yasa ta tsurawa likitoti biyun da suka fito daga emergency Room din idanu.

D'aya daga cikin doctors dinne ya k'araso inda suke, yana me kokarin zare hand gloves din dake hannunsa.

"Likita ya jikin nasa? Ya farfad'o ne?."

Moudou ta tambaya, cike da fargaban kada agaya mata mutuwarsa.

Ajiyar zuciya Doctorn ya d'an sauk'e, kana cikin son kwantar musu da hankali yace.

"Jikinsa yayi worst sosai, saboda haka dole sai yaga babban Dr dinmu, yanzu haka zamu wuce dashi ICU ne, amma karku damu insha Allah zai samu sauki."

Ya kai karshen maganan yana me kallon yarinyar da ta tsaresa da idanunta, da sukayi ja sosai.

Duk shiru sukayi gaba d'ayansu, yayinda shi kuwa Doctor'n ya rab'a ta gefensu ya wuce.

Wasu irin zafafan hawaye ne suka gangaro daga cikin idanunta, zuwa kan k'uncinta, cike da raunanta had'i da rashin k'warin zuciya ta koma ta sake jingina jikinta da bango.

Still  kofar Emergency Room din ne ya sake budewa.
Inda wasu nurses guda uku suka fito suna tura gadon nan na marassa lafiya, Wanda aka kwantar da Abboun akai.

Ganinsu da tayi ne kuma yasa azabure tayi kansu,  saidai kasancewar kuma suna sauri sosai ne, yasa ta kasa cimmusu saboda dakatar da ita, da d'aya daga cikin nurses din tayi.

Bisa dole haka ta tsaya akan k'afafunta dake rawa, daga can nesa ta  zubawa fuskar mahaifin nata idanu, duk da cewar baiyi wani nisa da ita sosai ba, amma dishi dishi take kallonsa, saboda ruwan hawayen da suka cika mata idanu.

Hakanan acikin zuciyarta, sai takejin cewa tamkar ta rasa shi ne.

Ya zatayi da irin wannan rayuwar da take shirin fuskanta.
Hakika ta sani cewa ita yarinyace mai rauni da kuma raunannar zuciya.
Wannan dalilin yasa idan wani abu ya samu Abbounta zata shiga cikin gararin rayuwa.

"Soumaya Soumaya!! Me yake faruwa ne meya samu Abboun naki? Yana Ina yanzu?".

Duk aka jefo mata way'annan tambayoyin, da muryar Malam Musbahu wacce sautin ta ta fito daga bayanta.

Juyowa tayi asanyaye, duk da cewar tasan me muryar amma hakanan taji tanason ganinsa acikin idanunta.

"Soumaya!"
Still Malam Musbahu da isowarsa cikin asibitin kenan, ya kira sunanta fuskarsa d'auke da tsananin damuwan, yanda yaga hawaye cab'a cab'a akan fuskarta.

Asanyaye ta d'an tako kafafunta zuwa inda Malam Musbahun yake.

Cikin muryan kukan dake kokarin fin karfinta, ta kamo hannun Malam Musbahun.
Hakanan takejinsa tamkar d'an uwa ne agaresu, wannan dalilin yasa  cikin sigan bayyana tsananin rauni da damuwarta  tace.

"Baffa Ab..b..ouna, ka taimakeni banason rasashi....." 

Yanayin  yanda tayi maganan cikin muryar kuka ne, yasa idanun Malam Musbahu ci kowa da hawaye.

Saboda yafi kowa sanin tsananin kaunar dake tsakanin Soumayan da mahaifinta.

Hannunsa yasa ya d'an dafa kafad'anta, cike dason kwantar mata da hankali yace.

"Insha Allahu Abbounki zaiji sauki, zai tashi kuyi rayuwa kamar yanda kuka saba, ki daina wannan kukan kinji Soumaya."

Kai ta jinjina masa, duk da batajin k'warin guiwa ajikinta, amma tayi believing cewa Allah bazai barsu haka ba.
D'an zame jikinta tayi tare da zama akan wani dogon benci dake wajen.

Sai alokacinne kuma ta lura da kanta, da kuma kayan uniform din dake jikinta,  saboda rudewan da tayi ne Kuma yasa, ko takalman dake  k'afafunta bata sasu adadai ba, duk da cewar normal takalma ne irin wanda take zaman gida dasu.

Kanta tad'an langwab'ar gefe tare da lumshe idanunta, tana me sauraran yanda zuciyarta ke bugawa da karfi.

Malam Musbahu dake tsaye agefe kuwa shi dinma yanzu zama yayi akan bencin, tare dayin zugum zuciyarsa cike da zullumin abunda zai faru.

Tabbas Tsoro da fargaban abunda zaije ya dawo yake, domin yasan lokaci yayi da dole Soumaya zata San abunda Abboun nata bayaso ta sani, abunda ya jima yana b'oye mata yanzu dole zata sani, lokacin bayyanar abun yayi, abunda suka jima suna tsoron bayyanuwarsa.
Abun dazai dakatar da duk wani farincikin su, tare da maishe da abu guda izuwa rabi.

*Intensive Care Unit*

Dr. Muhammad Boulama ne ke tsaye agaban gadon da Abboun ke kwance, Wanda aka riga da aka sawa wasu na'urori na musamman akansa.

Gyara zaman Na'urar Oxygen din da aka sawa Abboun yayi, kana cikin mamaki da kuma al'ajabin abundake zuciyarsa, yasa hannu ya goge gumin dake tsatstsafowa daga goshinsa.
Duk da cewar sunyi nasarar ceto numfashin patient din nasu, amma akwai sauran aiki mai yawa agabansu.
kasancewar ciwon nasa yayi worst sosai.

"Su waye suka kawoshi?"

Dr. Muhammad Boulama'n ya tambaya, yana me kallon d'aya daga cikin doctors din da sukayi aikin tare.

"Inaga matarsa ce da y'arsa."
Doctor'n ya bashi amsa, yana me zare hand gloves din dake hannunsa.

"Okay ka fad'a musu su sameni a Office."

Dr Mouhammad din ya fada cikin hanzari, tare da juyawa ya fice daga cikin dakin.

Kaitsaye babban office dinsa ya nufa,  Dan kasancewarsa babban DR shiyasa komai nasa ya kasance na musamman acikin asibitin.

Tura kofar office din nasa yayi ya shiga, Wanda shigarsa cikin office din yayi daidai da shigowar kira cikin wayarsa, dake aje akan babban table dinsa.

Jin kiran ya kusa katsewa ne kuma yasa cikin dan sauri ya karasa inda wayar tasa take, tare da leka screen din dan ganin sunan wanda ke kira. 

*"BILLIONAIRE DAWOUD SARAKI"*

Ya maimaita sunan akan harshensa.
Aransa yana me tunani da kuma fargaban abunda zaiji dangane da ciwon.

*MAJEED.*

(Karku manta wannan littafin ba Freebook bane, ga wacce takeson ci gaba da karantashi zata biya 300 naira ne kacal, zata tura kudin ta Account Number 0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz Bank ko kuma MTN card ta WhatsApp's Number, but banda VTU, then idan kika tura zaki turomin evidence na Payment dinki, ta WhatsApp Number na 07069917168 thank you my  lovely fans!)

*2:30 pm*

You are reading the story above: TeenFic.Net