Chapter Seven

Background color
Font
Font size
Line height

*MAJNOON!!*
           (The innocentmad)

*Writting By*
Fatymasardauna
   *Wattpad*
@fatymasardauna

*(This book is mainly for those that pay, If you know you didn't pay please don't read it. Here is the Account Number for people that are willing to pay-0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz Bank. AMOUNT 300, WhatsApp Number 07069917168)*

          
             *CHAPTER 7*

*FREEPAGE*


"Lallai wannan shine hanya guda d'aya, wacce zata warware matsalolin da dukanmu muke k'ok'arin fad'awa cikinta."

Abunda Dr. Mouhammad ya fad'a, kenan cike da kokarin samarwa kansa k'warin guiwa, had'i da yarda da abunda zuciyarsa ta gama shirya masa.

Jin zuciyarsa ta gama samun gamsuwa ne kuma,  yasa shi maida envelope din cikin aljihun rigar suit din dake jikinsa,  tare da juyawa kaitsaye ya nufi hanyar fita daga cikin office din.

SOUMAYA!!

Sama da mintuna 10 kenan yanzu da suke zaune ahaka, yayinda daga ita har Malam Musbahu babu Wanda ya sake cewa komai, gaba d'aya hankali da tunaninsu ya tafi izuwa waje na daban, kowa da irin tunanin da yakeyi acikin zuciyarsa.

Turo k'ofar d'akin da aka yi ne, kuma yasa gaba d'aya duk suka maida kallonsu ga bakin kofar, dan ganin me shigowa.

Dr. Mouhammad kuwa wanda shike kokarin shigowa cikin d'akin ne, ya d'an tsaya tare da zaro wayarsa wacce ta soma ringing, batare daya yi picking call d'in ba, kuma yayi off na ringintone din.

Sannan  ya k'arasa shigowa cikin d'akin,  hannunsa rike da wasu abubuwan gwaje gwaje.

"Likita barka da shigowa."
Cewar Malam Musbahu yana me d'an gyara zamansa.

Kai Dr. Mouhammad din ya jinjina, had'i da amsawa ta hanyar cewa.

"Yauwa sannu Malam Musbahu, ya me jikin?"

"To gashinan dai muna neman sauk'i awajen Allah."

"Allah ya Kara sauk'i."

Dr. Mouhammad din ya fad'a, yana me k'arasawa jikin gadon, Wanda tuni Soumaya ta matsa gefe, inda ta cusa kanta acikin tsakankanun cinyoyinta.

Wasu y'an gwaje gwaje Dr. Mouhammad din yayiwa Abboun,  tsawon mintuna 7 kafun ya juyo.

Soumaya dake zaune ya tsurawa ido, duk da cewar baya ganin fuskarta, amma yana iya jiyo d'an sautin sheshshek'an kukanta dake tashi.

Wani irin ajiyar zuciya ya sauk'e, kana ahankali kuma ya dawo da kallonsa ga Malam Musbahu, Wanda yayi tagumi da duka hannayensa.

"Malam Musbahu ko zan iya ganinka a office dina yanzu."

Dr. Mouhammad din Ya fad'a yana me duba agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunsa.

K'irjin Malam Musbahu ne ya yi wani irin bugawa, saboda jin abunda Dr. Mouhammad din ya fad'a, saidai kuma gudun kada ya nuna saurin karayarsa, yasa cikin dakiya dason arawa kai jarumta murya asanyaye yace.

"Babu damuwa likita Muje, Soumaya ki zauna ki kula da kyau bari naje na dawo."

Ya yi maganan yana me mik'ewa tsaye, tare dabin bayan Dr. Mouhammad wanda tuni ya riga daya fice daga cikin d'akin.

Soumaya kuwa Jin abunda Malam Musbahun ya fad'a ne ya sata d'ago kanta, tare da bin bayansa da ido harya fice daga cikin d'akin.

Kanta ta d'an langwab'ar a hankali, tare da lumshe idanunta wanda sukayi jaaa.

Sassanyan numfashi take fitarwa ahankali, kuma take sauraran bugun zuciyarta, bugun xuciyar da takejin ya zarce k'a'ida, saboda har yan yatsun hannunta ganinsu take suna motsawa su kad'ai, Wanda kuma hakan ya faru ne saboda k'arfin bugun zuciyar nata da yake tafiya without control.

Hannu tasa ta dafe kanta, da takejin yana juyawa tamkar ana waina mata shi.

Sannan ahankali ta sake d'an matse idanunta saboda wani irin duhu da take gani acikinsu.
duhun da ya soma rikid'e mata izuwa, kyawawan lips din da sukayi ja, tamkar zasu d'igar da jini, saboda yanda mamallakin lips din, ke caccakarsu da kyawawan milkcolor teeth dinsa, sautin nishi da kuma numfashin mai kama da gurnanani, shi ta ke ji yana amsa amo acikin kunnuwanta.

Wanda hakan yasa da sauri ta bud'e idanunta, tare dasa hannu ta dafe k'irjinta.
Kamar da gaske sannan kuma kamar a mafarki, haka takejin abubuwan na dawo mata.

Tabbas tasan cewar mafarki ne bawai gaskia ba, amma meyasa meye had'in ta da mutumin da ta gani amafarkin?

Tambayan da tayiwa kanta kenan, Wanda ba kuma ta da amsarsa.

Ajiyar zuciya ta d'an sauk'e tare da, sake gyara zaman ta inda ta sauke idanunta akan agogon dake cikin d'akin.

1: 50 pm. Shine abunda ta gani, Wanda hakan yasa ta d'an shiga mamakin, abunda yasa Malam Musbahu tun da ya fita har zuwa yanzu bai dawo ba.
Gashi lokacin sallan azahar yayi, wannan dalilin yasa ta tashi, ta shiga cikin toilet d'in dakin.
Alwala ta d'auro bayan ta fito ne Kuma ta shumfud'a sallaya, tare da data sallah.

Malam Musbahu.
Akaro na barkatai kenan daya sanya  hannu,  ya share gumin daya gangaro daga cikin kansa.
Duk da sanyin A/C'n dake cikin masallacin kuwa shi gumi yake had'awa, gumi irin wanda ke bayyana tsananin damuwa had'i da tashin hankalin da yake ciki.

Adaidai lokacin da kowa ke fita Daga cikin masallacin, kuma shi sake gyara zama yayi.
Saboda kalaman Dr. Mouhammad way'anda ke tayi masa yawo acikin kunnuwansa, kalaman da yake ganin tamkar bazasu tab'a yiwuwa ko zamewa gaskiya ba.
Haka kuma kalaman da suka tsaida duk wani tunaninsa.

Tabbas ada yana cikin damuwa, saidai kuma sabuwar damuwar da ta kunno masa kai ayanzu, tafi wacce tazo ta sameshi acikinta.

Abubuwan da suka ci gaba da yawo acikin tunaninsa ne kuma,
ya sashi soma girgiza kai, zuciyarsa ko cike da shakkun hakan.
Domin yasan abune mai wuya, iya fuskantar Soumaya da maganan, dake cikin zuciyarsa.

"MAJNOON!!!"
Ya maimaita sunan akan harshensa, wanda jinsa yafi komai hautsuna masa tunani.

Sake girgiza kai yayi, cikin kuma rashin kwarin guiwa, had'i da kuzari ya mik'e tsaye, tare da ficewa daga masallacin, kaitsaye cikin  Nizamiye Hospital din ya nufa, zuciyarsa cike da wasu wasi kala kala. 

Yana shiga cikin asibitin kuwa direct, d'akin da aka kwantar da Abboun ya nufa.

Asanyaye ya tura kofar d'akin bakinsa kuwa, d'auke da sallama ya kutsa kansa ciki."

Jin muryarsa ne kuma yasa Soumaya dake zaune akan sallaya, saurin d'ago  kanta ta kalleshi.

Ganin yanayin nasa ne yasa  ta zubawa fuskar tasa idanu, wacce babu wani mahaluki dazaiyi tozali da ita, batare da ya gane cewar tana cikin damuwa ba.

Akaro na barkatai taji zuciyarta ta kuma karyewa, Wanda hakan yasa dole tayi k'asa da kanta, tare da ci gaba da murza y'an yatsun hannunta.

Shikuwa Malam Musbahu asanyaye ya k'arasa shigowa cikin d'akin, tare da neman waje ya zauna acan gefe.

Idanu ya zubawa Soumaya'n, Wanda fargaba ya hanata juyowa ta sake kallonsa.

Wani irin kallo yakeyi mata mai d'auke da tsananin tausayawa, kallon daya haddasa masa rauni acikin zuciyarsa.
Hakika ita din yarinyace k'arama amma Allah Ya jarrabeta da k'addarori masu girma.
Jarrabawa akan wata jarrabawar, tabbas yasan cewa k'addara bata gushewa har sai ta afku, amma k'addarar Soumayan tazo da girma.
Kasancewar yasanta mace ce me raunin zuciya, haka kuma yarinyar da bai kyau tu, ace tasan k'uncin rayuwa ba.

Hawaye ne yaji sun cika masa ido, na tsananin tausayinta, yayinda maganganun da sukayi da Dr. Mouhammad kuwa ke ci gaba dayi masa yawo acikin kansa.

"Baffa!"
Soumayan ta kira sunansa asanyaye, tare da zuba masa narkakkun idanunta, da k'iris suke jira su d'igar da ruwan hawayen dake cike a cikinsu.

Jin shiru bai amsa ta bane kuma yasa ta d'agowa, ta kalleshi.

"Baffa!"
Ta sake kira'n sunansa akaro na biyu, zuciyarta cike da rauni, saboda ganin da tayi bai amsa ta ba, gashi kuma kamar yana cikin duniyar tunani.

Hak'ik'a duk da cewar tana d'auke da k'ananun shekaru, amma tana iya gane yanayin fuskar mutum idan yana d'auke da damuwa, wannan dalilin yasa  ta fahimtar cewa Baffan yana  cikin damuwar da ta zarce wacce yake ciki a farko.

Wannan yasa ahankali ta taso daga zaunen da take, tare da ninke sallayan da tayi sallan akai.
Sam batason sakejin wani abu dazai d'aga mata hankali dangane da rashin lafiyar Abboun nata.

Hakan yasa cikin d'an d'aga murya, yanda tasan Malam Musbahu'n zai jita tace.

"Baffa zan tafi gida."

Aikuwa firgigit muryar nata ya dawo dashi daga cikin duniyar tunanin da yake, hakan yasa ad'an zabure ya d'ago ya kalleta.

"Har zaki tafi ne Soumaya."
Ya fad'a yana me kokarin tura hannu acikin aljihun rigarsa.

"Eh Baffa gobe muna da test, gashi kuma ban wanke uniform d'ina ba."

Ta yi maganan tana me d'an murza yatsun hannunta.

"To shikenan ga wannan idan kinje gida saiki d'an samu abu kici, nima yanzu akwai inda zanje, saboda likita yace akwai nurses din da zasu kula dashi koda dukanmu bama nan."

Ya k'are maganan yana me mik'o mata, tsohuwar naira 500 da ya ciro daga cikin aljihunsa.

Kai ta girgiza cike dajin nauyin karb'an kud'i daga hannunsa, murya asanyaye tace.

"A'a Baffa Ina da sauran 200 nasan zai kaini gida."

"Kul karb'a maza kije Allah ya tsare."
Baffan ya fad'a cikin son b'oye damuwarsa.

Ganin hakanne kuma yasa ta amsa, tare dayi masa godiya.
Kamar kuma yanda ta saba, saida ta kalli fuskar Abboun nata, kafun ta juya  cikin nutsuwa  ta fice daga cikin d'akin.

Tana  fita kuwa Malam Musbahu ya zuba ta gumi, tare da zama jigum yana mai ci gaba da, tunanin maganganun da sukayi da Dr.Mouhammad.

Soumaya kuwa koda ta fito daga cikin asibitin, direct adaidaita sahu ta shiga wanda shiya kawota har kofar gida.

Kamar kuma koda yaushe yanzun ma gidan nasu babu kowa, sai y'ar kuliyarta dake ta shawagi tana tattake ganyayyakin bishiyansu na fruit Wanda suka zubo k'asa.

Kasancewar duk batajin dadin yanayin nata ne, yasa Direct d'aki ta wuce, batare da ta kula cutie'n nata ba.

Tana shiga d'akin kuwa kayan uniform d'inta masu datti ta d'auko, Wanda tun ranan saturday ya kamata ace ta wanke, amma rashin lokaci da kuma damuwar da take ciki ya hanata.

Kayan uniform din ta zubawa ido, saidai kuma amma azahirin gaskiya basu din take kallo ba, fuskar Malam Musbahu dake d'auke da damuwa take kallo, acikin nata idanun.
Tabbas ayanda taga fuskarsa tasan cewa akwai matsala, matsalan da duk yanda taso gaji, dole zata hak'ura, saboda tasan hakan shine kawai zai sama mata nutsuwar zuciya.

Haka dai asanyaye ta kwashi kayan, tare da ficewa waje ta wankesu.
Bayan ta kammala ne kuma ta shiga kitchen ta dafa sauran shinkafa gwangwani biyun
daya rage.

Bayan ta kammala girkinne kuma, ta d'iba acikin plate tare da wucewa d'aki.

Saidai duk yanda takai ga jin yunwa, ta kasa cin abincin yanda ya kamata, saboda har yanzu bata jin kanta acikin yanayi na dad'i.

Wannan dalilin yasa ta faka abincin a gefe.

Tare da tashi ta d'auro alwalah, kasancewar ansoma
kiraye kirayen Sallah'n la'asar.

Bayan ta kammala alwalan ne kuma, ta koma d'akin tare  da shumfud'a sallaya ta tada sallah.

Koda ta idar da sallan kwanciya tayi, had'i da lumshe idanunta,  duk da tasan cewar tana da karatun test amma batajin cewar zata iyayi harya shiga cikin Brain dinta.
Sake gyara kwanciyanta tayi ahaka  bacci b'arawo ya d'auke ta.

Baccin da tayisa na rashin dad'i saboda wasu irin mafarkai da ta dinga yi.

After some minutes ago.

Firgigit ta farka daga baccin nata had'i da tashi zaune, hannu tasa ta d'an rik'e kanta wanda takejin yana juyawa.
Lokaci d'aya kuma mafarkin da tayi yanzun, ya shiga dawowa cikin kanta filla filla.

"Innalillah!"
Shine abunda ta fad'a alokacin da, hoton idanunsa suka dawo cikin nata idanun, Wanda har saida hakan ya haifar mata da matsanancin bugun zuciya, had'e kuma da mimmik'ewar tsikar jikinta.

Hannunta na dama tasa ta mummurza idanunta, Wanda takejin sunyi mata dishi dishi, saboda tunowa da irin tsananin hasken da taga kanta aciki, yasa ta sauke ajiyar zuciya, tare da mikewa tsaye, cikin sanyi ta nufi waje dan d'auro alwalan sallan magriba.

Koda tayi sallan, a sujjadanta na k'arshe addu'o'i sosai tayi, kafun daga bisani ta sallame sallan.

Jakar makarantar ta dake gefe ta jawo, tare da d'auko littafin chemistry d'inta, kasancewar gobe ne suke da test din chemistry din.
Tasani akwai buk'atar dole sai tayi karatu sosai, saidai kuma duk yanda taso yin karatun abun yaci tura.

Kasancewar duk wani tunanin ta ya cushe.

Goshinta ta d'an dafe da hannayenta, tare da cije lips dinta.

"Yah Allah!"
Ta fad'a tana me jujjuya littafin chemistry din dake hannunta,  saboda kwata kwata  karatun da ta keyi d'in, baya zama acikin k'wak'walwarta.

Bisa dole haka ta rufe littafin, tare da komawa ta kwanta.

Sama da mintuna 15 kuwa tun da ta kwanta, sai juyi takeyi, saboda duk yanda taso bacci ya sake d'aukar ta abun yaci tura.

Fargaba takeji kwarai fargaban daya hana zuciyarta sukuni,  fargaban sake wayan gari da zatayi gobe, da sanin cewar saura kwanaki 5 acikin kwanaki 7 d'in da Dr. Mouhammad ya fad'a.

Tabbas tasan cewa tana fuskantar k'alubale da yawa, k'alubalen da girmansa ke shirin tarwatsa mata rayuwa.

Idanunta ta kuma lumshewa saboda tayi imani, ako da yaushe bata da wani zab'i saina Ubangiji, haka kuma bata da wani mafita sai wanda Allah ya kawo mata.

Kwanciya ta gyara akaro na barkatai, tare da soma fitar da numfashi ahankali.

Haka dai
Zuciyarta cike da zullumi bacci ya d'auketa.

*The following day*

7:30 am
Kamar koda yaushe, tsab ta gama shiryawa cikin riga da wandon uniform dinta, wanda yake d'auke da d'an madaidaicin hijabinta, da iyakarsa guiwan hannu.

Duk kuma da kasancewar uniform din white color, amma hakan bai hanashi yi mata kyau ba.

Takalminta wanda yafi kama da toms ta sanya ak'afafunta.
Tare da gyara zaman hijabin dake jikinta.
Ajiyar zuciya ta d'an sauk'e ahankali, had'i da rataya school bag dinta akan kafad'arta.

Batasan meyasa ba amma zata iya cewa, fargaban da takeji ayau din ya zama daban dana kullum, dan tun tashinta da wani irin fad'uwar gaba ta tashi.
Hakanan takejin tamkar wani abune zai faru da ita.
Wannan dalilin yasa komai nata takeyinshi asanyaye.
Har kawo yanzu da ta fito farfajiyan tsakar gidan nasu.

Moudou wacce ke zaune tana karyawa da kunu da k'osai ne ta d'ago ta kalleta, ganinta sanye da uniform da tayi ne kuma yasa ta kwab'e fuska, tare da kawar da kanta gefe.

Cikin halin ko in kula tace.

"Wato yau madai makarantar zakije, baki damu da mahaifinki dake kwance rai ahannun Allah ba, bayan kuma kinsan cewa duk kece masomin kowani lalura da zata sameshi, saboda wannan d'an iskan makarantar naki, ya ke kashe duka lokutansa yana aiki, amma bashi da lafiyanma bazaki fasa zuwa ba."

Kanta ta d'an sunkuyar, had'i da danne lips dinta na kasa, kasancewar ta d'an ji zafin kalaman Moudou'n, amma bata cikin yanayin da isashshen nutsuwa ke tare da ita, hakan yasa cikin sanyi tace.

"Nima ba ason raina zanje ba, amma muna da test idan banje ba zanyi asaran maki mai yawa, kuma....."

"Kuma me? Munafurci kawai da halla ni tafi ki bani waje, da wannan banzan makarantar, dama zuwa kikayi kika nemo kud'in da za'ayiwa mahaifin naki aiki, tunda aikinsan hanyoyin da ake samo kud'i."

Moudoun ta fad'i haka ta hanyar katseta, Daga maganan da takeyi.

Kwarai aganganun Moudoun sun daki zuciyarta, Wanda har saida hakan yasa hawaye taruwa acikin idanunta.
Saidai batare da ta barsu sun kwaranyo daga cikin idanun nata ba, ta juya ta fice daga cikin gidan.

Kamar kuwa dama jira hawayen suke ta fita daga cikin gidan, suka gangaro kan kumatunta.
Tabbas tasan awani lokacin bata iya fahimtar kalaman da Moudoun, take fad'i akanta, amma ayau  duk yanda takai ga rashin fahimta, maganganun Moudou'n na yau sun sata jin babu dadi acikin zuciyarta.

Isowarta bakin titi ne kuma yasa ta, sanya Hannu ahankali ta share hawayen nata, tare da soma kokarin tare wani mai adaidaita da. Yazo wucewa.

"Anna's Health Collage.."
Ta fad'a asanyaye tare da shiga, cikin napep din ta zauna.
Take ko mai napep din yaja suka tafi.

A hankali ta jingina kanta da jikin karfen napep din, tare da lumshe idanunta wanda sukayi ja.

"Kwanaki Biyar."

Shine abunda ta fad'a akan harshenta, tare da soma kokarin danne abubuwan dake cikin zuciyarta.

Maida idanunta tayi ta lumshe, daidai lokacin kuma suka iso kofar babban makarantar tasu, wacce motoci ke ta shiga da fice acikinta saboda kawo d'alibai.

Fitowa daga cikin napep d'in tayi, tare da mik'awa mai napep d'in, Kud'in dake hannunta, bayan ya bata canji ne kuma, ta gyara zaman school bag d'inta, tare da nufar cikin makarantar, kaitsaye.

Kamar kuma yanda abun ya zame mata al'ada, a yauma haka takejin idanuwan mutane na yawo akanta.
Saidai sab'anin yanda ta saba yin sauri idan ana kallon ta, yau ahankali take tafiyarta, ga duk wanda ya kalleta kuwa zai fahimci cewa akwai abunda yake damunta.

Tafiya mai d'an nisa tayi kafun ta iso kofar ajinsu, Wanda tuni abokan karatunta sun bayyana, saboda 8:00 am daidai za'a fara yi musu test din, kasancewar kuma lokaci ya shiga ne, yasa har malamin chemistry din nasu yazo ya basu question din da zasu amsa.

"Excuse me Sir." Isowarta bakin kofar ajin, yasa
Ta fad'i haka da raunanniyar murya.

Sautin muryar dayasa chemistry teachern dama duk sauran d'aliban ajin juyowa suka kalleta.

"What, Soumaya k'arfe nawa yanzu 80:5 am, meyasa yau kika makara?."

Chemistry teacher din ya fad'a, yana me duba agogon hannunsa.
Saboda wannan shine karo na farko da yaga Soumaya'n tazo late.

Soumaya kuwa irin kallon da yakeyi mata ne yasa ta kasa amsawa, saima sunkuyar da kanta k'asa da tayi.

Ganin hakan da yayi ne yasa shi,  d'an yin murmushi, kana cikin kulawa yace.

"Okay come in."

Yayi maganan yana me matsawa can gefe.

  Asanyaye ta shigo cikin ajin, Wanda hakan yasa duk idanun d'aliban ya zamana akanta.

Bazata iya jurewa irin yanda takejin idanuwan mutane na yawo akanta ba, hakan yasa ta zama akujerar farko dake roll din gaba.
Sab'anin permanent chair dinsu da suka saba zama ita da Noor.

Harara Noor dake can roll din tsakiya ta watsa mata, tare da cije baki, saboda haushin Soumayan bata zauna akusa da ita ba.

Soumaya kuwa koda ta zauna kasa fara rubutun test din tayi, duk da cewar wasu daga cikin question din ta san amsoshin su, amma bata da wannan nutsuwar bata da wannan daman.

Adaddafe ta iya amsa question d'aya,  Jin yanda kanta ke sarawa ne kuma yasa ta,  kife forehead dinta  akan desk, tare da lumshe idanunta wanda ayanzu cikinsu basa tab'a rabuwa da ruwan hawaye.

Daga can nesa Noor ta zubawa Soumayan idanu, domin duk a iya tsawon rayuwarsu bata tab'a ganin Soumayan tayi irin haka ba, wannan dalilin yasa duk taji jikinta yayi sanyi.

Kamar kuma yanda chemistry teacher'n ya fad'a musu, 40mn kwata kwata suke dashi danyin submit.

Wannan dalilin yasa 40mn din na cika d'aliban suka soma submitting test din.

jin anata submitting ne kuma yasa ta d'ago kanta ahankali, takardar nata ta k'urawa ido, Wanda bayan question d'ayan, da ta amsa bata sake amsa wani question d'in ba.

D'alibin da yake harhad'a kan papers dinnasu ne yazo wucewa, Wanda hakan yasa ta mik'a masa paper'n, tare da sake maida Kanta ta kifa akan desk.

Kusan mintuna 10 tana ahaka har chemistry teacher'n nasu ya fita.

"Soumaya."
Muryar Noor ta shiga cikin kunnuwanta wanda hakan yasa ta d'ago da kanta.

"Innalillahi Soumaya what's wrong with you? Are you okay?."

Noor dake tsaye ta tambaya da sauri, saboda yanda taga idanun Soumayan sunyi ja sosai.

Idanunta ta d'an janye daga kallon

You are reading the story above: TeenFic.Net