Chapter One

Background color
Font
Font size
Line height




*Bismillahirrahamanirrahim*

             *MAJNOON!!*
          (The innocentmad)

PAIDBOOK

*Writting By*
Fatymasardauna
             *Wattpad*
      @fatymasardauna

*FREE PAGE*

*18/11/2021*

                *Chapter 1*

#Firstday

*ANNA'S HEALTH COLLAGE ABUJA*

*5:00 pm*

Yamma ci ne mai dadi, haka kuma yau din rana ne da ya kasance na musamman wato Jumma'a, ranan da yake d'auke da albarka da kuma rahamar Ubangiji kala kala.

Wannan dalilin yasa sassanyar iska mai cike da tsananin dadi, da kuma sanya shauki ke busawa, a gaba daya ko wani lungu da sak'o dake cikin shahararriyar makarantar koyon likitanci, dake cikin garin Abuja wacce tayi suna sosai, kana  take kuma d'auke da yawan d'alibai maza da mata.

kamar kuma yanda d'aliban suka saba akoda yaushe, haka yau din ma takasance, domin kuwa 5 na yamma na cika, babban k'arrarawan dake sanar dasu lokacin tashi, ya soma bugawa yayinda karansa ya shiga karad'e ko Ina dake cikin makarantar. 

K'aran daya sanya da yawan d'aliban dake cikin makarantar farinciki, kasancewar abune da kowani d'alibi ya saba, cewar matuk'ar aka yi Nisan zango acikin makaranta to akwai gajiya da kuma yunwar dake damun d'alibi.

Jin k'aran k'ararrarwan tashi ne kuma,  yasa kowanne dalibi dake cikin makarantar, soma d'aukan jakunkunan su suna fitowa izuwa waje dan komawa gida.

*"SOUMAYA!"*
*"SOUMAYA!!"*

Cewar wata matashiyar budurwa dake tsaye, tana me kokarin rataya katuwar school bag din dake hannunta, Wanda kuma ahankali ta dan rank'wafo da kanta, tana me kallon wacce ke zaune agefenta.

"Soumaya wake up kodai bacci kikeyi ne?."

Matashiyar budurwar ta fad'i haka tana me gyara tsayuwanta, tare kuma dasa hannu ta dan zunguri wacce ke gefen nata, wanda kuma ita d'ince ake kira da suna.
*SOUMAYA*
(Gift of God)

Ahankali ta d'ago kanta wanda ta kifashi akan desk almost 15mn ago.
Sam ba bacci takeyi ba, hasalima duk abunda k'awar tata ke fad'a tana jinta.

Numfashi ta d'an sauke tare da d'ago manya manyan Oily eyes dinta, masu matukar kyau ta kalli abokiyar zaman nata.

Hakan da tayi dinne kuma nima ya bani daman kallon, tsananin kyawun dake kwance akan fuskar matashiyar budurwar, mai suna Soumaya.

Idanunta da suka d'anyi ja ta lumshe, tare kuma da bud'e su alokaci guda.

Cikin unique voice d'inta, mai dadin amo da sanyin sauti, tamkar ana busa sarewa tace.

"What happen NOOR (Light)? ba bacci fa na keyi ba, just I'm tired."

Ta k'are maganan tana me d'an kwantar da wuyanta gefe.

"What happening kike tambaya, time din tashi yayi, kalla class kowa ya watse sai nidake kawai, oya tashi mu tafi kodai zaman class dinne bai isheki ba?."

Waccce aka kira da suna Noor ta fad'a, tana me kokarin fita daga roll din da bencin su yake.

Fuska Soumaya ta d'an kwab'e, kana cikin yanayin gajiya, da kuma yunwar dake cinta tasa  hannu ta d'auki jakarta.
Domin kuwa zuwa lokacin har Noor ta kai kofar fita daga cikin ajin.

Wannan yasa cikin sauri ta rufa mata baya, tana me kokarin rataya jakanta bisa shoulder dinta.

Atare suka fito compound din makarantar tasu, wacce ke d'auke da tarin d'alibai.

Saidai kuma kamar yanda suka saba, kowani d'alibi harkar gabansa yakeyi, yayinda da yawan wasu  daga cikin d'aliban ke tafiya izuwa wajen motocin da suka zo d'aukarsu.

Kasancewar makarantar tasu ta masu kudi ne, shi yasa duk wani d'alibin dake cikinta to babansa wanine, kuma kowa a motar gidansu ake zuwa d'aukarsa,
sab'anin mutum d'aya wato SOUMAYA.

Yarinyar da zuciyarta ke cike da rauni, haka kuma yarinyar da k'addara da kuma k'alubalen rayuwa ke  gudana acikin jikinta kamar jini.

Har lau kamar koda yaushe anutse take tafiyanta, yayinda ta sadda kanta k'asa, saidai ahankali take matse lips dinta, da kyawawan teeth dinta.
Ahaka har suka iso babban filin parking space din dake cikin makarantar.

Isowarsu wajenne kuma yasa Noor sakin ajiyar zuciya,  saboda hango Musa driver'n gidansu da tayi.

Cikin jin dadi tace.

"Yawwa Soumaya yau musa driver yazo da wuri, kinga har ma zamu samu muyi dropping naki agida, basai kin shiga taxi dinnan da kika saba shiga ba, duk da na fahimci cewa shiga taxi din yana miki dad'i."

Noor din takai k'arshen maganan tana me juyowa, ga Soumaya wacce ke kokarin ratsa cikin motocin dake wajen ta wuce.

"Soumaya." 

Noor ta kira sunan k'awartata, tare kuma da Dan tsayawa tana kallonta.

Ganin yanda Soumaya'n ke d'an cizon lips dinta kad'an kad'an, yasa ta gyara tsayuwanta tare da cewa.

"What's wrong Soumaya, na fahimci kwana biyu duk kaman bakya jin dadi but bakyason fad'a meyasa?."

Noor din ta tambaya cike da kulawa.

Idanunta ta d'an rumtse tare da d'aura hannunta d'aya akan waist d'inta, cikin kuma nuna rashin mahimmancin abun tace.

"No Noor I'm okay fa, kawai dai kinsan period time Dina ya kusa shiyasa, kin kumasan yanda nake shan wahala."

Ta k'areshe maganan tana me d'an yayyarfa yatsun hannunta, kasancewar tana ovulation period ne, then pain din yakan taso mata time to time.

Kai Noor ta jinjina, cike kuma da tausayawa K'awartata tace.

"Eyyah sorry bestie you'll be fine insha Allah,Kizo mu saukeki agida."

Kai Soumaya ta d'an girgiza,  tare dasa hannu ta gyara zaman jakan dake shoulder dinta.
Cikin kuma yanayin nutsuwarta na koda yaushe tace.

"I'm sorry Noor karkice wani abu please, Zan fita bakin gate rana tayi sanyi nasan zan samu taxi, then nasan ma ABBOU ya kusa dawowa yanzu."

Tayi maganan tana me duba, d'an siririn wristwatch din dake d'aure ahannunta na dama.

Noor kuwa saurin juyowa tayi ta kalleta, tabbas idan da sabo yaci ace ta saba da halin Soumaya, domin bako da yaushe ne kakeyi mata tayin abu tayi accepting ba, ta sani Soumaya wata kalan mutum ce, duk da cewar ita din ba y'ar gidan masu akwai bane, amma Ware kanta gefe da takeyi abun yayi yawa.

Sanin halin Soumaya'n da tayine kuma yasa, ta b'ata fuska batare da tasake cewa komai ba, ta shige cikin motar tare da rufo murfin da k'arfi.

Idanunta ta d'an lumshe a hankali kuma sassanyan murmushi ya bayyana akan fuskarta.
Tasan cewa hakan da Noor din tayi alamane dake nuna cewar tayi fushi.

Saidai akoda yaushe bata da wani zab'in daya wuce haka.

Juyawa tayi ta nufi babban gate din fita daga makarantar,  yayinda take ta ratsa cikin manya manyan motocin d'aukan d'aliban da suketa wuce wa ta wajen.  

Tafiya takeyi amma gaba d'aya duk bata jin dad'in yanayin nata,  saboda ajikinta takejin cewa ana kallonta, duk da ta saba da hakan, amma da yawan lokuta kwata kwata batajin dadin, yanda idan ta shiga waje idanun jama'a ke yawo akan ta, domin kuwa kallon da sukeyi mata irin kallon nanne na kurulla.

Wannan dalilin yasa ta dan d'aga k'afanta, saboda batason irin kallon da mazan dake wajen keyi mata. 

Lokacin da ta tsinci kanta abakin kofar fita daga cikin makarantar kuwa, wani irin sassanyar ajiyar zuciya ta sauke, domin ko ba komai tasan ta tsira daga irin kallon da jama'a keyi mata.

Daidai fitowar nata waje ne kuma su Noor ma suka fito, harara Noor dake zaune acikin mota, b'angaren gidan baya ta watsa mata.

Wanda hakan yasa ta d'an saki murmushi, tare da had'e hannayenta waje d'aya alaman ban hakuri.

Da sauri Noor din ta kawar da kanta, tare da murgud'a mata baki,, sannan suka wuce.

Again murmushi Soumaya tayi, domin tasan halin Noor fushin nata bazai kai ko Ina ba.

Hango wani taxi da tayi yana zuwa ne kuma yasa da sauri ta soma d'aga hannu tana son tare mai taxi din.

Cikin sa'a kuwa ya tsaya, d'an saukowa tayi daga kan steps din da take, tare da lekowa ta kalla mai taxi din.

"Wuse 2."
Ta fad'a tana me sake kallon mutumin dake tuk'a taxi din.

"To yarinya zaki biya 200"
D'an dattijon Mai taxi din ya fad'a shima yana kallonta.

Kai ta jinjina batare kuma da ta nemi ya rage mata ba, ta bud'e murfin taxi din ta shiga, saboda dama ahaka ta saba kusan kullum 200 ake kawota, akuma maida ita 200.

Inda tayi sa'a kuma yau din babu kowa acikin taxi din, wannan dalilin yasa ta shiga da confidence dinta, domin dama batason shiga abun hawan da akwai mutane da yawa acikinsa.

Bayan ta rufe murfin motar ne kuma,  mai taxi din yaja sukayi gaba.

Hawa titin da taji sunyi ne kuma yasa ta, zare jakanta dake kan kafadarta,   tare da zuge zip din jakar.
Tsohuwar naira 500 din dake cikin jakan nata tasa hannu ta ciro tare da damk'e ta acikin tafin hannunta k'am, tana me tuno lokacin da Abboun ya biyota waje ya bata.

Hawayen da suka taru acikin idanunta ta share,  tare da d'an kifa kanta akan jakanta, tana me tuno mahaifin da yafi mata kowa da komai.
Wani irin so takeyi masa na musamman, son da yake tafiya da tausayi mai tsanani,  bata da kowa aduniyar nan daya wuce mata shi,  shine komai nata Garkuwanta haka kuma farinciki agareta.

Sake dunk'ule kud'in dake cikin hannun nata tayi,  a hankali kuma ta jingina bayanta da jikin kujeran motar.

*"INASONKA ABBOU NA"*

Ta fad'i hakan acikin zuciyarta, tana mejin tsananin shaukin son mahaifin nata na ratsata.
Uban da takejin babu irinsa aduniya, Uban da take fatan faranta masa akoda  yaushe, 
Uban da yake matukar son farincikinta fiye da kowa.

Babu wani wanda zata so sama dashi aduniya.

Soumaya kenan innocent girl din da batasan komai ba, sama da soyayyar mahaifinta, yarinyar da babu kunci ko matsanancin damuwa  acikin rayuwarta.
Ayanzu farinciki kawai tasani, duk da cewar suna rayuwa irin ta masu k'ananan k'arfi, amma kwata kwata hakan bai kawo mata nakasu acikin rayuwarta ba.

Batasan yawan tunani ko kuncin zuciya ba.

Haka kuma daskararriyar K'addarar dake kwance acikin jininta bata fara motsawa ba.

Hakika akoda yaushe rayuwa tana tafiya da k'alubale.
Haka kuma kowa da irin k'addararsa, amma nata K'addarar B'oyayye ne, kowa da irin na k'asunsa amma nata nak'asun mai tsananin RAUNI ne.

Kamar kuma yanda yake a bayan kowani bakinciki akwai farinciki, haka kuma a bayan kowani kunci akwai sassauci.

Rayuwa mai juyawa ce farinciki ko akasin haka, mummunan k'addara ko zazzafar Soyayya, wannene zaiyi tasiri acikin rayuwar yarinyar da zuciyarta ke cike da buri da kuma fatan tallafawa mahaifinta, yarinyar da batasan komai ba sai Soyayyar mahaifinta? Tayaya zuciyar yarinyar dake da Rauni zai iya jurewa k'arb'an k'addarori Biyu alokaci guda? Meye zaiyi mata shamaki da nutsuwar zuciyarta?
Yaushe ne kuma zata san kanta?

Kiiiiiiiiii!!!

Haka Drivern taxi din yaja burki, saboda wata mota mai azaban gudu da tazo ta gilma ta gabansu.

Wanda K'aran taka burkin nasa ne kuma yasa ta  bud'e idanunta, masu cike da gajiya, bugu da K'ari ga kuma yunwar dake tsakalan cikinta.

"Yauwa mun iso anan zan sauk'a."

Ta fad'a tana me kallon cikin unguwar tasu, wacce take d'auke da yalwatattun gidajen masu kudi.
Lokaci guda kuma  ta juyo da kallonta ga mai taxi din, inda ta Mika masa naira d'ari biyar din dake hannunta.

Bayan ya bata canji ne kuma ta bud'e murfin motar ta fito, hannunta rik'e da jakan makarantar ta.

K'ofar gidan dake facing dinta ta zubawa ido, Wanda kuma ya kasance nanne gidansu.
zuciyarta cike da fatan samun mahaifin nata, haka ta nufi gidan dake d'an gefe.

Gidan da aduk layin shine k'arami kuma na mararrsa k'arfi, duk da cewar gida ne na rufin asiri, amma kuma idan aka had'ashi da sauran gidajen dake cikin Unguwar shi ba komai bane.

A hankali ta tura kofar gidan nasu ta shiga, bakinta d'auke da sallama.

"Assalamou Alaekoum!"

Ta fad'a cikin nutsuwar daya zame mata sabo, duk da cewar tasan ba lallaine a amsa mata ba.

Kamar kuwa yanda tayi hasashe hakanne ya kasance, domin babu kowa a tsakar gidan nasu, sai kuliyarta dake ta yawo tana shawagi, ak'asan bishiyan fruit din dake tsakiyar gidan.

"My Cutie."

Ta fad'a tana me k'arasa shigowa cikin gidan, tare dasa hannu ta shafa kan kuliyar nata.

"Sai yanzu aka tashi daga makarantar?"

Sautin murya ta fito daga bayanta, Wanda hakan yasa ta saurin juyowa, inda ta sauke idanunta akan wata matsakaiciyar bafulatanan mata, wacce take rike da buta ahannunta, da alama fitowarta daga public toilet din dake tsakar gidan kenan.

"Moudou sannu da gida."

Soumaya ta fad'a tana me sunkuyar da kanta k'asa, saboda sanin halin Moudou din da tayi.

Moudou kuwa fuska ta d'an ya mutsa, kana cikin halin ko in kula tace.

"Yauwa."

Daga haka kuwa bata sake cewa komai ba ta wuce, izuwa d'akinta wanda sautin tv keta b'ab'atu.

Da idanu Soumaya ta bita, ganin da tayi ta shiga d'aki ne kuma yasa ta sauk'e ajiyar zuciya.
Tare da sunkuyawa ta d'au cutie dinta, kaitsaye wani d'aki dake can gefe ta nufa, Wanda da alama kuma nannne d'akin daya kasance mallakinta.

Anutse ta tura kofar dakin ta shiga.

Madaidaicin d'aki ne da yake dauke da katifar kwanciya, sai kuma madaidaicin drawer Wanda kayanta ke ciki, baya ga carpet din dake shumfud'e akasan tiles din dake cikin d'akin kuwa, babu komai sai fanka dake ta faman aiki ita kad'ai.

Jakar dake hannunta ta ajiye, tare dasa hannu ta zare Hijab din dake jikinta.

Wani irin azababben yunwa takeji, wannan dalilin yasa batare da ta tsaya cire uniform din nata ba, ta fito daga cikin dakin nata, kaitsaye ta nufi kitchine dinsu, dan nemawa cikinta abunda zata ci.

K'ofar gidan nasu aka turo ahankali,  tare dayin sallama da wata irin sark'akk'iya muryar, dake bayyana pain din wanda yayita.

Kyakkyawan farin dattijon da ak'alla bazai haurawa 50 years bane ya shigo, cikin gidan hannunsa rike da bakin leda.
Yayinda d'ayan hannun nasa kuwa ke dafe da kansa, ya rumtse idanunsa wanda yakejin tamkar zasu zazzago k'asa.

"Innalillahi!
Hasbunallahu wani'imal wakeel!!!"

Shine abunda Kyakkyawan matashin dattijon ke fad'a,  da muryarsa wacce ke rawa, yayinda kuma yake tsaye cak ya kasa motsa koda y'ar yatsar k'afarsa ne.
Saima wani irin numfashi mai kama da fusga da yake fitarwa.
Kasancewar da k'yar ya iya kawo kansa gidan, domin ayanzu ko ganin gabansa bayayi, saima wani irin duhun da yake gani ya rufe masa ido.

Daidai lokacin kuwa Soumaya dake cikin kitchine ta fito, hannunta d'auke da plate din shinkafa da wake.

Fitowar nata kuma yayi daidai da sakin nishi, da kuma fitan sautin gurnanin numfashin mutumin nan dake tsaye abakin kofa.

Jin sautin fusgar numfashin mutumin ne yasa, Soumaya dake tsaye saurin juyowa.
Take kuwa ta sauke idanunta akansa.

"ABBOU!!!"

Ta fad'a da k'arfi, lokaci daya kuma Idanunta suka zazzaro waje.

"ABBOU!!!"
Tasake fada cikin yanayin kid'ima da rudewa, tare kuma da tsananin tashin hankalin daya bayyana akan fuskarta, ahanzarce batare kuma da ta jirayi komai ba ta nufi inda Abboun ke tsaye.

Saidai kafun tayi taku biyu wanda zasu sada ta garesa.
Tuni ya saki ledan dake hannunsa, take kuma ya zube awajen hannunsa dafe da kansa.

Wani irin k'ara Soumaya ta sa, Wanda har hakan yajawo fad'uwar plate din dake hannunta.

Take kuma itama ta yanki jiki ta fad'i akan guiwowinta.

*Wannan shine Farkon fara bugun zuciyarta, haka kuma farkon fara kukanta, kukan da babu mai rarrashi.*

Hak'ik'a wannan ne K'addararta, k'addarar dake janta izuwa bak'uwar rayuwa.


MAJNOON bakamar yanda kuke tunani bane, ba kuma irin yanda kuke hasashe bane.
MAJNOON acikinsa wani  soyayyane mai tsananin zafi.

Meye zai faru? Meye kuma zai rinjayi Zuciyoyi biyun, dake bugawa alokaci guda batare da sunsan da juna ba?.



*6:40pm*

You are reading the story above: TeenFic.Net