Chapter Nine

Background color
Font
Font size
Line height


*MAJNOON!!*
(The innocentmad)

*Writting By*
Fatymasardauna
*Wattpad*
@fatymasardauna

*(This book is mainly for those that pay, If you know you didn't pay please don't read it. Here is the Account Number for people that are willing to pay-0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz Bank. AMOUNT 300, WhatsApp Number 07069917168)*


*CHAPTER 9*

*FREEPAGE*

Gaba d'aya duk jikinta rawa yake, yayinda wani irin kuka ke kokarin k'wace mata, Wanda yake tasowa tun daga k'ar k'ashin k'asan zuciyarta.

Wanda hakan kuma shiya sanya numfashinta seizing tamkar wanda zai bar gangar jikinta.

Idanu Dr. Mouhammad ya zuba mata, cike da tsananin tausayinta, domin tabbas ya hangi tsananin damuwa had'i da kuma d'imuwa akan fuskarta.

Allah ya sani basuyi hakan dan cutar da rayuwar Innocent girl kamanta ba, saidai dan cimma wani manufa da kuma burin da ke yawo acikin zuk'atansu a kowacce rana.
Burin da suke fatan cikarsa, burin dason cikarsa ke hanasu bacci.
Tsawon shekaru biyu, da tabo ke yawo acikin zuk'atansu.

Yayinda daga wani sashi na zuciyarsa kuwa yayi farinciki k'warai, da amincewar nata, wanda hakan yasa shi sakin ajiyar zuciya.

"Soumaya!"
Ya kira sunanta, atausashe kana cikin lallashi da kuma din nuna mata cewa, K'addara babu ta yanda bata zuwa wa bawa.

"Soumaya!"
Ya sake kiran sunanta akaro na biyu.
Saboda ganin da yayi bata amsa shi ba.

Saidai kuma ayanzun ma still bata amsa shiba, sannan bata d'ago kanta ta kalleshi ba, hasalima idanuwanta har yanzu a rumtse suke.

Ajikinta kuwa Babu wani abu da yake motsi, face zuciyarta dake bugawa da wani irin k'arfi tamkar zata faso k'irjinta ta fito.

Kwata kwata ta kasa gane komai, kamar yanda brain dinta ta daina fahimtar komai ayanzu, duk wani tunanin ta ya tsaya cak.
So takeyi ta saki kukan da k'arfinsa ke neman zautar da ita amma ta kasa.

So takeyi tayi kukan da kowa zai jita, duk da tasan babu me iya rarrashinta.

Amma ta kasa saboda wani irin juyawa da kanta keyi.

Daidai lokacin aka turo k'ofar Office din Dr. Mouhammad din, Wanda hakan yasa Dr. Mouhammad dake tsaye maida kallonsa ga k'ofar.

Wata nurses ce ta shigo ad'an har gitse, cikin gaggawa tace.

"Please Sir we need to help, ankawo emergency patient ICU, he's unconscious."

Numfashi Dr. Mouhammad din ya fesar, kana cikin gaggawa yace.
"Okay I'm coming."

Ya k'are maganan yana me tura takardar yar jejeniyar dake hannunsa cikin aljihu, kana cikin sauri ya juya ya fice daga cikin Office din.

Motsin fita da kuma sautin rufe k'ofar office d'in nasa da yayi ne, yasa ta bud'e lumsassun idanunta ahankali.

Kamar kuwa dama jira hawayen dake cike acikin idanun nata suke, tana bud'e su suka soma gangarowa tamkar an kunna famfo.

Yayinda har yanzu tunanin ta bai gama dawowa cikin jikinta ba.
Kamar yanda zuciyarta ta kasa tsaida tsanin bugun da takeyi.
Wani abu da takejin ya tokare kirjinta, kuwa shi ya kasa bari ta fitar da numfashi cikin salama.

K'ok'arin aro duk wani jarumta da juriya take, ta hanyar mik'ewa ta tsaya akan k'afafunta, duk da irin jirin da taji yana neman kada ita, amma haka ta jajircewa tsayuwan, tare da soma taka k'afafunta ahankali, har ta isa bakin k'ofar fita daga cikin office din.
Handle din k'ofar ta murd'a tare da tura kofan gaba, Wanda hakan yasa k'ofar bud'ewa, inda kaitsaye ta fice daga cikin office din.

Tafiya takeyi anan cikin d'an dogon corridor din dake gaban office din, tafiya irin na way'anda basa cikin hayyaci da tunaninsu.
Zuciyarta tayi rauni, tunanin ta ya gushe, haka kuma farinciki yayi k'aura daga cikin y'ar k'aramar zuciyar da batasan menene rayuwa ba.

Akaro na biyu kenan yanzun da bata sanin inda take jefa k'afafunta, kamar yanda batasan Ina ta nufa, acikin tafiyan nata da takeyi ba.

"Soumaya!"
Muryar Malam Musbahu ya karad'e gurin, Wanda ganin shiru shiru ya sashi biyo ta dan ganin ko lafiya.
Ganin tana ta tafiya gaba gad'ine kuma, yasa shi k'iran sunanta, cike da mamakin yanda yaga rashin nutsuwa atattare da ita.

K'iran sunan nata da yayi kuma Tabbas shi ya sata tsayawa cak, tare da juyowa ta zuba masa idanunta.

Hak'ik'a sunan nata daya kira yayi sanadiyar dawo da ita cikin hayyacinta, Wanda har hakan yasa ahankali ta soma takowa zuwa gareshi.

"Soumaya lafiyanki k'alau kuwa, daga ina kike? ina kuma zakije naga kin nufi wata hanyar daban?"

Malam Musbah'un ya tambaya yana me saurin k'arasowa inda take.
Tare da saurin kamo hannunta, saboda ganin yanda take ta layi, tamkar zata fad'i.

"Soumaya! Soumaya!!"

Ya sake kiran sunanta saboda ganin da yayi ta tafi luuuu Kamar zata fad'i.

Cikin kukan dake neman fin k'arfinta, ta fad'i a k'asa tare da zubewa akan guiwowinta, ad'imauce ta saki kuka, tare da kama hannayenta ta had'esu awaje d'aya.

Kuka take mai tsananin tab'a zuciya, kukan dake bayyana abun dake cikin zuciyarta.

Kukan daya sanya duka jikinta soma kakkarwa, har yakai ga ta soma shid'ewa, yayinda numfashinta ya shiga fusga da k'arfi.

Sosai kukan nata ya bawa Malam Musbahu tsoro, Wanda hakan yasa cikin fargaba yace.

"Soumaya lafiya kike kuwa? Ki fad'amin meya faru kike wannan kukan?."

Kanta ta shiga girgizawa, cikin azababben kukan da takasa controlling d'insa, murya na shaking, kamar yanda ke tsuma tace.

"Najefa rayuwa ta acikin had'ari, da kuma k'addarar da bansan yaushe ne ranar k'arewarsa ba, Baffa mutuwa zanyi idan k'addarar tayi min tsauri, na amince da buk'atar da ko amafarki ban tab'a tunanin makamancinsa zai shigo rayuwata ba, natsaida duka fatana, Na'amince Baffa na'amince..."

Ta k'are maganan cikin matsanancin ciwo, k'unci had'i da damuwar dake barazanar d'aid'aita tunanin ta, kana cikin matsanancin kukan da takeyi, Ta kifa kanta ajikin wani d'an benci dake kusa da ita, babu abunda ke tashi awajen kuwa face sautin kukanta dake amsa amo tamkar zai fasa kunnuwa.

Idanu Baffa dake tsaye ya zuba mata, yayinda duk kalamanta ke dawowa cikin kansa filla filla.
Fahimtar abunda ta amincewar ne kuma yasa shi, Jin zuciyarsa ta buga take ko yaji wani irin gumi ya keto masa.

Da sauri cikin tashin hankali yace.

"Soumaya ki dawo cikin hayyacinki, meyasa haka meyasa kika yanke wannan d'anyen hukuncin batare da nasani ba? Me zamu sanarwa Abbounki aduk sanda ya bud'e idanunsa? Ba kisan Aure ba Soumaya, bakisan ya zaman cikinsa yake ba, wai shinma kinsan cewar MAJNOON me yake nufi? MAHAUKACI fa Soumaya, zama da mahaukaci, ba irin zama da mutane wanda kika sani bane, domin wani mahaukacin tamkar guba ne acikin abinci."

Idanuwanta ta rumtse da k'arfi tare dasa hannu ta dafe k'irjinta, daidai saitin zuciyarta da ta tsananta bugawa, saboda sunan MAJNOON da taji Baffan ya ambata.
Sunan dake tarwatsa tunani da kuzarin ta, then sunan da takejinsa na yawo acikin kowanni kofar magudanan jini dake jikinta.

Hakan yasa ta Jan wani irin dogon numfashi.

yayinda Malam Musbahu kuwa ya ciga ba da cewa.

"Me yasa zaki amince da hakan Soumaya, bayan kinsan cewa har yanzu muna da sauran kwanaki 5 wanda suka rage, da munyi hakuri watakila Allah ya kawo mana wata mafitar."

"Bani da zab'i akan hakan Baffa, bani da zab'i, Zanen K'addara koda yaushe tana yawo ne acikin jini, bani da zab'i akan k'addarata, yau kwanaki 5 ne kawai suka rage, idan aka kai Gobe kuma ya zama 4, yaya zanyi Baffa? Ta Ina zan fara? bani da wani zab'in daya wuce mik'a wuya, koda zan fuskanci k'alubale mai tarin yawa, bazan bari na Rasa Abbouna ba, bazan bari ba."

Ta k'are maganan tana me jujjuya kanta, kana Kuma cikin matsanancin kukan da har yanzu takeyinsa tamkar ranta zai fita.

Wannan dalilin yasa Baffan yin shiru, tare da rumtse idanunsa saboda babban k'alubale da yasan zata fuskanta.
Rayuwace me juyawa da yanayi daban daban.
K'addara kuwa itace me afkuwa aduk sanda lokacin ta ya tsaya.

Tabbas sautin kukan Soumayan yana tab'a masa zuciya K'warai, Wanda hakan yasa asanyaye Kuma cikin matsanancin tausayinta da yakeji yace.

"Taso muje Soumaya, kukan ya isa haka kada ki sawa kanki wani ciwon, acikin kwanaki biyunnan kinyi kuka sosai, ya isa haka kukan taso muje, Allah bazai tab'a barinki haka ba, Kamar yanda da taimakonsa ne likitoti, suka sake samun daman ceto numfashinsa a karo na biyu."

Baffan ya kare maganan cike da lallashi, tare da sanya hannu ya kamo hannun Soumayan dake zaune, duk da cewar shima zuciyarsa ta Karye, amma yasan cewa Soumaya'n tana buk'atar mai lallashinta ayau.

Ahaka ta mike tsaye, yayinda takejin kanta yayi mata wani irin nauyi, ga kuma idanunta wanda suka k'ank'ance kana sukayi luhu luhu dasu, har saida fatan samansu suka kumburo, kasancewarta farar fata Kuma, yasa lokaci d'aya fuskarta tayi jajur, tamkar anshafa mata jan borkono.

Tafiya takeyi batare da tasan inda suka nufa ba.

badan Baffan dake rike da hannunta ba kuwa da tuni ta yanki jiki ta fad'i, saboda jiri had'i da ciwon kan da suke damunta.

Isowarsu bakin kofar dakin da Abboun ke ciki ne kuma, yasa Malam Musbahu sanya hannu ya tura kofar, hade da Jan Soumayan suka shiga ciki.

Wanda sai alokacin ta sake Ware kumburarrun idanunta, inda ta sauk'esu akan mahaifinnata dake kwance.

Ahankali ta soma tafiya har ta k'arasa inda yake kwance, idanunta da ke ganin dishi dishi ta zuba masa tare da zamewa ta zube akan guiwowinta, fuskarsa take kallo cike da tsananin sonsa, da kuma tunanin yanda zatayi kewarsa aduk tsawon rayuwarta.

"Inasonka Abbou!"

Ta fad'a ad'an hard'e saboda kukan dake son dawo mata, Wanda hakan yasa ta kifa kanta akan shoulder din mafaifin nata, tare da kifa hannunta ak'irjinsa, daidai saitin zuciyarsa.

Kuka takeson yi irin na wanda ke cikin maraici, haka kuma kuka irin na wanda ke buk'atar taimako ko kuma ya rasa duk wani hope d'insa.

So takeyi ta furta duk wani cutar dake kwance acikin zuciyarta garesa, so takeyi yaji sautin kukan nata, akaro na farko na rayuwarta da ta fara jin zafin rashin uwa.

Sake cusa kanta acikin kafad'an nasa tayi, tare da sak'ala hannunta ta rungumesa.

Cikin yanayin kasa control din kai, da kuma shaking voice tace.

"Kayi hakuri Abbou, nasan bazakayi farinciki da hakan ba , amma I'm so sorry, idan ka tashi ka dakeni ko ka mareni ma, idan kanaso ma kayi min fad'a, amma nidai fatana shine ka rayu akusa dani, kayi alk'awarin zama atare dani, amma yanzu komai babu dadi, Please Abbou koda sau d'aya ka bud'e idanunka, duk da nasan cewa koba yanzu ba zakajini watarana, Abbouna zuciyata bugawa take, fargaba da tsoro sunyi tasiri acikin rayuwata, bansan zan iya samun kaina acikin wannan k'addarar ba, nayi maka laifi, nayi maka laifin amincewa da Auren MAJNOON, I'm so sorry Abbou......"

Ta Kasa k'arasa maganan nata saboda yankewa da muryar nata keyi, dalilin fitinannen kukan da takeyi kamar ranta zai fita.
Wannan dalilin yasa ta sake shigewa jikin Abboun, tare da boye kanta acikin shoulder dinsa tana kuka.

Kukan da sautinsa ya cika ko Ina, yayinda kalaman da suka fito daga bakinta kuwa, suka sanya Malam Musbahu dake tsaye zubar da hawaye.

Kwarai yasan so da kuma shak'uwar dake tsakanin Soumayan da Abbounta, Wanda hakan kesa zuciyarsa sake raunana akoda yaushe.

Yayinda kuma yasan cewa abakinsa babu wata kalman rarrashi, da zai fad'eta ga Soumaya'n, hakan yasa shi zama tare da soma share hawayen dake idanunsa.

Soumaya kuwa sama da tsawon mintuna 20 ta d'auka tana kukan, kafun daga bisani ahankali sautin kukan nata ya soma raguwa, kamar yanda dare ke sake nisawa.

Sannu ahankali kuma wani irin zazzafan zazzab'i yayi mata dirar mikiya, wanda har hakan yasa ta duk'unk'une jikinta waje d'aya.
Tare da zame kanta ajikin Abboun ta cusa shi a tsakankanin cinyoyinta.

Jin lafawar sautin kukan nata ne kuma, yasa Baffa sauke ajiyar zuciya, tare da d'aga kansa ya kalli agogon dake cikin d'akin.

Murya atausashe yace

"Soumaya ya kamata ki tafi gida, dare na k'arayi dan wajajen k'arfe goma yanzu ake nema, muje natara miki abun hawa idan yaso gobe da safe sai Kizo kafun ki wuce makaranta."

Baffan ya fad'a yana me mik'ewa tsaye.

Kanta ta d'an girgiza kana ahankali tace.

"Zan zauna tare da Abbaouna, dan Allah Baffa karkace a'a, watakila wannan shine damana kawai, damana na k'arshe...."

Ta k'are maganan da raunanniyar murya, tare da d'ago jajayen idanunta ta kalli Baffan.

Wanda hakan yasa shi jin jikinsa yayi sanyi, sosai yakejin tausayinta musamman ayanzu, da rayuwarta take shirin fuskantan, k'alubale da kuma k'addara mabanbanta.

Ajiyar zuciya ya sauk'e, cikin kuma gamsuwa da barin ta, akusa da mahaifin nata yace.

"Shikenan Soumaya yau tunda zaki kwana, ni bari na tafi gida, amma ki kula da kanki kinji, dan Allah ki rage yawan wannan kukan, ki sani babu wani tsanani da baya tafiya da sauk'i, haka kuma babu wani k'addara da zata zo, face anrubutata tuntuni acikin rayuwar mutum, idan dan rashin lafiyar Abbounki ne kisa aranki cewar zai samu lafiya kinji?."

Kai ta jinjina masa, tare da maida Kanta ta kwantar ahankali.

Shi kuwa Malam Musbahu'n, y'an abubuwan da yasan zai buk'ata ya d'auka, kana kaitsaye ya fice daga cikin d'akin.

Bayansa Soumayan tabi da idanu, yayinda acikin zuciyarta take fatan, ganin Abbounta nata ya tashi yayi rayuwa kamar Baffan watarana.

Siraran hawaye masu zafi ne suka kwaranyo daga cikin, Kumburarrun idanunta wanda hakan yasa ta lumshe su.

Tare da maida bayanta ta jingina da jikin bango.

Hak'ik'a K'addarace take gudana acikin jikinta tamkar jini, k'addarar Auren MAJNOON, Tayaya zata rayu da wani wanda bata sani ba? wanin ma kuma mahaukaci, wayeshi? a ina yake? Duk bata sani ba.

Lokaci daya taji sabon kuka na shirin k'wace mata, Wanda ita kanta tasan cewar, zuwa yanzu idanunta sun gaji da fitar da hawaye daga cikinsu.

Jin da tayi kanta na sarawa ne kuma, yasa ahankali ta sulale tare da kwanciya ak'asa, kana ta duk'unk'une jikinta waje d'aya.

Kasancewar kuma tana d'auke da Zazzafan zazzab'i, ajikinta ne yasa tana kwanciya, mintuna 15 kacal tayi, wani wahalallen bacci ya d'auketa.

12:00 am

Numfashi take fitarwa da sauri sauri, yayinda sautin amon bugun zuciyarta ke komawa cikin kunnuwanta, duk yanda jikinta yakai ga karkarwa kuwa ta kasa bud'e idanunta, Wanda ta rumtse su k'am.

"MAJNOON!!."
Shine sunan da takeji yana yawo acikin kanta, yayinda lumsassun idanunta kuwa, ke gane mata abubuwa mabanbanta dake wanzuwa acikinsu.

Duk da sanyin A/C'n dake cikin d'akin kuma ita gumi take had'awa, yayinda jikinta keta kakkarwa tamkar wacce aka watsawa ruwan sanyi.

Sautin gurnanin da k'arfinsa ke neman toshe kunnuwanta, ne yasa ta saurin bud'e idanunta, tare da tashi azabure ta dafe daidai saitin zuciyarta.

"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!!"

Ta fad'a cikin kid'ima had'i da gigicewa, yayinda lokaci d'aya mafarki, mai kama da zahiriyyan da tayi, ya shiga dawo mata filla filla.

Kanta ta d'an soma girgizawa da sauri, tare da maida kallonta ga tafukan hannayenta, Wanda suka jik'e jagab da gumi.

Tsurawa tafukan hannayen nata idanu tayi, tamkar wacce takeson gano wani abu ajikinsu.

Har tsawon wasu y'an mintunoni kafun ta janye idanunta, inda ta maida kallonta ga Abboun dake kwance kamar gawa.

Banda sautin k'aran na'urorin dake jikinsa kuwa, babu wani abu dake tashi acikin d'akin.

Araunace take kallon yanda numfashin mahaifin nata ke tafiya, ta cikin wani d'an abu me kaman computer, Wanda yake nuna layin green and red.
Idanu ta tsurawa layuka biyun, zuciyarta cike da fargaban, watarana randa layukan zasu tsaya su daina motsawa , watarana randa numfashi bazai sake fita daga jikin Abboun nata ba har abada, ranan da zatayi kuka irin na zautattu, ranan da farinciki zai bar rayuwarta bari na har abada, tabbas bata fatan zuwan wannan ranan.

Bayan hannunta tasa ahankali ta goge kwallan daya cika mata ido.

Jin da tayi kanta na ci gaba da sarawa ne kuma, yasa
Asanyaye ta koma ta kwanta, tare da sake duk'unk'une jikinta waje d'aya.

Saidai kuma ayanzun ta kwanta ne kawai, badan wai akwai d'igo d'aya na bacci acikin idanunta ba.

Domin hakika abubuwan da suke cikin rai da zuciyarta, sun isa hanata bacci.

Wannan dalilin yasa ta kwanta lub, tana me sauraran adadin yawan bugun zuciyarta.
Bugun zuciyar da ako wani minute yake shigar da sabon abu agareta.

Ahaka dai ta kwashe awanni masu yawa, batare da bacci ya d'auketa ba.

Kamar kuwa yanda taga rana haka taga Daren yau din.
Kwata kwata bacci ya kasa zuwar mata.

Kamar yanda yake ab'angarenta, hakanne ya kasance a b'angaren mutane biyu.

Wato Dr. Mouhammad da kuma Malam Musbahu.

Yayinda Dr. Mouhammad ya b'ata dare yana shirya kud'ad'en da sukayi alk'awarin bata acikin takardar yar jejeniyar tasu.

Saidai duk yanda yaso samun farinciki ya Gaza, abubuwa da yawa ke yawo acikin tunaninsa, na farko shinen tunanin tauye hakkin yarinya da sukayi, sai kuma matsalar MAJEED.
Wanda akullum k'ara girma ta keyi, kamar dai yau, da abubuwa da yawa suka faru, Wanda azahirance koson tunasu bayayi.

Yakanji k'una alokacin da yaji kururuwa da kuma ihun MAJEED d'in.

Kalma d'aya kuma tak data kasa daina yi masa yawo acikin kwakwalwarsa, itace kalmar MAJNOON!
Kalma mafi tsananin munin tab'o, wacce take yawo acikin rayuwar MAJEED.

Ajiyar zuciya ya d'an sauk'e akaro na barkatai, yayinda maganganun da sukayi da Billionaire Dawoud Saraki, ke dawo masa, duk da yasan buk'atar Billionaire Dawoud din yayi kusa, amma zai jarraba, kasancewar hakan ma na d'aya daga cikin yarjejeniyar tasu.

Acan b'angaren Malam Musbahu kuwa, bacci yaki d'aukarsa ne, saboda tunanin halin canjin rayuwa da Soumaya zata fuskanta, kasancewar shi kansa baisan wani MAJNOON ne Soumayan zata aura ba, yasani kuma k'warai matuk'ar Abboun ya bud'e idanunsa, bazai tab'a yafe abubuwan da kunnuwansa zasu jiye masa ba.
Saidai basu da zab'in daya wuce haka, domin ya tabbata, bayan wannan hanyar basu da halin, biyan mak'udan kud'ad'en da ake buk'ata.
Amma k'warai yasan tauye hakki ne, saka mai hankali zama da mahaukaci, musamman ga Soumaya wacce take da k'arancin shekaru da Kuma raunanniyar zuciya.

Haka dai kowa daga cikinsu ya raya daren na yau da tunani kala kala acikin zuciyarsa.

*Washegari.*

5:30 am

Alokacin da kowa ke k'ok'arin bud'e nasa idanun, ita alokacin take kulle nata, saboda kwana da tayi batayi bacci ba.

Cikin sa'a kuma bacci me nauyi ne ya d'auketa, Wanda har gari ya gama yin haske batare da ta farka ba.

Malam Musbahu wanda ya kwana da damuwa acikin ransa, sammakon zuwa asibitin yayi, saidai tarar da Soumayan da yayi na bacci ne, yasa shi jin d'an nutsuwar zuciya, duk da yanayinta ya nuna cewar kwana tayi batayi bacci ba, kasancewar duk fuskarta ya kumbura.

Ganin da yayi tana baccin ne kuma yasa shi, fita waje dan dayawan lokuta yafi jin dadin zama awajen yana ganin masu shiga da fice.

9:00 am.

Ahankali take bud'e idanunta wanda sukayi nauyi, had'i da kumbura, tamkar wacce ta kwana ta wuni kuka.

Bud'e idanun nata kuwa da tayi, yayi daidai da shigowar Malam Musbahu, Wanda hakan yasa ta tashi ta zauna.
Tare da kafesa da idanu, saboda ganinsa da tayi da wata k'atuwar jaka.

"Baffa!"
Ta kira sunansa asanyaye, tare da d'an karyar da wuyanta gefe.

"Na'am Soumayan kin tashi?"

Baffan ya amsa yana me karasa shigowa cikin dakin, tare da ajiye jakan wanda yake rike da ita , tare da neman waje ya zauna.

"Ina kwana." Soumayan

You are reading the story above: TeenFic.Net