Chapter fourteen

Background color
Font
Font size
Line height

*MAJNOON!!*
(The innocentmad)

*Paidbook*

*Chapter 14*

Sake rumtse idanunta tayi had'e dasa Hannayenta ahankali ta dafe kanta, da takejin nayi mata wani irin sarawa.
zuciyarta kuwa bugu take kamar zata tarwatse.

Hak'ik'a wani abu Brain dinta keson tuno mata, wanda yasa duk ta birkice haka, wani abu dake gudana acikin jininta tsawon shekaru.
Abun dake neman wargaza duk wani tsarin tunaninta.
Duk jikinta tsuma yake kamar yanda labb'an bakinta ke rawa
Lallai tana son tuna wani abu dake k'wance ak'asar zuciyarta.
Saidai duk yanda taso ga yin hakan abun yaci tura, saboda wani irin beating zuciyarta keyi da k'arfi, yayinda daga gefe guda kuwa kanta ne ke ci gaba da sarawa, haka takejin kamar ana kwad'a mata guduma.

"Soumaya."
Billionaire Dawoud ya k'ira sunanta, cikin tausasa murya saboda ganin yanda jikinta ke b'ari ga kuma yanayin tsoro da ya bayyana atattare da ita.

Sauk'an sautin amon muryarsa acikin kunnuwan nata da taji, yasa ahankali ta bud'e lumsassun idanun nata, wanda tuntuni sukayi luhu luhu kana kuma suka k'ank'ance, saboda kukan da ta yawaita yi acikin kwanakin yasa idanun nata yin ja tamkar wacce aka watsawa garin barkono acikinsu.

Sam bata yarda da sauk'e idanunta akansa ba.
Saboda yanda takejin duk wata tsikar jikinta na mimmik'ewa, dalilin kallon cikin idanun nasa da tayi akaro na biyu.
wanda hakan yasa takejin kirjinta na bugawa, saboda idanunsa da takeji akanta.
Hakan yasa duk yanda taso samun nutsuwa abun yaci tura.

Wannan dalilin yasa acikin mintunan da basu wuce 5 ba, taji wani sabon zazzab'i na mamaye duk kan ilahirin jikinta.
Yayinda wani irin abu mai kama da fargaba ke sake danne duk wani k'warin guiwarta.
Wanda har hakan yasa ta kasa d'agowa ta kalli Billionaire Dawoud din.

Billionaire Dawoud kuwa, kallon Dr. Mouhammad dake zaune yayi, kasancewar kuma sun had'a idanune yasa shi yi masa alama akan ya basu waje.

Ajiyar zuciya Dr. Mouhammad ya sauk'e, tare da mik'ewa cikin nutsuwa ya juya ya fice daga cikin library'n, hannunsa rik'e da y'ar k'aramar jakar likitoti.

Ganin fitan nasa ne kuma yasa Billionaire Dawoud sauk'e ajiyar zuciya, tare da maida kallonsa ga Majeed din dake zaune, ya kawar da kansa izuwa wani waje na daban, idanunsa kuwa alumshe suke, ahankali kuma yake saka white teeth d'insa yana me matse jajayen lips d'insa.

Kaitsaye idan ka kalleshi ahaka bazakayi masa kallon MAJNOON ba, domin babu wani abu na hauka daya bayyana atttare dashi, duk da yabar dogon gashi akansa wanda saboda tsawo yake rufe fuskarsa.

Ajiyar zuciya Billionaire Dawoud ya sauk'e akaro na barkatai, tare da d'aura idanunsa akan hannun Majeed din wanda suke d'auke da zanen tattoo, wanda duk ya k'akkarcesu da yak'ushinsa irin na zautattu.

Wasu irin hawayene suka taru acikin idanunsa, Wanda hakan yasa muryarsa raunana, gami da bayyana tsananin damuwan dake cikin zuciyarsa.

Asanyaye murya na shaking yace.

"Tabbas sunan MAJNOON yayi tasiri acikin rayuwar mu ta hanyar zana mana mummunan tabo da bamusan ranan gogewarsa ba, akullum akuma kowacce rana sunan na sakeyin tasiri acikin rayuwar MAJEED, yatsai da farincinkin mu, jin dad'inmu, dama duk wani nutsuwar mu, akullum haka yake, haka yake Soumaya, tsawon shekaru haka yake rayuwarsa batare da kowa ba, Baisan farinciki ko akasin hakan ba, shiba kamar kowa yake ba, domin zuciyarsa ba irin ta kowa bace, shi wani irin mutum ne da tun asali baya iya fallasa sirrin zuciyarsa, Sirrin zuciyarsa shi kad'ai ya santa, bansan yaushene ko tayaya zuciyarsa ta kamu da ciwo ba, ciwon da watarana muke fata da sakaran warkewarsa, k'addara takan zowa bawa da sauye sauye kala kala arayuwa, kamar dai yanda yake ayanzu bashi da takamai mai me kulawa dashi, zuciyarsa ko bata da nutsuwar yin tunani, farinciki nakeso ki sama mishi Soumaya, farincikin da zaijisa koda a iyaka rabin zuciyarsa ne, mutane da yawa nayi masa kallon MAJNOON, mutum wanda ke cikin hauka, amma bana cire rai da cewa watarana zai zama kamar yanda yake ada, Farinciki shine abunda na keson gani akan fuskarsa, gami da muryarsa wacce ta disashe, amon sautinta ya daina bayyana tsawon lokaci, yaushe ne shima zai zama kamar kowa? Yaushe zan k'irasa ya amsamin? Yaushe zai fad'i wani abu daga cikin abunda yake damunsa? Hak'ik'a Ban yarda da cewa shi mahaukaci bane, banyarda da hakan ba, duk da cewar nayi imani da jarrabawar Unbangiji takanzo ta kowanni siga, amma banajin rayuwar zata tabbata ahaka."

Shiru ya d'anyi ahankali tare dasa farin handkerchief ya goge hawayen daya taru acikin idanunsa.
Ahankali cikin sark'ewar muryar dake bayyana, tsananin soyayyarsa ga d'an nasa yaci gaba da cewa.

"Shi mai raunine akan dukkan komai, bansan me zuciyarsa keso ba, kamar yanda bansan menene muradinsa ba, acikin shekaru biyu ya zama wani na daban, SHEKARU BIYU kawai, su suka sanja rayuwarsa izuwa yanda yake ayanzu, su suka juya gaban rayuwarsa ya koma baya, acikin sune kuma k'addarar da bata tab'a gogewa ta rubuta kanta acikin k'ahon zuciyarsa, k'addarar dake wahalar da rai da numfashinsa, abun da nake tambayar zuciyata akullum shine, yaushe ne MAJEED zai samu farinciki? Yaushe zai daina cutar da kansa? Yaushe zai daina wannan kururuwan da ke neman zautar masa da k'wak'walwa? Nasani shi kad'ai yasan me yakeji acikin kowacce rana, saidai da yawan lokuta abubuwansa na kama da mutumin dake cikin muradi da fatan wani abu."

Shiru yayi gami da sauk'e ajiar zuciya, kana asanyaye ya lumshe idanunsa.
Hak'ik'a shi Ubane dake fatan ganin farincikin d'ansa, shi Ubane da yake da burin ganin d'a d'aya tilon da Allah ya basa yayi rayuwa kamar yanda kowa keyi, amma Yaushe? shine abunda bai sani ba, Kamar yanda yasan ba'a girmewa k'addara, haka yayi imani cewa kowanni tsanani yana tare da sauk'i.
Kasancewar MAJEED MAJNOON bashi yake nufin cewar, zasu rasa duk wani fata ba, lallai akwai watarana da zasu tsinkayi farinciki azuk'atansu.

Duk da sautarin lokuta idan ya tuna da rayuwar Majeed d'in, ta baya yakanji hawaye na zubar masa, saboda tun asali Majeed baisan menene walwala ko nishad'in rayuwa ba.

Soumaya kuwa da tun fara maganarsa, ta sunkuyar da kanta k'asa, sai ayanzu ta d'ago idanunta ta kalli saitin da Majeed d'in yake.
Wanda hakan yasa ta sauk'e idanunta akan kyawawan k'afafunsa dake mik'e.

Wasu daga cikin kalaman Billionaire Dawoud d'in ne suka soma dawowa cikin kunnenta, wanda hakan yasa ta d'an karyar da wuyanta.
"Wani irin mutum ne shi?"
Tambayar da zuciyarta tayi mata kenan, musamman ayanzu da ta gangaro da idanun nata zuwa kan fuskarsa, da rabinta take iya kallo, kasancewar gashin kansa ya rufe masa gefen fuska.

Tabbas arayuwarta zata ce shine Namiji na farko, da ganinsa ke haifar mata da yalwataccen bugun zuciya, haka kuma shine Wanda idanunta ke yi mata nauyi, da kuma gaza iya jure kallonsa.
Akansa ta farajin ta zama zautacciya, akuma kansa ta faraji da fahimtar sauyawar duniyarta.

"MAJNOON!"
Ta fad'i kalmar da take jinta abaki da kunnuwanta kamar ba daidai ba, kalmar da takejin kamar bata cancanta afad'eta ako ina dangane dashi ba, shi daban yake haka kuma kalmar ma daban take.
Komai daban dabanne acikin kyawawan idanunta da ta mayar ta lumshe su ahankali.

Billionaire Dawoud kuwa zamansa ya gyara tare da fuskantar Soumaya'n, cikin sanyi me d'auke da damuwar dake damun zuciyarsa, murya atausashe yace.
"Bamu jawoki cikin rayuwarmu dan mu cutar dake ba, saidai inaso kiyi min alk'awarin kulawa da MAJEED, duk da cewa nasan hakan abune me matuk'ar wahala, amma nasan zaki iya Soumaya!Dan Allah kiyi mini alk'awarin bashi farinciki koda kuwa na lokaci kad'an ne nasan hakan zai taimaka, Majeed bai saba rayuwa da kowa ba, amma nayi imani ba kad'aici yake so ba, dole akwai abunda yake MURADI, kimin alk'awarin zame masa katanga, da kuma mafaka aduk lokacin da yake jin cewa bashi da kowa ki zame masa kowa da komai."

Saurin bud'e idanunta dake alumshe tayi, tare da kallon Billionaire Dawoud d'in. Duk abunda ya fad'a acikin maganganun nasa taji, amma saidai bata fahimta na.

Ta zama katanga ga MAJEED d'in ta yaya? Tayaya zata iya bashi farinciki? Shi mutum ne dako magana bayayi, ta inane zai bayyana farincikinsa?
Tayaya yarinya kamarta wacce zuciyarta ke cike da rauni, zata iya bawa Namiji MAJNOON farinciki?
Itama farincikin take nema, saboda tayi nesa da k'ashin bayanta.

Wannan dalilin yasa ahankali ta soma d'an girgiza kanta, tare da k'ok'arin motsa labb'anta da takejin sunyi mata nauyi.
Magana take sonyi amma takasa hakan yasa ta rumtse idanunta.
Daidai lokacin kuwa Dr. Mouhammad ya dawo cikin Library'n, hannunsa rik'e da wasu allurai guda biyu.
Da kallo ta bisa, yayinda shi kuma Billionaire Dawoud yake kallo, tare da d'an duba agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunsa.
"Lokacin injection d'insa yayi."
Ya fad'a yana me d'an tsirta ruwan alluran dake hannunsa, gami da nufan Inda Majeed din ke zaune.

Da sauri Soumaya ta maida idanunta ta sake rumtsewa.
Tare da kawar da kanta gefe.
Wanda ganin hakan yasa Billionaire Dawoud mik'ewa tsaye.
Cikin tausasa murya yace.

"Taso muje na nuna miki masauk'inki."

Aikuwa dama kamar jira take, cikin sauri ta mik'e duk da cewa babu kuzari ajikinta, batare kuma da ta sake waigayawa ta kalli Majeed d'in ba, tabi bayan Billionaire Dawoud suka fice daga cikin library'n, hannunta na dama rik'e da na hagun wanda yake d'aure da bandage.

Kaitsaye wannan d'an madaidaifin falon suka fito da yaji abubuwan more rayuwa, inda Billionaire Dawoud yasa hannu ya bud'e d'aya daga cikin k'ofofin, d'akunan dake falon wanda suke b'angaren dama.

"Wannan shine d'akinki, za kuma ki iya amfani da komai dake cikinsa, akwai kayayyakin dake cikin akwati suma naki ne."

Billionaire Dawoud din ya fad'a, yana me yi mata nuni da hannunsa alaman ta shiga.

kai ta jinjina masa da sauri, tare da rab'awa ta gefensa ta shiga cikin d'akin, duk atsorace take domin gani take kamar Majeed din zai biyota ya kamata.

Ganin ta shige cikin d'akinne kuma yasa Billionaire Dawoud jawo k'ofar ya rufe, tare da juyawa kaitsaye ya koma cikin library'n.

Soumaya kuwa.
Idanunta ta soma jujjuyawa ahankali tana me k'arewa babban d'akin kallo.
Kasancewar irin d'akin nanne da aka k'awatasa da komai na more rayuwa. Musamman kayan furnitures d'in dake cikinsa, Roman bed ne irin na k'asar waje da babu yawan kwalliya ajikinsa, amma anyi masa tsari mai kyau da burgewa.
Daga can k'arshen bangon d'akin kuwa,?babban glass drawer ne mai murfi shida, wanda aka k'awata jikinsa da kwalliyan daya k''ara haska d'akin.

Idanunta ta d'an lumshe ahankali tare da matsawa can gefe ta jingina bayanta da jikin bango.
Akaro na farko kenan da ta sauk'e ajiyar zuciya tare da d'an zamewa, ta zauna dab'as akan lallausan Turkish carpet d'in, da ya rufe tiles d'in dake k'asan d'akin.

Numfashi ta kuma shak'a, numfashin daya shigar mata da wani irin sassanyan yanayi.
Mai d'auke da wani irin k'amshin da ta rasa ta ina yake shigowa.
"Lallai wannan shine sabuwar rayuwa Soumaya, wannan itace sabuwar Duniya, haka kuma sabuwar k'addararki.
K'addarar da bata gushewa, wacce afkuwarta ya zama dole agareki."

Abunda zuciyarta ke fad'a mata kenan wanda hakan yasa ta d'an bud'e idanunta, siraran hawayen dake cike acikinsu suka samu daman gangarowo kan k'uncinta.
Hannunta wanda ke d'auke da ciwon ta kalla, hakan yasa ta k'ara jin hawaye na zuba mata, kasancewar sai ayanzune takejin zafi da kuma rad'ad'in ciwon.

Wannan Wacce irin rayuwace?
Zuciya da k'wak'walwarta ke tambayanta.
Wanda hakan yasa take wata magana da suka tab'ayi da Noor ya fad'o mata.
Bata tab'a manta yanda Noor din cikin sakin fuska ke sanar da ita cewa tanason aure.
Ranar aurenta, ranar da zata kasance da wanda takeso, ranar da za'akaita gidan mijinta, rana ta farko da bazata tab'a mantawa da ita ba arayuwa.

Ranar da zata zama y'ar gata mai amsan farinciki ga masoyinta.
Ranar da zai shagwab'ata ya kuma tarairaya ta.
Wannan ranar take jira.

K'warai alokacin dariya takeyiwa Noor d'in, saboda ita alokacin maganar Aure bata tab'a shigowa cikin tunaninta ba, bata tab'a kawo cewa k'addara zata sauya rayuwarta haka ba.
Wannan shine farinciki?
Tabbas itakam ta samu canjin rayuwa.
Domin aranar Auren nata ne tayi kuka irin wanda bata tab'a yi ba, akuma ranar auren nata ne tasamu raunin da yayi sanadiyar d'aura mata bandage ahannu.
Meyasa nata k'addarar ya banbanta dana kowa?

Shine abunda take tambayar kanta, yayinda acikin zuciyarta takejin kewar mahaifinta, wanda ayanzu tunaninsa ya fad'o cikin k'wak'walwarta.

Sabbin hawaye ne suka sake silalowa daga cikin idanunta, Wanda hakan yasa ta sanya hannu ta dafe daidai saitin zuciyarta.
Ahankali cikin kuma rawar murya tace.
"Rayuwa ta ta canja Abbou, ina matuk'ar kewarka, ina kewarka sosai! k'addarata ta nesanta ni da zama akusa dakai, saidai ina fatan watarana, watarana na sake zama dakai."

Ta k'are maganan tana me rumtse Idanunta, saboda wani irin kuka da taji yana neman k'wace mata.
Kukan da tasan zatayi shine kawai babu mai rarrashi, kukan da ita kad'ai zataji sautinsa.
Daga ita sai wata zuciyar dake manne da nata, zuciyar da takejin sautin amon bugawarta akullum akuma koda yaushe.

MAJEED!!
Idanunsa dake abud'e ya rumtse, badan wai dan kuma zafin alluran da ya ratsa jikinsa ba.
Saidan yanda yakejin tamkar ana buga masa guduma atsakiyar kansa.
Yayinda zuciyar dake Killace acikin kirjinsa, ke bugawa da k'arfi tamkar zata faso k'irjin nasa ta fito waje.

Akullum daidai wannan lokacin tunaninsa ke juyewa.
Wani abu yakejin yana da buk'ata.
Abun da zai tsayar da wannan bugawar zuciyar.
K'ara da kuma sautin iface ifacen da yakeji acikin kunnuwansa, sune ke neman haukatasa, tare da birkita masa duk wani nutsuwarsa.
Baya ga haka tayaya ne zai iya jurewa yanda yakejin suka acikin fatar jikinsa?

Kansa ya shiga girgizawa ahankali wanda hakan yasa duk wani gashi dake jikinsa mimmik'ewa.

Ad'imauce kuma cikin gigicewa tare da gushewan da tunaninsa yayi, ya sanya hannayensa duka biyu ya rik'e kansa.
Da sauri Dr. Mouhammad yaja jikinsa baya, cikin tsananin tashin hankali, tare da kallon Billionaire Dawoud Saraki, Wanda ya tsurawa d'an nasa idanu.
Shiru d'akin ya d'auka na d'an wasu seconds.
Before Majeed d'in yafara girgiza kansa cikin kid'ima tare da k'ank'ame jikinsa waje d'aya.
Duk jijiyoyin jikin nasa sun tashi sunyi rud'u rud'u tamkar wanda ake hurasu.

Kansa yake murzawa abirgice, yana sakin wani irin numfashi, tare da fara neman inda zai saka kanshi.
Da'alama wajen b'uya yake nema, mafakar da zata sama masa relief na daga abunda yakeji.

"Yah Allah wannan wacce irin rayuwace? Wacce irin k'addarace Majeed ke fuskanta?."

Billionaire Dawoud ya fad'a cikin tashin hankali had'i da rumtse Idanunsa.
Saboda bazai iya jure kallon Majeed din cikin irin wannan yanayin ba.
Kasancewar da wannan yanayin ne Majeed d'in ya samu tambarin sunan MAJNOON!!

Abunda yasa shi mik'ewa tsaye da sauri ya juya ya fice daga cikin library'n.
Yana me sanya hannayensa ya toshe kunnuwansa, saboda ihun Majeed din daya fara jiyowa na tashi.

Dr. Mouhammad ma dake tsaye ganin hakanne yasa shi juyawa da sassarfa yabi bayan Billionaire Dawoud din.

Hakan yasa suka bar Majeed din shi kad'ai acikin library'n.
Yayiwa kansa rik'o me tsananin k'arfi tare da rumtse idanunsa.
agigice kuma cikin yanayinsa na fitar hankali, ya mik'e tsaye tare dasa duka hannayensa, ya soma watsi da duk wani abu dake cikin library'n.
Batare dako damuwa da yanda yake sake jiwa kansa ciwo yayi ba.

Tabbas buge buge yakeyi irin na mahaukata.
Saidai kuma sab'anin tunani shine, abunda ke cikin kwakwalwa da zuciyarsa bashi yake aikatawa a fili ba.

K'warai muradin wani abu yake, had'e da neman inda zaije ya b'oye kansa.
Duk da yanayin nasa kuma hakan bai hana zuciyarsa raunana ba.
Zuciyarsa dake bugawa aduk bayan kowanni second, cikin yanayi na daban mai matuk'ar ban tausayi.

Almost 15mn
A kid'eme yake ci gaba da yawo acikin libraryn, yana me neman mafaka wanda rashin samun hakan yasa shi sulalewa k'asa, tare da sanya kansa, abayan wani d'an drawer dake cikin library'n ya duk'unk'une jikinsa dake b'ari waje d'aya.
Agigice kuma yaci gaba da sakin numfarfashi, kamar yanda jikinsa ke rawa haka ma lips d'insa, ga kuma tongue d'insa dake nannad'ewa.

Wani abu yakeson furtawa abu d'aya amma ya kasa.
Abunda ke cikin zuciyarsa akullum akuma koda yaushe.
Duk da yanajin abun nesa dashi.
Amma zuciyarsa na fafutukar nema.

Idanunsa ya sake rumtsewa, tare da sanya hakwaransa ahankali ya soma cizan lips d'insa.
sannu ahankali kuwa yake jiyo sautin bugun zuciyar, dake amsa amo acikin kunnuwansa.
Hakan yasa cikin abunda bai wuce mintuna 6 ba, duk wata gab'a dake jikinsa ta somayin sanyi.
kafun cikar wasu y'an mintuna kuwa komai nasa ya sak'e, ya zamana ko d'an yatsan hannunsa ya kasa motsawa.

Asanyaye da kad'an da kad'an kuma idanunsa suka fara rufewa, har dai suka rufe kirib, atake numfashinsa ya soma janyewa yana yin k'asa.

Haka ma brain d'insa dake haukace cak ta tsaya da yawaita aikin da takeyi.
Tamkar wanda akayiwa alluran gusar da hankali haka ya zama lokaci d'aya.

Babu wani abu dake aiki ajikinsa face numfashi da bugawar zuciyarsa, Wanda duk k'arfin alluran da akayi masa, bata tab'a tsayawa saboda beating din da takeyi ba na haka kawai bane.
Na fatan samun muradinsa ne!.

Adaidai wannan lokacin itama wata zuciyar dake bugawa da k'arfi, ta soma bugawa slowly, abunda yasa Soumayan bud'e lumsassun idanunta ahankali, ta sauk'esu akan wani babban hoton dake mak'ale jikin bangon d'akin, Wanda tun shigowarta sai yanzu idanunta suka sauk'a akai.

Tashin farko na kallon hoton, idanunta suka soma yi mata gizo Wanda hakan yasa ta kafe hoton da idanu.
Tare da d'an sake ware idanun nata dan tabbatar da cewar shid'inne, gaskiya idanunta ke gane mata ko kuwa da gaske ta zauce ne.

"Tabbas nima na zama zautacciya."
Ta fad'a alokacin da kyawawan eyeballs d'insa ke sake cika mata idanu, Wanda suka kasa barin tayiwa hoton kallon tsab.

Duk da cewar gizo idanun nasa keyi mata, amma hakan bai hanata hango wani abu acikinsu ba.
Wani abu mai wuyar fassaruwa, Wanda ta kasa karantarsa, duk da ya kasance tamkar rubutu ne wanda baya tab'a goguwa.

*0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz Bank.*

WhatsApp 07079917168

*7:47 pm*


You are reading the story above: TeenFic.Net