Chapter Five

Background color
Font
Font size
Line height

*MAJNOON!!*
(The innocentmad)

*Writting By*
Fatymasardauna
*Wattpad*
@fatymasardauna

https://chat.whatsapp.com/HpvXJSFFoZs9S2nIXPa5xh

*(This book is mainly for those that pay, If you know you didn't pay please don't read it. Here is the Account Number for people that are willing to pay-0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz Bank. AMOUNT 300, WhatsApp Number 07069917168)*


*CHAPTER 5*

*FREEPAGE*

Wani irin tsalle had'e da bugawa zuciyar Soumaya tayi, Wanda har saida hakan ya haifar mata, da tsayawan numfashinta na y'an wasu mintunan.
Haka ma duk wani tunani, da ke tafiya da bugun zuciyarta saida ya tsaya cak.

Maganganun Dr. Mouhammad ne suka shiga yi mata yawo, acikin kunnuwanta.

"Rashin yi masa aikin daidai yake da rasashi, I mean rasashi na har Abada."

Wanda hakan yake neman yi mata barazanar tarwatsa kwakwalwa da zuciyarta, then kalaman da suka sa, Rauninta sake Raunana, suka kuma tsaida motsin duk wani abu dake jikinta, saidai numfashinta dake kokarin kwacewa wanda take ta faman kokuwa dashi.
Tabbas bata shirya rasa Abboun nata ayanzu ba, wannan dalilin yasa ta tsurawa Dr. Mouhammad din idanunta wanda suka riga da suka kakkafe, duk da yawan kukanta, ayanzu kam hawayen sunyi nisa, saboda tsananin shock din da tasamu kanta aciki.

"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un! Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!!"

Shine abunda Malam Musbahu yake fad'a, tare da zare hulan dake saman kansa ya soma fifita da ita, duk da sanyin A/C'n dake cikin d'akin kuwa, shi wani gumi yake had'awa.

"Likita wannan wani irin aiki ne haka daya zama dole sai anyi masa, kuma sai an fitar dashi har k'asar waje fa naji kace."

Malam Musbahu'n ya tambaya, cike da damuwa, had'i da rud'ewa.

Kai Dr. Mouhammad ya jinjina, had'i da sauk'e Ajiyar zuciya, saidai hango tsananin tashin hankalin da yayi akan fuskokinsu ne yasa shi, tausasa muryarsa ta hanyar cewa.

"Hak'ik'a aiki ne daya zama wajibi sai anyi masa, saboda cutar tayi k'arfi ajikinsa sosai, ta yanda take kokarin fara tab'a masa wasu sassa dake cikin kansa, Kamar kuma yanda na fad'a muku dole sai anfitar dashi waje, zuwa k'asar Germany domin acanne suke da asibiti na musamman, Wanda suke yiwa mutane masu irin nasa matsalar aikin kwakwalwa, duk da cewar aikin yana da tsada sosai, amma yi masa aikin shine abu mafi sauki, saboda ayanda ciwon yaci k'arfinsa, babu wani magani da za'a bashi wanda zai sama mishi sauki."

D'an Jim yayi tare da gyara zaman glass din dake idanunsa, duk da baisan tayaya zasu fahimcesa ba amma ya zama dole ya fad'a musu gaskiya.

Wannan dalilin yasa asanyaye yace.

"Dukanmu mun sani, Allah ne me rayawa da kashewa, amma a iya binciken da mukayi irin namu na likitoti, mungano cewa matuk'ar ba ayi masa aikin zuwa nan da Kwana bakwai ba, To yana iya rasa rayuwarshi, aciki lokaci k'ank'ani!!"

Idanunta ta rumtse da sauri tare da dafe daidai saitin zuciyarta, wacce ke barazanar faso kirjinta ta fito.

"A'a Abbouna bazai mutu ba insha Allah, zan rayu dashi zamu kasance cikin farinciki, nayi mishi alk'awarin zama abunda yake so, nayi mishi alk'awarin zama babbar Likita tayanda, zan taimakawa al'umma, nayi masa alk'awarin sanyasa farinciki na har abada, ban shirya rasashi ba, bazan iya rayuwa babu shiba bazan iyaba."

Zancen zucin da takeyi kenan, Wanda hakan yasa wasu zafafan hawaye gangarowa daga cikin idanunta, zuwa kan fuskarta.

Araunace kuma cikin muryar matsanancin kukan dake kokarin kwace mata, ta juyo da kallonta ga Dr. Mouhammad d'in.

"Dr. Inason Abbouna ya rayu, dan Allah kada kafad'amin cewar rasashi yana daga cikin k'addarar rayuwar da Zan fuskanta, na rasa mahaifiyata bani da kowa aduniya sai shi, dan Allah Doctor....! Dan Allah!!!!"

Ta k'are maganan tana me rumtse idanunta, Wanda suke ta zubar da hawaye tamkar an kunna famfo.
Yayinda acikin zuciyarta takejin, tamkar ace itace ke dauke da ciwon bawai Abboun ta ba.

Numfashi mai d'umi Doctor Mouhammad ya fesar, tare da dafe kansa saboda har acikin zuciyarsa yakejin tsananin tausayinsu.

Malam Musbahu da jikinsa ya gama yin sanyi kuwa, kallon Dr. Mouhammad din yayi, kana cikin sigar damuwa yace.

"Likita tunda kace aikin ya zama dole, nasan to lallai ya zama dolen ne, baya ga haka kuma nasan bazaka rasa, sanin kud'in da aikin zaici ba, dan Allah ka fad'a mana muji ko akwai wani abu da zamu iya."

Idanu Dr. Mouhammad din ya lumshe, saboda ya sani abune me matukar wahala su iya biyan kudin aikin da za'ayin, wannan dalilin yana daya daga cikin abunda yasa, yakejin tausayinsu, haka kuma yakejin fargaban fad'a musu, amma abune daya zama dole sai ya fad'a.

D'an yunk'urawa yayi, tare da turowa Malam Musbahu wata takarda dake gabansa.

"Duk wani bayanai daya shafi rashin lafiyar nashi yana nan acikin takardar nan, kama daga kudin aikin da za'ayi mishi da komai, Wanda har kudin aikin nasa da za'ayi masa, da ya kasance Naira million 30, shima yana rubuce acikin takardar."

Tabbas awannan karon kam ba iya zuciyar Soumaya bace, ke barazanar tarwatsewa harma dana Malam Musbahu, Wanda jin kud'in aikin, yasa gumi yanko masa, take kuma yaji tsohuwar Ulcer'n sa na kokarin tashi.

"Naira Million 30!! Innalillahi wa Inna ilaihirraju'un, Hasbunallahu wani'imal wakeel, allahumma ajirni fil musibati!!!"

Shine abunda Malam Musbahu'n ya fad'a, yana me dafe kirjinsa.
Sbd wani irin abu da yaji yana sukan kirjinsa.

Iya Malam Musbahu kenan, Soumaya ko tayaya zata misalta yawan tashin hankalinta?
Tayaya zata misalta tsananin tashin hankalin da ta samu kanta aciki, Tayaya zata fara fad'in yanda zuciyarta, ke barazanar tarwatsewa, saboda kalaman Dr. Mouhammad din da taji.

Hak'ik'a duk wani tunani da k'warin guiwarta sun tsaya, kamar yanda gangar jikinta ma ya tsaya,daga motsa komai nasa.
Numfashine kawai yake fita daga hancinta, numfashin da fita da shigansa ke haifar mata, da tsananin tsoro da fargaba.

"Likita dan girman Allah da Annabinsa, ka taimake mu ka samo mana wata hanyar, domin nayi maka imani da Allah mu talakawa ne, bamu da wannan kudin, haka kuma bamu da hanyarsu, wallahi Allah ko rabin million d'aya bamu dashi, balle wasu mak'udan kud'ad'e har naira Million 30."

Malam Musbahu ya fad'a, yana me kokarin zamewa k'asa alaman roko, saboda abune daya sani, ko kawunansu zasu sayar bazasu tab'a samun way'annan Millions din kud'ad'en ba.

Ajiyar zuciya Dr. Mouhammad ya sauk'e, kana cikin sanyin murya yace.

"I'm sorry to say, domin da ace akwai Wata hanya mai sauki da bata kai Wannan ba, To da ita zan fad'a muku, amma babu wani solution sai wannan, da ace kuma aikin nasa anan gida Nigeria ne, zanyi duk wani kokarin da zan iya, amma akasin hakan yasa babu wani abu da zan iya."

Dr. Mouhammad din ya k'are maganan araunace, tare da maida kallonsa ga Soumaya, wacce idanunta ke alumshe, yayinda hawaye ke gangarowa daga cikin idanun nata zuwa kan kuncinta.

"Innalillah."
Shine abunda kawai Malam Musbahu ya iya fad'a, still yana me fifita da hulan dake hannunsa.

Daidai lokacin kuma aka soma Knocking k'ofar office din Dr. Mouhammad din, da alama kuma next patient ne sukeson shigowa.

Hakanne kuma yasa, Dr. Mouhammad din d'ago dakai ya kallesu, kana cikin tausasawa yace.

"Zaku iya komawa d'aki ku dubasa, amma karku manta bamason hayaniya a inda yake, idan nagama abubuwan da nake Zan sake shigowa na duba jikin nasa."

"To shikenan Likita."
Malam musbahu ya amsa tare da mikewa tsaye.

"Soumayatu tashi muje."
Ya fad'a asanyaye tare da kallon Soumaya'n wacce ke zaune, Wanda har zuwa yanzu b'ata bud'e idanunta ba, sannan kuma har yanzu zuciyarta bata daina bugawa ba.

Saidai kuma jin sauk'an muryan Malam Musbahu'n acikin kunnuwanta ne, yasa ta bud'e idanunta wanda sukayi jajur, kana asanyaye ta mik'e tsaye, tare da soma taka k'afafunta wanda take jin sunyi mata nauyi, tamkar ma bazasu iya d'aukar ta ba.

Haka dai asanyaye tabi Bayan Malam Musbahu da ya soma tafiya, daidai sun kai bakin k'ofar fita daga cikin office d'inne kuma.

Dr. Mouhammad daya bisu da idanu, cike da tausayawa, kana kuma cikin d'an d'aga murya yace.

"Kada ku manta kwana bakwai kawai kawai muke dashi."

Idanunta ta kuma rumtsewa, saboda yanda takejin bugawar zuciya da kuma fad'uwar gaba naci gaba da ruskarta, yayinda kowanne maganan da zai fito daga bakin Dr. Mouhammad din, yakasance tamkar makamashin rura tsoro, fargaba, da kuma tashin hankali ne agareta.

Duk da cewar kuwa izuwa yanzu sun fice daga cikin office din, amma sautin muryar Dr.Mouhammad dinne keyi mata yawo acikin kunnuwanta.

Kaitsaye d'akin da aka kwantar da Abboun nata suka nufa, yayinda ya kasance bayan Malam Musbahu'n kawai takebi, batare da tasan inda take jefa k'afarta ba, saboda tsabar hawayen da suka cika idanunta kuwa, yasa ko gani da kyau batayi.

kasancewar kuma dakin da aka kwantar da Abboun babu nisa, da office din Dr. Mouhammad dinne yasa cikin mintuna kad'an suka iso.

Malam Musbahu dake cikin yanayin damuwa da firgici ne, ya bud'e musu kofar d'akin suka shiga.

Har yanzu dai kyakkyawan farin dattijon, yana nan akwance sanye da oxygen, duk da cewar kuma fuskarsa wacce take yanayi dana y'an k'asar Somalia🇸🇴, ta d'an fad'a amma hakan bai hana mai kallonsa, ganin tsananin kaman da sukeyi da Soumaya.

Idanunta wanda suke cike da ruwan hawaye ta zubawa, kyakkyawar fuskar mahaifin nata.
Yayinda takejin wani irin tsananin sonsa da k'aunarsa na ratsa ta.

Ahankali kuma ta d'an soma takawa zuwa jikin gadon da yake.
Inda yake kwance flat, babu wani abu dake motsi ajikinsa, banda kirjinsa dake d'an motsawa, saboda numfashi da kuma bugawar da zuciyarsa keyi.

"Abbou!"
Ta kira sunansa ahankali, da muryarta wanda sautin ta baya fita, saboda kukan dake kok'arin k'wace mata.
Sanin da tayi cewar bazai amsa mata bane, kuma yasa Asanyaye ta sa hannu ta dafa, kafad'an sa.

Sosai kuwa kallon fuskar nasa da takeyi ayanzu, ya sake haifar mata da rauni, hadi da karyewan zuciya.
Tabbas Tana tsananin son mahaifin nata, domin shi din ya kasance na musamman ne agareta.

Yayinda har izuwa yanzu kuma maganganun Dr. Mouhammad, ne keyi mata yawo acikin kwakwalwa, bazata tab'a iya jure rashin mahaifin nata ba, kamar yanda bata san inda zasu samo Naira million 30 acikin kwana bakwai ba.
Abune mawuyaci ta sani, domin aduniya basu da komai sai d'an gidan daya rage musu, gidan da duka duka idan akayi masa kud'i bai wuce 2.5 Million ba, tayaya zasu samu irin way'annan mak'udan kud'ad'en? 30 million ba kud'ine na wasa ba, kuma acikin kwana 7.

Asanyaye ta sunkuya ajikin Abboun nata, tare da d'aura kanta akusa da nashi, lokaci daya wani irin kuka mai tsuma zuciya ya k'wace mata, kukan da ta shiga rerasa tamkar ranta zai fita.
Kukan da babu mai rarrashi.

Domin shi kansa Malam Musbahu dake tsaye, yana me sauraran kukan nata, ayanzu shima hawayene fal acikin idanunsa.
Hawayen tausayin ta, saboda yasan bayan Allah mahaifin nata ne kad'ai gatan ta.
Yaune rana ta farko da yasoma jin Ina ma da ace shi wanine aduniyar nan, to tabbas daya taimakawa amininsa da kuma y'arsa, saidai shima talakane dake neman rufin asirin Allah akoda yaushe, talakan da dak'yar yake samun nakaiwa bakinsa.

Sam bazai iya hanata kukan nata ba, saboda imani da yayi cewa, kuka rahama ne dan yana ragewa maiyinsa rad'ad'in zuciya.

Wannan yasa gaba d'aya d'akin ya d'auki shiru, sae kukan Soumayan kawai dake tashi acikin lungu da sak'o na d'akin.

Kwarai kuka take me tab'a zuciya, kuka irin wanda ke bayyana losing hope d'inta.

Kusan kuma mintuna 20 ta kwashe tana rera kukan nata, kafun daga bisani. Sautin kukan nata ya soma raguwa ahankali, yayinda sautin bugun zuciyarta kuwa ke k'ara tsananta.

Kanta dake gefen na Abboun nata ta zare, kana ta d'ago jajayen idanunta, Wanda lokaci daya suka rune tamkar anwatsa musu Jan borkono.

Juyo da kallonta tayi ga Malam Musbahu wanda ke tsaye, yayi jigum kallo d'aya zakayi masa ka fahimci cewa yana d'auke da tarin damuwa.

"Kowani bawa da irin nasa k'addarar amma ni Baffa me yasa tawa tazo ahaka? Narasa mahaifiyata tun ina da wata 2 aduniya, yanzu kuma gashi Ina shirin rasa Abbou na, bazan iya ci gaba da rayuwa ba matuk'ar na rasa shi, shi kad'ai nasani, shine wanda ya raineni tun Ina da wata 2 har kawo yanzu dana girma, shekaru 19 yayi yana d'awainiya dani, Baffa Abbou ne wanda yake hana idanunsa bacci, saboda yaje ya Nemo kudin dazai kula dani, Abboune wanda zai wuni baici abinci ba, saboda yana nemamin abunda zai rufa asirina, saboda nayi farinciki kawai Abbou zai iya jure kowani irin wahala, shine wanda nake iya fad'awa matsala ta ya fuskance ta, akowani bugun zuciyata bana tab'a mantawa da sunan Abbou na, tayaya zan iya fuskantar rasashi ayanzu? Tayaya zan samo tarin kud'ad'en da za'ayi masa aiki ya samu lafiya? Me zanyi Baffa yaya zanyi? Waye zai taimakeni akan wannan?...."

Ta k'are maganan cikin sabon kukan, dake fitowa daga k'ark'ashin zuciyarta.

Kukan da yasa hawayen Malam Musbahu gangarowa bisa kan fuskarsa.

Shikansa zuciyarsa ta jima da karyewa, wannan dalilin yasa asanyaye yace.

"Allah zaiyi mana komai Soumaya, matuk'ar Allah Nanan babu wani damuwa da zata tabbata, haka kuma babu wani k'unci dazai d'ore Insha Allah Abbounki zai samu lafiya."

Kanta ta d'an soma girgizawa, cikin muryar ta da bata fita sosai, saboda kukan da tayi tace.

"Kwana bakwai Doctor yace, kwana bakwai kawai, inajin tsoron rasa Abbou, saboda babu ta yanda zamu iya biyan wannan kud'in, lokaci kankani kudi da yawa Baffa tayaya?"

"Allah zaiyi Soumaya, hanyoyin Ubangiji basa k'arewa, yanzu dai ki daina wannan kukan, domin zai iya haddasa miki ciwon kai, ki sawa ranki juriya, a komai naki kuma kina tuna Allah, rahamarsa bata yankewa, ni yanzu bari naje na nemo kud'in gwaje gwajen da akayi masa na biya, dan naga suma kud'ad'ene masu d'an yawa, dan sun cimma dubu d'ari."

Ya k'are maganan yana me juya takardar dake hannunsa, wacce take d'auke da bayanai akan rashin lafiyar Abbou'n, da kuma kud'ad'en da zasu kashe.

Da Idanunta masu bayyana rauni ta d'ago, ta kalli Malam Musbahu'n, saboda tasan cewar shi ma kamarsu yake, dan haka ba lallaine ya zama yana da kud'in da zai iya biyan asibitin ba.

"Kajira ni Baffa inazuwa."
Ta fad'a asanyaye tare da mik'ewa, kaitsaye ta nufi hanyar fita daga cikin d'akin.

Da sauri Dr. Mouhammad wanda tun d'azu yake tsaye abakin k'ofar yaja da baya, tare da shigewa cikin wani corridor saboda Sam bayaso suganshi.

Ajiyar zuciya ya d'an sauk'e, yayinda hakanan yaji al'amarin su ya tsaya masa arai da zuciyarsa.

Soumaya kuwa batare da ta lura dashi ba kaitsaye ta fice daga cikin d'akin, yayinda Malam Musbahu kuwa ya nemi waje ya zauna.

Tafiya ta somayi ahankali, batare dako sanin inda take saka k'afarta tayi ba, tabbas bazata ce akwai nutsuwa ajikinta ba.
Wannan dalilin yasa duk inda ta gilma, sai mutanen dake wajen sun bita da ido.

Kaitsaye hanyar fita daga cikin asibitin ta nufa, koda ta fito wajen kuwa, rana akeyi sosai da sosai, Wanda hakan yasa ta tsayawa akan titi, batare da ta damu da zafin ranar dake dukanta ba.

Sama da mintuna 30 ta kwashe tsaye awajen, saboda ababen hawa na haya da sukayi wa wajen k'aranci.

Cikin sa'a kuwa tana nan tsaye, wani mai taxi yazo wucewa, hakan yasa da sauri tasa hannu ta tareshi.

Yana tsayawa agabanta kuwa ta bud'e murfin motar ta shiga, bayan ta gaya masa inda zai kaita ne kuma, yaja taxi din sukayi gaba.

Bayanta ta jingina da jikin kujeran motar, had'e dasa hannu ta dafe kanta, da takejin yanayi mata ciwo sosai, daga gefe guda kuma wani irin masifafaffen yunwa ne ke tsakalan cikinta, Wanda har hakan yasa takejin wani abu na sukan bayanta.

Ajiyar zuciya take ta sauk'ewa akai akai irin na way'anda sukaci kuka suka k'oshi, wannan dalilin yasa mai taxi din ke yawan kallonta ta madubi.

Daidai isowarsu inda tayi masa kwatance ne kuma, yasa shi tsaida motar.
Jin alamun tsayuwar motar ne kuma yasa,
Ahankali ta bud'e idanunta wanda suka fara kumbura, tare da mikawa mai taxi din ragowar canjin dake hannunta, kana ta bud'e murfin motar ta fito, kaitsaye kuma ta nufi gidansu.

D'an makullin dake hannunta tasa ta bud'e gidan, kasancewar har zuwa yanzu Moudou bata dawo ba, yasa kaitsaye ta wuce d'akinta.

Asanyaye ta zame d'an madaidaicin mayafin dake jikinta.

Tare da karasawa ta tsugunna adaidai wajen katifarta, gefen katifar ta d'aga, tare da zaro wata bak'ar leda.
Kana ta koma ta zauna, gami da tankwashe k'afafunta.

Ahankali ta warware ledan, tare dasa hannayenta duka biyu ta ciro kud'ad'en dake ciki.

Jujjuya kud'ad'en ta somayi ahankali, lokaci daya kuma taji sabbin hawaye sun sake cika idanunta.
Saboda tunawa da tayi, yanda Abboun ke bata duk kud'in daya samo kullum idan ya dawo tana tarawa, saboda biyan schoolfees.

Kud'in wanda yakai dubu 80 dake hannunta ta sake jujjuyawa, tare da maida jikinta ta kwanta akan katifarta.

Saura musu 1week su fara biyan kud'in, Wanda kuma duk wanda bai biya ba, a zaune yake bazai rubuta exam din second semester da zasu fara rubutawa nanda sati biyu masu zuwa ba.

Kasancewar suna biyan schoolfees din 100k, yasa Abboun yi mata alk'awarin nemo mata sauran 20k da zata cika ta biya kudin makarantar.

"Bazakayi nisa dani ba ABBOU."

Ta fad'a asanyaye tare dasa hannu ta goge, zafafan hawayen da suka gangaro daga cikin idanunta.

Lokaci d'aya kuma ta mik'e, tare dasa kud'in acikin d'an baby hand bag dinta, cikin sauri ta fita daga d'akin.

Anan cikin tsakar gidansu, ta samu cutie'n ta, wacce ta takure jikinta waje d'aya, da dukkan alama kuma yunwa takeji.
Dan dama Abbou ne ke saya wa cutien kifi kullum tanaci, sai kuma ita idan ta d'an samu kudi ta saya mata madara.

Durk'usawa tayi tare da d'ago cat din nata, ahankali ta soma shafa jikin kuliyar.

"I'm so sorry cutie, yau babu abinci but insha Allah everything will be fine."

Tayi maganan tana meyin raurau da idanunta, duk da kuwa tasan cewar kuliyar bajinta zata yi ba.

Kusan mintuna 5 ta d'auka ahaka. Kafun daga bisani ta sauke cutien daga jikinta, cikin d'an hanzari ta fice daga gidan.

Kamar yanda tayi da safe haka yanzun ma, bayan ta rufe gidan mai adaidaita sahu ta tara tare da gaya masa inda zai kaita.

Haka suka d'auki hanya batare da ta damu, da matsanancin ciwon kai da kuma yunwan dake damunta ba.

Ahaka har suka iso kofar asibitin, bayan ta sallami mai napep dinne kuma, ta shiga cikin asibitin.

Ahankali ta tura k'ofar d'akin ta shiga, bakinta d'auke da sallama, duk da cewa har yanzu muryar nata baya fita sosai.

"Soumaya kin dawo?"
Malam Musbahu dake zaune jigum ya tambaya, tare da yunk'urin mik'ewa tsaye.

"Eh Baffa na dawo, ya ya jikin Abboun?"

Ta tambaya tana me kallon mahaifin nata, wanda har yanzu yake nan kamar dai yanda ta barsa.

"Da sauki."
Malam Musbahu ya bata amsa.

K'arasa shigowa cikin d'akin tayi, tare da bud'e jakanta ta ciro kudin schoolfees din nata wanda ta d'auko daga gida.

"Baffa ga wannan watakila zai taimaka, abiya kudin gwaje gwajen da akayiwa Abboun."

Ta fad'a tana me mik'a masa kud'in.

"Soumaya a ina kika samu way'annan kud'ad'en?"

Cewar Malam Musbahu fuska d'auke da mamaki.

"Kud'in schoolfees dina ne, da zan biya Monday mai zuwa, amma yanzu buk'atar biyan kud'in asibiti ya taso, dole ne na badasu."

Idanu Malam Musbahu ya zuba mata, cike da tsananin tausayinta.

Saboda babu yanda zaiyi ne yasa shi

You are reading the story above: TeenFic.Net