Chapter fifteen

Background color
Font
Font size
Line height

*{This book is mainly for those that pay, if you know you didn't pay please don't read it. Here is the Account Number for people that are willing to pay- 0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz Bank. AMOUNT 300, WhatsApp number 07069917168}*

             *MAJNOON!!*
       *(Theinnocentmad)*

*15*

Numfashi ta fesar tare da sauk'e wani irin sassanyar ajiyar zuciya.
Wanda kuma akaro na farko kenan yau d'in da taji sanyi acikin zuciyarta.

Idanunta dake alumshe ta bud'e tare da sake k'ank'ame jikinta waje d'aya, saboda wani irin fitinannen sanyin da takeji.
Duk da cewar bazata iya banbance wani  lokaci bane yanzun, amma Tabbas tasan cewar dare ya riga da yayi.
Saboda haka dole tana buk'atar tayi sallah.

Idanunta ta kuma d'an jujjuyawa ahankali tana me sake k'arewa d'akin kallo, har ta sauk'e ganinta akan wata k'ofa dake cikin d'akin, Wanda da dukkan alama toilet ne acikinsa.

Yunk'urawa tayi tare da soma tafiya ahankali,  duk da kasancewar batajin dad'in jikinta.
Ga kuma d'an zogin da hannun nata keyi mata.
Asanyaye ta d'aura hannunta  akan handle din kofar, tare da tura ta ciki.
Kamar yanda tayi tsammani kuwa toilet ne, me zaman kansa wanda aka k'awata cikinsa da abubuwan buk'ata na toilet masu hasken gaske.

Kumburarrun Idanunta ta d'an sake  warewa, Hade da soma k'arewa toilet din kallo.
Komai da yake cikinsa tsab tsab yake, Wanda hakan ke nuna yanda ake tsananin kula dashi, duk da cewar abubuwan dake ciki basu nuna alaman cewar ma ana amfani da toilet din ba.
Musamman wajen wankan da aka k'awatasa da gilasai masu kyau.
Haka ma mirrors d'in dake cikin toilet d'in, ko ledan dake jikinsa ba'a cire ba.

Ahankali ta saki k'ofar toilet d'in, bayan ta tura kanta ciki, ad'ad'are cikin kuma yanayi na rashin sabo, ta k'arasa gaban sink din dake cikin toilet din.

Mayafin dake jikinta ta zare ahankali tare da sunkuyawa, ta soma alwala.
Sauk'ar ruwan alwalan akan hannunta, yasa ta rumtse Idanunta tare da soma yayyarfa hannun nata dake d'auke da ciwo, Wanda ruwa ya ratsa cikin bandage din harya sauk'a akan ciwon, da lilin hakanne kuma takejin zafi.

"Auchhh!"
Ta fad'a tana me yin raurau da idanunta, Wanda tun tsawon lokaci suka sanja daga white zuwa pink color, Wanda hakan ya faru ne Kuma saboda kukan da takeyinsa babu dare ba rana.

Hannun nata take kallo asanyaye, saidai kuma sanin babu yanda zatayi yasa, dole haka ta shanye zafin ta k'arasa alwalan.

Tana kammalawa kuwa ta bud'e k'ofar toilet d'in ta fito.
Still tana me kakkama jikinta saboda wani irin fitinannen sanyin da takeji.
Wanda ya had'e mata da sanyin da zazzab'i keson haifar mata, da kuma sanyin A/C Wanda bata saba jinsa ba kwata kwata arayuwarta.
saboda tunda take sanyi biyu kawai ta sani daga na fanka sai na weather.    

Mayafin dake jikinta ta gyara, tare da soma kallon ko Ina dake cikin d'akin amma sam bataga sallaya ba.
Hakan yasa ta gyara tsayuwarta akan lallausan carpet din dake mamaye k'asan d'akin,
Tare da tada sallah.

Kamar kuma yanda yake sallan magriba ta farayi kafun tayi na isha.
Kasancewar tasan zuwa yanzu an riga da anyi sallan isha.

Koda taje sujjadarta na k'arshe Ahankali tarin hawayen dake cike a idanunta suka soma d'igowa kan lallausan carpet din.

Tabbas bazata so ace ta tsugunna agaban Allah, kuma ta tashi hakanan ba, ita mai damuwa da rauni ce akan dukkan komai.
Hak'ik'a tanason yin kuka sosai, tanason bayyana abunda ke b'oye acikin zuciyarta,  domin tasan a irin wannan lokacin, koda babu mutum d'aya da  zaijita, Allah Zaiji kukanta domin shine masanin abunda ke fili da b'oye.
Shiya shumfud'a mata k'addarar kuma shi zai bata mafita.

Saidai duk yanda taso fad'an abunda ke zuciyarta ta kasa, harshenta yayi nauyi, labb'anta kuwa sun kasa motsi.
Idanunta ta lumshe ahankali tare da d'agowa daga sujjadar, duk da yanda takejin kuka mai k'arfi nason k'wace mata, amma haka ta daure tare da sallame sallan.

Asanyaye ta nannad'e k'afafunta waje d'aya, tare da d'an zamewa ta jingina bayanta da jikin bango.

Bugawar zuciyarta dake tafiya ahankali take saurara, Wanda hakan yasa sassan jikinta ke karb'an kowanne sak'o da zuciyar ke aika mata.

Yayinda acikin idanunta kuwa wasu abubuwa na dabanne keyi mata gizo.
Tabbas har yanzu tana cikin rud'u, na ganin mafarkinta ya zama gaskiya.
Lallai ba almara bane tana ganinsa acikin mafarki, sautin gunjin numfashinsa, harma da yak'ushin da yakeyiwa fatar jikinsa komai tana gani.
Saidai bata tab'a kallon fuskar tasa ba sai ayau.
Kamar yanda bata tab'a kallon cikin idanunsa ba sai yau d'in.
Idanun da kallon cikinsu sau d'aya tak ke haifar mata da mummunan bugawar zuciya da kuma yankewan numfashi.

Tabbas akwai wani abu acikinsu, Wanda ganinsa ke jijjiga tunaninta.
Kanta ta d'an langwab'ar ahankali,  yayinda daga wani sashi na brain d'inta keson tariyo mata wani abu daya wuce.

"Watarana zakiyi nesa dani Soumaya, watarana bazamu kasance Kamar yanda muke ayanzu ba, watarana zaki tafi inda babuni akusa."
Maganganun Abbounta kenan wanda suka dawo cikin tunaninta.
Maganganun da yayi mata awatarana da tak'i zuwa makaranta saboda kawai kansa na masa ciwo.

"Banyi fatan ace ranar tazo da wuri haka ba Abbou. banyi fatan yin nesa dakai ba, Tabbas wannan sabuwar rayuwace agareni, sabuwar duniya wacce ke wasa da rayuwata, Yah Rabb ban shiryawa hakan ba."
Ta fad'i hakan cikin rawar da muryarta takeyi.
Tare kuma da zamewa k'asa ta duk'unk'une jikinta waje d'aya.

Hakanan yau din takejin kamar ba ita bace, tanajin tamkar sauyata akayi.
Domin wannan ba itace rayuwar da ta sabayi ba.
Idanunta ta kuma lumshewa a hankali, bayan ta sanya mayafin dake kanta, ta rufe duka jikinta dashi.
Duk da cewar akwai gado da kuma lallausan blanket acikin d'akin.
Amma batajin zasu iya rufe mata damuwar dake cin zuciyarta.
Haka kuma batajin cewar kwanciya akansu zai haifar mata da nutsuwar zuciya.
Domin tayi imani arana irin ta yau babu wani abu, dazai dakatar da bugun zuciya, da tunaninta.
K'wak'walwarta ta riga da ta hautsune, saboda haka babu wani abu da take tunanin zai dawo da ita daidai.

Idanunta ta kuma lumshewa had'e da sake matse jikinta waje d'aya.
Zuciyarta cike da fatan samun nutsuwar yin bacci.
Duk da tana iya jiyo yanda cikinta ke k'ugin yunwa, amma ko sau d'aya bata kawo tunanin saka abinci abakinta ba.
Hasalima fargaba take, domin Akaron farko na rayuwarta, yau zata kwana awani waje na daban da ba gidansu ba.

Yayinda daga wani sashi na zuciyarta kuwa, take bugawa saboda tsoron kada sautin amon numfashin dake barazana ga rayuwarta ya sake dawowa cikin kunnuwanta.
Wanda tasan ayanzu sake jin hakan, daidai yake da sake yankewar numfashinta.

Da wannan tunanin acikin ranta bacci b'arawo yayi awon gaba da ita.

Baccin da aduniya zata ce bata tab'a yin irinsa ba, saboda wasu irin mafarkai da tayi.
Saidai abu d'aya daya kasa barinta ta samu sukuni acikin baccin nata.
Shine Sautin bugun zuciyar dake tafiya da nata.
Wanda da ace batasan cewar kowani mutum zuciya d'aya yake dashi ba, To da zatace ita zuciyar biyu aka halitta mata acikin k'irjinta.

*Washegari.*

7:50am.

Tsanananin sanyin dake ratsa tafukan k'afa, da kuma legs d'inta  ne yasa ta soma motsa jikinta, wanda ya kwashe tsawon awanni yana duk'unk'une.
sannan duk da cewar ta lullub'e jikin nata da mayafin gyale, amma hakan bai hana sanyin safiyan da ake busawan ratsa cikin jikinta ba.

Mik'a ta d'anyi ahankali had'i da bud'e idanunta, Wanda ta sauk'esu akan Babban hoton dake mak'ale ad'akin.

Duk da cewar wannan shine karo na biyu, da ta sauk'e idanunta akan hoton.
Amma yanzun  saida taji wani irin abu acikin jikinta.

Kyakkyawar fuskar dake jikin hoton take kallo, yayinda idanunta  keson hasko mata asalin fuskar, wanda yake jikin hoton.
jajayen lips dinsa da ta kallane kuma yasa ta saurin maida idanun nata  ta lumshe, saboda hasko mata cikakkiyar fuskar sa da sukayi.

"Shine!"
Ta fad'a da muryarta wanda take ciki ciki, kasancewar yanzun tashinta abacci.
Sannu ahankali kuma Brain dinta ke sake haskowa eyeballs dinta, gefen kyakkyawar fuskarsa wacce take yalwace da beard.

Numfashi ta d'an fesar, tare da yunk'urawa ta tashi zaune.
Tana me sake gyara zaman mayafin dake jikinta, had'i da juyawa ta kalli windown dake cikin d'akin.
Taarr idanunta suka sauk'a akan hasken ranan daya fara bayyana asararin samaniya.
Zazzaro idanun nata waje tayi cike da mamaki, saboda kwata kwata batayi tunanin cewa gari yayi haske sosai har haka ba.

Da sauri ta mik'e tsaye tare da nufan hanyar toilet, fitsari tayi tare da d'auro alwala, cikin hanzari tazo ta tada Sallah'n, da ya d'auketa 5minute kafun ta idar.
Sake gyara zaman ta tayi alokacin da take karanto azhkar.
"La'ilaha illallahu wahadahu lasharika lahu, lahul mulku walahul hamdu wa huwa ala kulli shae'in k'adir!"

Shine abunda lallab'an baki da zuciyarta ke furtawa, yayinda idanunta kuwa suka  kasance alumshe.
Iya k'ok'arin samawa zuciyarta nutsuwa take, Musamman ayanzu da tayi imani cewa ta fad'a cikin k'addarar rayuwar da babu mai iya cireta acikinsa sai ALLAH.

Kwana d'aya kawai jinsa take Kamar kwana dubu, saboda wani nauyi da takeji acikin zuciyarta.

"D'id'in...d'id'in...d'nnnnn"

Wani sautin k'ara ya soma shigowa cikin kunnenta wanda yasa ta bud'e idanunta, tare da d'an dakatawa daga karanta.
"Hasbiyallahu la'ilaha illahuwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil Azeem!"  Da takeyi.

Tare da juyawa cikin bugun zuciya ta kalli k'ofar d'akin da take ciki d'in, wanda yake ad'an bud'e.
Daidai lokacin ko ta kuma jin k'aran na sake tashi.
Duk da cewar k'ara ne irin na bugun k'ofa, amma hakan bai hanata jin  tsoro ba, dan har saida taji wani sabon fitsari na k'ok'arin zuwar mata.
K'an k'ame jikinta tayi tare da mik'ewa tsaye ahankali, zuciyarta cike da tsoro ta nufi hanyar fita daga d'akin.

Koda ta iso bakin k'ofar hannu ta d'aura akan handle d'in k'ofar, jiki na b'ari ta k'arasa bud'ewa.
Tare dakai dubanta ga corridor d'in, da idanunta suka gane mata shi acikinsa jiya.
Dan atunaninta daga canne k'aran ke fitowa.
Kanta ta sake lek'awa cikin corridor d'in da cikinsa library'n yake, saidai babu abunda kunnuwa da idanunta ke gane mata face duhu,  wanda yake tamkar ba safiya ba saboda yanda wajen ke cike da duhu, babu wani alaman haske.

D'id'in...d'id'In...d'id'innnn

Kunnuwanta suka sake jiyo mata sautin Wanda yake fitowa daga can gefe.
Abunda yasa ta juyawa amatuk'ar razane ta maida kallonta ga, inda tajiyo sautin dake tashi like knocking door.

K'ofar falon ta zubawa ido, cike da tsoro saboda yanda kirjinta keta fat fat.
Kasancewar batasan wayake knocking d'in ba.
Duk da cewar d'an abu me kaman na'ura ake dannawa, bawai dukan k'ofar akeyi ba amma ta tsorata sosai.

Wannan dalilin yasa cikin sand'a da tsoro ta nufi k'ofar, da k'afafunta wanda suke ta rawar tsoro.
Duk da azahirance so take ta tambayi ko waye amma ta kasa, saboda wani nauyi na musamman da taji bakinta yayi.
Hakan yasa ad'ad'are takai hannu ta murza handle d'in k'ofar.
Wanda atake ta bud'e, saidai tun kafun k'ofar ta kai ga k'arasa bud'ewa ta rumtse Idanunta k'am, saboda tsoro da kuma kokonton abunda zata gani.

"Good morning Maa."

Matashin saurayin dake tsaye abakin k'ofar ya fad'a, Wanda jikinsa ke sanye da white uniform.
Yayinda hannayensa kuwa ke d'auke da wani babban tray, da cikinsa ke d'auke da plates and food flask na abinci kala kala.

"Good morning maa!"
Ta maimaita kalmar akan bakinta, cike da d'an yanayin mamaki,  tare da Ware Idanun nata ta sauk'esu akan saurayin wanda ya zuba mata ido.

Ita d'inma  idanu ta zuba masa tamkar wanda taga statue, haka take kallonsa.
Wanda haka yasa saurayin ganin irin kallon da takeyi masa, yasa shi d'an rusunar dakai duk da yasan ya girmewa shekarunta sosai, amma tsarin aikinsa ne martaba duk wanda ya gani acikin gidan.

"I'm sorry Maa abincin ki dana MR. M.J na kawo."

Ya fad'a yana me mik'a mata tray d'in, tare da d'anyin k'asa da kansa.

Itakam Soumaya mamaki ne ya kasheta.
"Maa, Mr.M.J."
shine abunda ta maimaita akan harshenta, batare kuma da ta karb'i tray din ba.
Ganin hakan yasa shi sake mik'o mata tray d'in.
kallonsa ta kuma yi, kamar bazata karb'a ba kuma saita sanya hannayenta duka biyu asanyaye, fuskarta d'auke da d'an yanayi na rashin gamsuwa, ta k'arb'i tray din tare da juyawa ad'ad'are ta koma cikin falon.

Wanda hakan yasa shima saurayin juyawa ya sauk'a k'asa.
Ita kuwa tray d'in ta zubawa ido, dake d'auke da nau'o'in plates d'in abinci almost 6 colors, kowanne kuma da kalan abunda ke cikin sa.

"MR. M.J. Waye shi?" Ta fad'a tana sake kallon tray d'in, tare da d'an rumtse Idanunta.
Wanda hakan yasa atake Brain d'inta ta bata wanda ake nufi.

Wani irin raasss taji k'irjinta yayi.
Atake ta d'an zazzaro idanunta alokacin da take kallon, duhun library'n wanda ta fita tabarsa aciki daren jia.

"Abincinsa? wai kuma ni ce zan bashi na shiga uku na!"
Ta fad'a da muryarta wacce ke rawan tsoron da ita kanta batasan na meye ba.

Ahankali kuma ta sake maida idanunta ga library'n, da duhunsa kad'ai ke k'ara sanya mata jin fargaba.
Wannan dalilin asa araunace ta sake kallon tray d'in, Wanda zuciyarta ke raya mata cewar ta ajiye ta gudu.

Saidai batasan me zai biyo bayan ajiyewar nata ba, domin idan har MAJNOON ne shi to abune mai wahala yazo ya d'auki abincin.
Hakan yasa a hankali ta lumshe Idanunta  wanda lokaci d'aya taji ruwan hawaye ya taru acikinsu.

Jarumta take k'ok'arin arawa kanta, hakan yasa cikin danne fargaba da tsoron dake zuciyarta.
Ta nufi libraryn hannunta rik'e da tray din, duk da yanda takejin, zuciyarta na bugawa akowanne taku d'aya da zatayi.

Kwarai tana matuk'ar jin tsoro, musamman ayanzu da ta shigo cikin library'n, da babu ko d'igon haske acikinsa.
taku kad'an tayi tasoma tsayawa, saboda tunanin da zuciarta ta fara yi,
"Ko dai bayanan ne."
Tayi maganan ad'ad'are, tare daci gaba da takawa ahankali, tar d'an kasa kunne ko zata jiyo sautin numfashinsa.
Amma saidai akasin hakan k'aran sautin bugun zuciyarta ne ya hanata jin komai.

Almost 5mn tana tsaye, kamar me nazartar wani abu, jin tsoro na k'ara mamayeta ne kuma yasa ta juyawa da sauri da niyar barin wajen.

Aikuwa tana juyawa taji tayi karo da wani abu, Wanda duhu yasa ta kasa tantance ko menene shi, wani gigitaccen k'ara ta sake tare da sakin tray din dake hannun nata ak'asa  komai ya tarwatse.

*9:39 pm*

*(Wattpadians bandamu da kuyi comment ba vote kawai nakeso, iya adadin vote din da nake samu, iya abunda zan baku, wannan littafin ba Free bane but ina daura muku shi anan,  mutum 2k zasuyi read amma ace vote bai wuce 500 haba😡)*


You are reading the story above: TeenFic.Net