Chapter Eleven

Background color
Font
Font size
Line height

                   *MAJNOON!!*
             *(The Innocentmad)*

"Writing by*
fatymasardauna
     *Wattpad*
@fatymasardauna

*(This book is mainly for those that pay, if you know you didn't pay please don't read it. Here is the Account Number for people that are willing to pay- 0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz Bank. AMOUNT 300, WhatsApp number 07069917168}*

             *CHAPTER 11*

Idanunta da sukayi nauyi, kana kuma suka b'ata tsawon awanni alumshe, ta soma bud'ewa ahanakli.

Saidai kamar yanda takejin tunani da hankalinta na juyawa, haka ma d'akin ke juya mata.
Inda ahankali ta sauk'e idanunta akan silin din dake mamaye saman d'akin.

Wanda hakan yasa ta
sauk'e wani irin ajiyar zuciya me k'arfi.

Tare dasa bayan hannunta, agefen fuskarta ahankali ta share hawayen dake d'igowa ta gefen fuskar nata.

Tabbas tasan cewa a irin rana ta yau, akowanne gida, haka kuma kowanne Aure, mutanen gidan na tashi ne da farinciki, yayinda amadadin shiru kuwa, sautin hayaniyan mutane y'an taya murna ne, ke amsa amo tako ta Ina.
Kamar kuma yanda aka sani a irin yau, ga duk wacce take shirin fuskantar Ranar d'aurin aurenta, To farinciki ne ke  cika zuciyarta, yayinda take fata da d'okin zuwa ga masoyinta, Wanda ta zab'a amatsayin abokin rayuwa, Masoyin da zai b'ata farinciki.

Irin farincikin da ita tasan cewar yayiwa rayuwarta k'aura, kamar yanda ranar ta zame mata Ranar kuka, had'i da tsananin fargaba, Ranar da takejin kamar ba gaske ba, ranar da bazata ki ace ya zamto mafarki agareta ba, Wanda zuciyarta ke fatan inama da hakan zai kasance, inama da wani zaizo ya tasheta daga kwancen ya sanar mata cewar mafarki takeyi.

Inama da ace wani zai iya kawo kansa kirjinta, yaji salon sautin bugun zuciyarta.
Sautin da amon bugunsa ke amsawa acikin kunnuwanta.
Sautin dake k'ara haddasa mata tsoro had'i da tarin fargaba.

Tabbas ayau ta sake sanin ciwo irin na rashin mahaifiya.
Duk da cewar batasan dad'in mahaifiyar ba, amma tayi imani cewa da ace tana da Uwa mahaifiya, to da ta sanar da ita, rad'ad'i da kuma zafin da takeji acikin ranta.

Ranar da ya kamata ta zamo na farinciki arayuwarta ya zame mata ranar tsoro, tsoron fuskantar MAJNOON wanda  k'addara ta zab'a mata.

"Yah Allah Wannan wacce irin k'addarace, da take neman tsaida bugun zuciya, da numfashina? Wacce irin k'addarace da take neman, zautar da tunani na.... yah Allah ka taimakeni...."

Maganan da zuciyarta keyi kenan, Wanda hakan yasa hawaye gangarowa daga cikin idanunta.
Tare da fesar da numfashi na zazzafan zazzab'in daya riga yaci k'arfinta.

Daidai lokacin aka bankad'o k'ofar d'akin nata wanda hakan yasa, asanyaye ta juyar da idanunta zuwa bakin k'ofar dan ganin wanda ya shigo.

Moudou wacce itace ta turo k'ofar d'akin ne ta shigo, tare da sanya hannayenta duka biyu a k'ugunta tana kallon Soumaya'n.

Ganin yanda take numfarfashi ne kuma, yasa ta tab'e fuska,  cikin kuma halin ko'in kula tace.
"Ke kuma kwanciyar me kikeyi tun safe sai kace wani ruwa? Ko dai kin manta da cewar yau za'a d'aura miki aure da mahaukacin mijin naki ne?, ni gara ma kiyi ki tafi, saboda Ina da buk'atar d'akin."

Moud'oun ta k'are maganan tana me k'arasawa wajen d'an drawer'n Soumayan, tare da soma duddubawa, kasancewar har ta riga da tayi cinikinsa zata sayar.
Acewarta ayanzu har gidanma idan taga dama saita sayar.

Still Batare kuma da ta damu da yanayin da Soumaya'n ke ciki ba tace.

"Nidai ban tab'a ganin wulak'antaccen Aure irin wannan ba, ace babu dangin uwa babu na Uba, ba kuma kayan Aure balle goro da cingam, ni wannan wani irin tsinannen Aure ne, koda yake MAHAUKACI ai duk baisan Wannan ba."

Tayi maganan tana me soma k'arewa d'akin kallo.

Soumaya kuwa Akaron farko da taji wani irin abu ya soki k'irjinta, Wanda har saida hakan ya tilasta mata rumtse Idanunta.
Wanda suke zubar da tsinkakkun ruwan hawaye.

Kalmar MAJNOON itace kalma d'aya tak, da jinta ke sanya mata bugawar zuciya, haka kuma itace kalma d'aya tak dake yawo acikin k'wak'walwarta.
Kalmar dake fatali da duk wani nutsuwarta.

Ganin hawaye a idanunta ne kuma, yasa Moud'oun watsa mata harara, cikin kuma halin ko in kula tace.

"Ba kuka ba kiyi uban kuka, yau dai zaki tafi ki bawa mutane waje."

Ta k'are maganan tana me nufan hanyar fita daga cikin d'akin, saboda sallaman da takejin yana tashi atsakar gidan nasu.

Koda ta fito kuwa ganin wacce take sallama'n ne, yasa ta had'e fuskarta, tare dayin kicin kicin da fuska.

Inna Hauwa kuwa wacce itace ta shigo cikin gidan, murmushi tayi tare da  d'agawa Moudou'n gaisuwa.

Wacce ta amsa mata ad'add'age fuska babu yabo ba fallasa.

Saidai ita Sam bata damu da hakan ba, dan dan da sabo tariga da ta saba da halin Moud'oun, wannan dalilin yasa batare da ta damu da kalar amsa gaisuwar nata ba, kaitsaye ta nufi hanyar d'akin Soumaya'n, kasancewar dama ita badan Moud'oun tazo ba.
Malam Musbahu ne ya turo ta, akan tazo ta kula da Soumayan tamkar yanda ake kulawa da kowacce amarya aranar aurenta.

aikuwa ganin tayi hanyar d'akin Soumayan ne, yasa Moudou ta bita da harara, musamman ledar da tagani rik'e ahannun Inna Hauwan.

Inna Hauwa kuwa da sallama d'auke abakinta, ta kutsa kanta cikin d'akin Soumaya'n.

Wanda shigowar Inna Hauwan ya sata bud'e idanunta da suke d'igar da hawaye ahankali.

"Subahanallahi Soumaya kukan me kikeyi haka?."

Inna Hauwan ta fad'a tana me ajiye ledan dake hannunta, tare da d'an sunkuyowa, ta dafa kan Soumaya'n, kasancewar tana shigowa taji sautin numfarfashin da take fitarwa, irin na way'anda suke d'auke da zazzab'i.

"Tashi ki zauna ki fad'amin meke damunki."
Inna Hauwan ta fad'a tana me k'ok'arin tada ita zaune.

Saidai kuma rashin k'arfin jikin da bata dashi sosai yasa ta kasa tashi.

Hakanne kuma yasa Inna Hauwa fuska d'auke da d'an yanayin damuwa tace.

"Soumaya dama baki da lafiya ne? Ina fatan dai kinsha magani ba kwanciya haka kawai kikayi ba."

Kanta ta d'an girgiza tare dayin raurau da idanu alaman "A'a."

Numfashi Inna Hauwan ta d'an fesar, cike kuma da tausayin yarinyar ta zauna agefenta, bayan ta jawo k'atuwar ledan da ta shigo dashi.
Kulan dake cikin ledan ta ciro tare da bud'ewa, ta ajiye agaban Soumaya'n, saboda sanin da tayi cewar lallai akwai yunwa acikin Soumaya'nne kuma yasa, ahankali cikin tausasa Murya tace.

"Nasan cewa bakya cikin farinciki Soumaya, haka kuma kinajin ranar yau d'in daban dana kullum, Hak'ik'a dole damuwa zatayi tasiri acikin rayuwarki nasani, saidai idan kika daure Soumaya komai mai wucewa ne, karb'an Auren nan da kikayi K'addarar kice, kuma Insha Allah, Allah bazai barki haka ba, zai kawo miki d'oki aduk inda kike, nasani akwai ciwo matuk'a had'a mai hankali da marar shi, saidai kuma abunda K'ADDARA tazo dashi, babu wanda ya isa guje masa, kada kiyi bak'in ciki Soumaya, domin ba kece kikayiwa kanki zab'i ba, Allah ne ya zab'a miki MAJNOON!, kuma yasan abunda hakan zai haifar agaba, alkhairi ko akasinsa duk daga mai sama ne, saboda haka yanzu kici abincinnan sai kiyi wanka, na taho miki da kayan da zaki sa, ki daina kuka kinji, yau ba ranar kuka bace, ko kin manta da cewar mahaifinki yana gab da samun lafiya ne, kiyi shiru kinji.

Inna Hauwa ta k'are maganan cikin lallashi.

Wanda hakan yasa akaron farko kenan da, Soumayan ta sauk'e wani irin nannauyan ajiyar zuciya.
Badan kuma wai taji sanyin kalaman Inna Hauwa'n da tayi mata ba.
domin ita zuciyarta Mai RAUNI da DAMUWA ce ako da yaushe.
Kamar yanda
Hawaye da bugun zuciyarta batasan yaushe ne zasu dawo daidai ba.
Komai na rayuwarta ganinsa takeyi abaibai.
Yayinda k'addarar
Auren MAJNOON ke k'ok'arin farrak'a tunaninta, da kuma d'an guntun fatan dake rayuwa acikin zuciyarta.

Saidai kaman yanda ake fad'a, ta sani bakin alqalami ya riga ya bushe.
Kaman yanda labb'anta suka kasa motsa kansu ayanzu.

"Share hawayen nan naki, bari naje na sayo miki magani."

Inna Hauwa ta fad'a tana me mik'ewa tsaye, tare da d'aukar y'ar k'aramar jakanta ta fita zuwa sayo maganin.

Soumaya kuwa ganin fitan Inna Hauwa'nne, yasa ta maida jikinta ta jingina da jikin bango, tare da lumshe idanunta.
Inda sam batajin zata iya saka wani abu me sunan abinci acikin cikinta.

"MAJNOON!!"
Kalmar tayiwa k'wak'walwarta dirar mikiya, Wanda hakan ya sata jin fad'uwar gaba.
Bata san meyasa ba kalmar ke yawan dawo wa cikin tunaninta, kalmar da ta hana k'wak'walwarta sakat.

Idanunta ta kuma lumshewa, tare da duk'unk'une jikinta waje d'aya.

Kwarai tsananin duhun da take gani acikin idanunta, zata iya yin imani cewa ayau cikin zuciyarta yafi haka duhu.  
Numfashi ta d'an ja, tare dasa Hannayenta ta d'an rufe kunnuwanta.
Saboda wani irin sauti takeji acikinsu, sautin numfashin dake fusga tamkar zai bar gangar jikin meshi.
Sannu ahankali kuma duhun dake yawo acikin idanun nata, ya soma rikid'ewa izuwa haske.
Acikin tsananin hasken ne kuma
take hango, fararen hannayen da jikinsu ke d'igar da jini.

Idanunta ta kuma rumtsewa, alokacin da jikinta ya soma tsuma, saboda yanda idanun nata ke gane mata, jinin dake kwarara, ahannun mutumin da yawan gashi ya rufe  fuskarsa.
Yayinda sautin gurnanin numfashin da yake, ke neman fasa dodon kunnuwanta.

Tabbas tasan cewar ba mafarki take ba, amma kuma ta kasa bud'e idanuwanta, duk da yanda takejin kanta na sarawa.

"Soumaya lafiya k'alau kike kuwa, meyasa bakici abincin ba?."

Muryar Inna Hauwa kenan da yayi sanadiyar dawo da ita hayyacinta, da sauri kuma cikin d'an zabura, ta Ware idanun nata, Wanda suka bayyana alaman tsoro k'arara atattare da ita.

Ganin hakan ne kuma yasa Inna Hauwa'n zuba mata ido.
Inda cikin mintuna kad'an kuwa ta fahimci yanayin Soumayan.

Wanda kuma dama tasan dole za'a samu hakan.
Wannan dalilin yasa ta zauna tare dasa hannun ta dafa kafad'an Soumaya'n, cikin kulawa tace.

"Ki d'anci abincin ko kad'anne kinji Soumaya, ga magani nan na sayo miki, kuma kinsan dole sai kinci abinci kafun kisha, maza ki ci ko babu yawa."

Ta k'are maganan tana me sake tura mata abincin gabanta.

Gudun kada Inna Hauwa'n taga kamar tayi mata taurin kaine kuma, yasa ahankali ta d'ibi abincin takai bakinta.
Wanda ta ji d'and'anonsa akan harshenta tamkar magani.

Haka dai ta d'anci kad'an, jin aman dake taso mata ne kuma yasa ta, ture abincin gefe, tare da langwab'ar da kanta.
"Nak'oshi."
ta fad'a cikin sanyi, had'i da rawar da voice dinta keyi.

"Yauwa ko kefa duk dama bakici da yawa ba, karb'i magananin kisha."

Inna Hauwa ta fad'a tana me mik'o mata, k'wayoyin magungunan da ta b'are, had'i da ledan ruwan pure watern.
saidai kuma kasancewar dama tun asali ita bamai son magani bane,  yasa ta d'an shagwab'e fuska.

Ad'ad'are kuma ta karb'i maganin Tasha, tare da komawa ta kwanta.

Inna Hauwa kuwa mik'ewa tayi ta fice daga d'akin, kaitsaye kitchine dinsu ta nufa, inda ta d'aurawa Soumayan ruwan wanka, akan d'an ragowar gas d'insu da yayi saura.

Ruwan na zafi ta juye acikin bokiti, tare da surkawa ta kai mata shi, cikin d'an madaidaicin public toilet d'in dake tsakar gidan.

Bayan takai ruwan toilet ne Kuma, ta koma d'akin Soumayan.
Dan ta sota tayi  wanka

Koda ta shiga akwance ta sameta tayi irin kwanciyar nan na rub da ciki.

"Soumaya je kiyi wanka kizo sai ki ci gaba da kwanciyan."

Inna Hauwan ta fad'a tana me kokarin soma kimtsa d'akin Soumayan.

Soumaya kuwa dake kwance, wanda zazzab'in ya d'an soma sauk'ar mata saboda maganin da tasha.
Ahankali ta tashi tsaye, tare da rage kayan dake jikinta, kaitsaye ta wuce zuwa ban d'akin.

Wanka tayi Kamar yanda Inna Hauwan ta buk'ata, wanda kuma babu laifi yin hakan yasa ta d'anji k'arfin jikinta.

Saidai wani abu dake neman sake hautsuna tunaninta shine, sabon fad'uwar gaban da ta fara ji, daya sanya zuciyarta tsananta bugawa.

Hakan  yasa cikin rashin k'arfin jiki, ta dawo d'akin.
Tare da neman waje ta zauna.
Ganin shigowar nata ne kuma yasa Inna Hauwa, bud'e ledan da ta shigo dashi, wani farar doguwar riga mai adon golding da mayafinsa ta ciro.
"Gashi amsa kisa."
ta fad'a tana me mik'awa Soumaya'n.
Wacce ta amsa jiki asanyaye, hade da kurawa kayan idanu, kamar me nazartan wani abu. 

"Kisa mana, babu lokaci fa."

Maganar Inna Hauwa kenan da yasa ta d'auke idanunta akan kayan.
Tare da tashi tsaye ta warware rigan.
Kasancewar rigar Irin dogin nanne masu kama da abaya sabuwa k'al.

Asanyaye ta zura rigar ajikinta, wacce tayi matukar yi mata kyau, musamman yanda fuskarta tayi fa yau, duk da cewar kyawawan idanunta sun kumbura amma hakan bai Hana sirrin kyaunta bayyana ba.

"Masha Allah gashi kuwa duk da babu kwalliya kinyi kyau."

Inna Hauwa ta fad'a tana me k'arewa Soumaya'n kallo, wacce ta sake dogon gashinta, da ya sauk'o har gadon bayanta.

Batare da ta yafa mayafin kayan ba Kuma ta sake komawa ta kwanta.
Saboda yanda takejin k'afafunta na rawa, asanadin dawowan da zazzab'in yayi mata.

Idanunta ta lumshe ahankali, tare da fesar da sassanyan numfashi.
Saboda wani irin sabon bak'on yanayi da takejin kanta aciki.

10:00 pm.

Ak'alla su 7 ne ke zaune akan tabarman.
Yayinda Malam Rabiu dake akusa dashi ya d'ago ya zuba masa idanu.
Ganin yanda yayi tagumi ne kuma yasa shi, d'an gyara zamansa tare da kallon Baffa'n, cikin son sanin abunda ke faruwa yace.
"Malam Musbahu lafiya kuwa, naga tun d'azu kayi shiru kayi tagumi."

Nannauyan ajiyar zuciya Baffan ya sauke, tare kuma da zare hannun daya yi tagumin dashi.
Hakika damuwa ne fal acikin zuciyarsa.
Domin yasan cewar ayanzu Soumayan nauyi ce akansa, nauyin da yake shirin mik'ata ga MAJNOON.
Tausayi da fargaban halin da Soumayan zata fuskanta ayanzu yake, Wanda kuma hakan shi ya sashi zuba ta gumi.

D'ago kansa da yayi ahankali da niyar yiwa Malam Rabi'u magana ne kuma, idanunsa suka sauk'a akan wasu tsala tsalan motoci guda 5 da suka shigo cikin layin tare da tunkarosu kaitsaye.
Idanunsa ya zubawa motocin, da suka dumfarosu.

Yayinda Biyu agaba d'aya a tsakiya, sai kuma wasu biyun kiran Mercedes dake bin bayan babban Jeep din dake tsakiyan.
Motoci ne irin na alfarma, motocin dake nuna matsayi da kuma ajin, mutanen dake cikinsu.

Daidai sun kawo k'ofar gidan su Soumayan ne kuma, motocin suka tsaya.

Da sauri mutanen dake cikin motocin dake gaba da bayan suka fiffito, Wanda suke sanye da bak'ak'en kaya, dake nuna matsayinsu na escort.
Inda Cikin hanzari suka k'arasa tare da bud'e murfin had'add'Iyar Jeep din nan dake tsakiyan motocin.

Dr. Mouhammad wanda ke zaune agaban motar ne ya fara fitowa.

Sai kuma Alhaji Haris.
Kafun Billionaire Dawoud Saraki wanda yake zaune a gidan baya daya fito.
Kyakkyawan farin dattijo ne Wanda yake asalin balaraben k'asar YEMEN🇾🇪.
Kasancewarsa babban mutum mai haiba da kuma tarin dukiya, wannan yasa fuskarsa ke cike da kwarjini.

Duk da cewar ashekare bazai d'arawa, shekaru 55 ba, amma yanayin hutu da kuma kud'in da suka samu mazauni agaresa, yasa sam tsufa bai bayyana sosai atattare dashi ba, saidai d'an farin gemun dake wadace akan fuskarsa.

Zuciyar Malam Musbahu ne ya buga, atake kuma cikin sauri ya mik'e tsaye, yana me kallon, mutumin da sai a gidan tv da jarida kawai yake iya ganinsa.

Hakan yasa da sauri ya k'arasa dan tarosu, kasancewar ganinsu da Dr. Mouhammad ya sanya shi fahimtar ko sud'in suwaye.

Koda ya k'arasa kuwa cikin sakin fuska, Billionaire Dawoud Saraki ya mik'a masa hannu suka gaisa.
Yayinda Malam Musbahu'n kuwa duk ya rud'e saboda bai tab'a kasancewa kusa da Kusa da manyan mutane irin haka ba.

Wannan yasa cikin girmamawa yayi musu iso zuwa, kan tabarman da suka shumfud'a ak'asan  wata y'ar rumfa dake gefen gidan.
Ga mamakinsa kuwa, sai ganin Billionaire Dawoud Saraki'n yayi ya zauna akan tabarma, batare da ky'ank'yami ko kuma k'yama ba.

Haka ma Dr. Mouhammad da Alhaji Haris wanda suka zo atare da Billionaire Dawoud sarakin.
Duk zama sukayi, yayinda escort din nasu kuwa, suka je gefe suka tsastsaya, hannayensu rik'e da bindigu bayan sun ajiye kayan goro dasu sweet din da suka zo dashi dan d'aurin auren.

Sabuwar gaisuwa suka sakeyi, cike da mutumta juna, duk da cewar abokanan Malam Musbah'un daya gayyato, sun kasa sakewa saboda ganin Billionaire Dawoud Saraki, mutumin da ko amafarki basu tab'a tunanin zasu gansa ido da ido ba, haka kuma mutumin da sunansa ke yawo acikin mujallan Nigeria, dama wasu k'asashe daban, balaraben da yazo ya kafa tushen arzikinsa a Nigeria, Wanda kuma ya kawowa Nigeria sauye sauye daban daban.

Da yawansu mamaki suke, had'e da al'ajabin jin cewar wai  shi da kansa ya zo neman Auren Soumaya y'ar gidan MALAM SA'OUD.mutum mai matsakaicin k'arfi, Wanda saiya fita ya nemo kafun ya kawo gidansa aci.
Lallai Allah babu yanda baya abunsa.

Saidai kuma duk zuciyoyinsu sun zak'u dason sanin waye ne Wanda zai auri Soumayan.
Saboda sun san d'a d'aya tilo kawai yake dashi.
Wanda kuma shine MAJEED shugaban kamfanonin *S* sannan kuma mamallakin companyn *M&J*  matashin saurayin da babu Wanda baisan sunansa ba, saboda tashen kud'in da yakeyi, da kuma yanda shima hotunansa ke yawo ajaridun wasu k'asashe, musamman k'asar ITALY da acanne tushen kamfanin nasa yake.
Richestman ne k'warai
Wanda ayanzu duniya ke rad'e rad'in haukacewarsa.

Wannan dalilin yasa dukansu suka k'osa dason a d'aura Auren, dan suji waye angon, dan sunsan koda Haukan, abune mai wahala Hamshak'ai irinsu suso y'ar talaka, saidai in kuma da wata b'oyayyar manufa.

Dr. Mouhammad ne ya katse hanzarin tunanin nasu ta hanyar, mik'awa Malam Musbahu kud'i Naira dubu 60 da yayi, amatsayin sadakin Auren.

Kamar kuma yanda al'ada ta shar'anta, Baffa shi ne ya zama wakilin Soumaya, inda Alhaji Haris kuwa kasan cewar sa aminin Billionaire Dawoud Saraki shiya zama waliyin ango.

Limamin masallacin unguwar tasu da Baffa ya gayyato kuwa, shine ya gyara zaman sa, domin Ganin lokaci na tafiya, wannan dalilin yasa cikin tausasa murya yace.
"Inaga ya kamata mu d'aura Auren ko."

Kai duk suka jinjina
Inda Alhaji Haris ya kalli Malam Musbahu murya anutse yace.

"Ni Alhaji Haris waliyin Ango ina nemawa d'an aminina Alhaji Dawoud Saraki, wato "ABDULMAJEED DAWOUD SARAKI neman auren SOUMAYA SA'OUD! akan sadaki naira dubu 60."

ajiyar zuciya Baffa wanda jikinsa ke rawa ya sauk'e, tare da shanye bugawar da zuciyarsa keyi.
Duk kuwa da yanda kirjinsa yakai ga bugu fat fat haka ya daure.
Cikin sanyi kana da muryarsa wacce ke rawa yace.

"Ni Malam Musbahu wakilin amarya, kuma amini ga mahaifin Soumaya Malam Sa'oud, na bawa ABDULMAJEED DAWOUD SARAKI auren SOUMAYA SA'OUD akan sadaki naira dubu 60. Jama'a ku shaida."

Ya k'are maganan yana mejin hawaye na cika idanunsa, saboda tausayin yarinyar dako gama sanin kanta bata yiba, yarinyar da ayanzu kuruciyarta ke fuskantar barazana.

"Alhamdulillahi Aure ya d'auru, sai muyi salati goma ga Annabi."

Malam Usman wato liman din da Baffa ya gayyato ya fad'a, cikin d'an d'aga murya saboda kowa ya shaida.

"MUNSHAIDA!!"

Muryoyin abokan malam Musbahu suka amsa wajen.
Yayinda zuciyoyinsu ke cike da aljabi.

Adaidai lokacinne kuma.

Zuciyoyin dake awaje maban banta suka soma amsa amon bugawarsu dake tafiya atare.
Inda duk wani abu dake cikinsu ke  motsawa.

Kowanne bugawa yake saboda damuwar d'an uwansa.
Yayinda Raunin dake cikin d'aya zuciyar take tafiya da wanda cikinta ke cike da kewa.
Bugawa suke irin bugun daya zarce tunani da hankalin junansu, bugawar kuma

You are reading the story above: TeenFic.Net